*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty**SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT
SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDAHAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU
INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM.
INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI
INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL
INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z
*Page 7*
Kofar ya ƙurama ido wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka wuce a baya suna gilma masa, in hasashen sa ya zama gaskiya Mansoor bai manta da Mimi ba har kwanan gobe tana cikin ransa kuma saboda ita ne har gobe ya kasa iya kula kowacce ƴa mace.
Shi da kuma ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba, ba zai taɓa auranta ba kuma ga shi har gobe yana sonta shi kam ya rasa ta in da zai saka tunanin wannan al'amarin.Komawa ya yi ya kwanta yana wasu tunane tunane, shima tun bayan abin da ya faru ba su kara haɗuwa ba shi daman ya bar Gombe ya koma Kano. Nasir dai kwanaki can da jimawa ya ce sun taɓa haɗuwa har ta karɓi lambarsa to ba ta taɓa kiransa ba shima kuma daman itace ta karɓi Layin nashi shi bai karɓi nata ba sai dai suna ganinta a akwatin talabijin ɗin, tunda tana aiki a sananniyar gidan talabijin sannan ta yi suna kowa ya santa. Shima dai yana ganinta lokaci bayan Lokaci in yazo garin a tibin Inna in Walida ta kunna, Mansoor ne ba shi da wani masaniya a kanshi sanin shi fa ba ka gane gabansa ballantana bayansa to kila har gwara shi ya kan tsaya su yi magana mai tsawo, wasu tuni ya yanke wannan alaqar a tsakanin su.
Bai taɓa tunanin haka soyayya ke da zafi ba sai akan Mansoor a lokacin ma daga shi har Mimi suna da karancin shekaru shi ya ɗauka a shekarun da suka ɗauka ba sa tare soyayyarsu za ta disashe ashe ba haka ba ne, tana nan ta kara girma ne acikin zukatan su.
Ba zai taɓa man tawa da ciwon da Mansoor ya kwanta a lokacin ba, da kukan da ya riƙe ƙirjinsa yana yi ba, bqasonta yake yi ba kaunarta yake yi sannan sun shaku sosai soyayya ta rufe musu idon da suka kasa gane bambamcin dake tsakaninsu har sai da komai ya kwaɓe sannan Mansoor ya fahimci abin da aka jima ana nuna masa. Tun Mu'azzam na zaman jiransa har barci ya ɗaukesa Mansoor bai fito daga tiolet ba. Sama da awa ɗaya sannan ya fito daga cikin tiolet ɗin jikinsa na faman ɗigan da ruwa. Tsaye kawai ya yi a tsakiyar falon ookaci ɗaya yana mai harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa. Mu'azzam yake kallo yana barcin sa cikin salama da kwanciyar hankali ba shi da damuwan komai a cikin zuciyarsa.
Yana jin dama shima haka yake ba shi da wata damuwa. Dama shima zuciyarsa ta sauke wannan nauyin abin da ya tokareta shekaru goma ya yi rayuwarsa cikin salama ba tare da damuwa da tunani ba.Duk lokacin da ya tuna abun sai ciwon da ke kirjinsa ya dawo sabo, saboda ita ne har gobe ya kasa kallon wata ƴa mace da sunan kallon soyayya. Saboda ita ce ya ji aure ya fita kansa kwata kwata ya ji a duniyan nan ba zai iya zaman aure da wata mace ba.
Saboda ita ne ya sauya rayuwarsa da ga mai yawan hira da son mutane zuwa wani mutum mai son kaɗaici da son zama shuru, Saboda ita ne ya ji ya tsani masu kaki gani ya ke yi dukkansu haka suke marasa adalci da sanin ɗarajan ɗan Adam.
A lokacin baya da ita ya yi mafarkin kasancewa har karshen rayuwarsa.
Shi fa mafarkansa gabaɗaya ko ɗaya bai cika ba, duka ya rasa su sai wasu ya gina sabbi acikin duniyarsa.
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI