Page 19.

132 4 0
                                    

*IDAN AN CIZA..!*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*

*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*

*BONANZA*

Kana naka 500.
Ta fita zakka 500.
Gidanmu 300
Sadaukarwar so 200
Malika malik 200.
Zaman gidanmu 200
Ra'ayi ne ko buri? 300.
Tsaka mai wuya 500
Mr bello 200.
Sillar Hallaci 200.
Saifudden 500.
Zainazain 300.

*Bonanza za ta ƙare a gobe in sha Allahu, in ba ki karanta ba, wannan wata dama ce*

Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.

*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*

Zaku sameta  a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0

*Page 19*

*Bayan Wata Ɗaya*

Bayan wata ɗaya da ya yi dai dai da kimamin wattani biyu da kwanaki da rasuwar Abi, kuma wata ɗaya tsakani da zencen da Hajiya ta yi da Inna Meri sai dai tun bayan lokacin ba su ƙara haɗuwa ba, Inna Meri ba ta koma ba itama Hajiyan ba ta dawo ba saboda sun kara komawa Abuja da aka yi arba'in ita da Mimi suka kwana biyu suka dawo. Gidan can na Abuja ya rage daga Mommy sai Inna Ladidi ita Inna Zainaba bayan arba'in ta koma gida, sai kuma yan aikin Mommy na amana, duk da gidan ya yi rashin megidan amman Dr.  Sulaiman da Alhaji Hamza ba su bar shi ya yi kewa ba komai da ake bukata har da wanda ba'a bukata ma suna tana dar da shi. Mommy dai duk wannan bai dame ta ba, ita dai kukanta ta yi rashi rashin da har da har abada ba za ta mai da  makwafinsa ba.

  Sannan ta kuduri niyar cika wasiyyan mijinta shi ya sa zuwan da su Hajiya suka yi ta yi mata mganar Mimi da Mansoor Hajiya ta zayyane mata abunda ya gudana a tattaunawar da suka yi da Inna Meri, Mommy cikin wani yanayi ta ce" Hajiya ni zan je da kaina mu yi mgana, ba zan iya sukuni ba tare da na cika wasiyar Habibi ba, ya rasu da Mimi a bakinsa da kuma ƙudurin nemansa ya nemi gafaransa tunda shi bai samu wannan damar ba, ni ina raye Hajiya in sha Allahu da zaran na fita takaba batun zan fara tunkara in sha Allahu."
Hajiya tace"Shike nan Allah ya fitar dake lafiya." Ta amsa mata da Amin suka cigaba da tattaunawa, duk akan mganar Mimin ne wacce duk ta yi sanyi ta koma wata iri, sannan kowa ya gan ta ya san tana da damuwa ga rashin mahaifi ga ciwon da ya jima a zuciyarta. Har su Khadija sun zo addu'an arba'in su kan su, suna ta korafin ganin Mimi ta rame kuma wani abu da kowa bai sani ba tun daga ranar da Aji ya saka mata wannan rigar da ita take kwana da ita take ta shi, in ta na jin kewarsa sai ta rumgume rigar ta yi ta kuka. Ba kowa ba ne zai iya fahimtar Halin da ta ke ciki  ba sai ita kanta da ubangijin da ya halliceta.

  Kwanansu biyar suka dawo gombe lokacin tuni daman Mimi ta koma bakin aikinta ko a can ma ana ta ƙorafin ta sauya sai dai ana tausaya mata sanin ta yi rashin uba musamman ma Rukky da suke tare ta fi kowa sanin Mimi ta rage karsaahi da fara'a
ko labarai take karantawa za'a ganta irin so cool haka kamar wata mara lafiya.
Sai dai ana yi mata uziri saboda ta yi rashi kuma dole daman sai a hankali.

  Hajiya ba ta taɓa mganar da kowa ba amman Mommy ta yi mgana da Dr Sulaiman shi kuma sai yake ganin abun wani iri har yana cewa"Mommy to tunda Hajiya ta ce ta yi mgana da mahaifiyar shi ta kuma ba ta tabbacin sun yafe ai ina ga shike nan ba lalle sai kin je da kanki ba."
Mommy ta ce a lokacin"A'a ai shi yaron aka saɓamawa kuma shi Habibi ya jadadda neman gafaransa sannan kuma ya ce ya janye kalamansa kan Mimi in har tana son shi har yanzu da amincewarsa mu aura mata shi." Kai tsaye ya ce"Haba Mommy wannan fa wani abu ne da ya shuɗe shekaru sama da takwas, ki ƙyale wannan mganar."

IDAN AN CIZA..!Where stories live. Discover now