Page 14.

143 8 1
                                    

*IDAN AN CIZA..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*

*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*

Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.

*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*

Zaku sameta  a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0

*Page 14*

Mommy na zaune a gefen gadota tana sharan hawaye daman abin da take gudu kenan, da gudu Khadija ta faɗo ɗakin tana faɗin "Mommy mun shiga uku bindiga ina ga Abi zai ɗauko." Ta faɗa lokaci ɗaya  tana hawa saman gadon ta lafe a bayan Mommy, tana ta haki tare  da sauke numfashi.
Mommy ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce"Allah ya duba mu, yau sai abin da Allah ya yi."
Khadija ta ce"Mommy me ya faru ne? me Mimi ta yi ne?

  Nan Mommy ta karanta mata abunda ta sani sai Khadija ta zaro ido kafin ta ce"Mommy ke ma me ya sa ba ki hana ba? Mimi tana hauka ne? Wani yaro ƙarami da bai wuce a wanke masa kashi ba ne za ta jawo ma na bala'i muna zaman zaman mu?
Mommy ta karɓe da faɗin "Hajiya ce ta mara mata baya, me zan ce Khadi?
Khadija ta ce" Mommy ke ma me ya sa kika yi shuru? Kin san fa halin Abi wlh ba Mimi kaɗai ta shiga uku ba har dake har damu gabaɗaya." Mommy ta yi tagumi kafin ta ce"Khadi addu'a za mu yi Allah ya sausauta zuciyar Habibi."

Khadija sai ta kasa mgana wayar Mommy dake kan gado ta ɗauka ta kira lambar Madiha tana ɗauka cikin ruɗewa ta fara gayamata abunda ke faruwa. Daga can bangaren Madiha ta ce"Subhanallah Ita Mimin ce ta ce aure take so?
Khadija ta ce"Mommy ma ta ce ta sani tun zuwanta Gombe take tare da yaron, wai kiji ma yaro ƙarami kila ma sa'an Mimin ne."
Madiha ta ce" Ba su da hankali ne, ita kuma Hajiya ta fara tsufa me ya sa mommy ba ta hana ta kiran Abi ba? Mommy na gefe tana jin khadija na maida ma Madiha zencen bayan Madiha sai da ta kira Sulaiman bai ɗauka ba ta tura mata saƙo.

  Ranar a ɗaki ɗaya Khadija suka kwana da Mommy saboda tsoro Abi kuma ko runtsawa bai yi ba bindiga a gabansa yana shan alwashin harbe wannan shegen yaron.
Shi a tsarin rayuwarsa ba tsarin ya aura ma ƴarsa kowani datti, haka kurm rana tsaka wani ɗan talakawa zai zo ya lalata tarbiyan Mimi, duk laifin Hajiya ne ita ce ta matsa sai da ya bar mata Mimi shi ne daga karshe ta yi masa wannan sakayyan.
A washegarin ne kuma Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya ya sameta da maganar, Hajiya ta zauna ta yi masa bayanin komai game da Mansoor har tana gayamasa maraya ne mahaifinsa ya rasu shi ya sa Inna Meri ta yi aure a nan gidan Wanzamai, shi bai gayama Hajiya sun yi waya da Kabiru ba amman shi kanshi sai da ya nuna ma Hajiya abun bai dace ba.

  Kai tsaye ya ce"Hajiya kema me ya sa za ki bi ye ma Mimi? Har yaushe take yarinya ƙarama gaskiyan Major ne ta maida hankali a karatunta, shima yaron ya je ya yi fafutar rayuwarsa  a gaba in suna da rabon auran juna sai su yi auran lokacin sun san dai dai da rashin sa amman yanzu dai ko ni ban goyi bayan wannan shirmen ba Hajiya."
Hajiya ta fara faɗa tana faɗin" To ai ba abu mara kyau ba ne, kuma sun yi yarinta da auran ne? ni ban ga illar haka ba ni fa magana na ce ayi ko da ba yanzu za'ayi auran ba ya samu ya taimaki yaron ya cika burinsa daga baya sai ayi auran."
Alhaji Hamza yace"Hajiya to ai ke ba ki da wannan ikon, magana na wajen Major kuma kinsan yadda ya ke da burin ƴaƴansa su yi karatu." Hajiya ta fara shiga tana fita Alhaji Hamza ya ga ba za ta gane ba ya yi mata sallama ya fita kuma shima ya saka an yi masa binciken Mansoor abun ka ga ɗan siyasa mai jama'a tuni ya samu cikakken bayani akan Mansoor. Kuma nan take ya kira Major ya zayyana masa.
Amman sai da ya ce"Ka bi komai a hankali Major a lallashi Hajiya a fahimtar da ita illar haka, shi kuma yaron ba sai  an yi masa wani abu ba, bakin ka alaikum ka ɗauki ƴarka ta koma hannunka, In ma ta kama sai a sauya ita mahaifiyar yaron da wata mai aikin Hajiyan saboda a samu masalaha."
 
  Ko alama bai ɗauki wannan shawaran ba, ai sai ya nuna mana wannan yaron ya taɓo tsuliyan dodo ashe ma Agola ne mai tsaurin ido zai gane ya shigo gonar Soja, da wuri ya tashi daga Office ya na komawa gida ya shige ɗaki Mommy ba ta nan tana wajen aiki itama Khadija ce kaɗai acikin gida tun safe ta ke waya da Madiha Sulaiman ma sun yi magana ta gama fesa musu abin da ke faruwa duk da suna can amman a tsorace suke. Khadijan da ta kira Mimi tana mata faɗan abunda ta aikata da cewa"Mimi are u mad? maganar Abi zaki warware? Ko Madiha ba ki ga an mata aure ba sai ke tun baki tafasa ba zaki ƙone?
Mimi ta tura baki kamar tana ganinta kafin ta ce"Ni ai ban ce bazan yi karatu ba, amman bayan mun yi Aure da Aji sai na cigaba da makarantar ko?
Khadija ta zage ta daman ga su saƙo da sakon haihuwa kafin ta ce"Ko ba Aji ba, ai Abi zai Aje miki kanki a kasa da bindiga wawiya kawai."

IDAN AN CIZA..!Where stories live. Discover now