*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty**SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.
*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0
*Page 13*
*3rd June, 2011*
Suna zaune a ƙofar ɗakin Inna Meri ne gabaɗayan su. Satin da ya wuce a ka yi bikin Yaya Amina tare da Yaya Halima to labarin bikin su Bintu ke ta yi Inna Meri na biye musu. Mansoor da Mu'azzam daga baya su ka shigo gidan tare da Baba Ɗanjuma, sai suka barshi a bangaran Magajiya da tunda aka yi sha'anin nan take ta bala'i da ya da habaici.
A tunaninta Baba Ɗanjuma ya ƙarar da duka abin da ya mallaka a auran Amina da Halima ko a wajen taron bikin sai da suka yi hatsaniya da yayar Mahaifiyarsu Aminan Madina sai da Inna Meri ta shiga tsakani ta ce duk kowa ya yi banza da ita daman abokin yi take nema, kuma daman ita Magajiya burinta shi ne ta watse taron kar a gama lafiya tunda tana da ciwon hassada a cikin ranta ga duk abin da ya shafi rayuwar Inna Meri da ƴaƴanta.
Idanuwanta ya rufe a tunaninta duk kayan da aka yi ma Amina da Halima da abubuwan da akayi na hidimar biki daga aljihun Baba Ɗanjuma ne, abin da ba ta sani ba hatta da abincin da a ka ci a wajen bikin Inna Meri ta yi tanadin shi tuni, sannan game da kayan ɗaki da sauran
hidima dangin mahaifiyarsu sun yi matukar namijin koƙari sannan ita kanta Inna Meri bangaran su tukunya kayan aiki na mata duk ita ta yi su aikin da take fita kullum ba ta bar shi a banza ba duka tattalinta na wajen yara nan mata manya musamman Amina da Halima. Shi Baba Ɗanjuman ma lokacin da maneman auran Aminan suka zo cewa ya yi ba shi da abun aurar da Amina Inna Meri ce ta ce a saka shekara zuwa a ga abunda ubangiji zai yi. To an fa saka na Amina ko wata uku ba'a yi ba Halima ta samu Inna Meri ta ce a haɗa waje ɗaya tunda dangin Habiba sun ce su za su yi komai da yardan Allah.To da Jajircewanta tare da tsayuwar yan'uwan mahaifiyar su Amina aka samu aka yi auran nan cikin rufin asirin Ubangiji a ka kai kowacce gidanta dake cikin gari, to tun bayan bikin Magajiya ba ta bar su sun zauna lafiya ba sai Allah ya isa take yi in an ci amanarta, ita masifarta ai zuwaira ma ta samu miji Ɗanjuma ya ce ba shi da Kuɗin aurar da ita yanzu sai dai kila zuwa gaba a tunaninta ya ƙi aurar da Zuwaira amman ya buɗe bakin Aljihu ya aurar da yaran da yake so duk ba ta san kokarin na matar kwarai ce irin Inna Meri ba
Suna shigowa lungun ɗakin Inna Meri Mu'azzam ya ce"Inna sai yaushe ne Magajiya za ta hakura da wannan zage zagen ne? Inna Meri na zaune a kofar ɗakinta ƙafafunta na mike, Bintu ta samu kafafun Inna ta yi filo da su, a yayin da kuma Walida ke can daga bayan Inna tana faman zuro kanta. Share tambayar na shi ta yi da kallon zaratan ƴaƴan nata, cikin Yanayin maganarta ta ce"Sai yanzu kuka dawo?
Mu'azzam ne ya samu gefen tabarman da suke zaune ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin " Wlh Inna sai dai har yanzu ba'a dace ba duk inda muka san za mu samu hanya mun bi abun dai sai godiyar Allah kawai."
Sai inna ta jinjina kai kafin ta kalli Mansoor da ke tsaye ya jingina kansa da garu ga takardu a hannunsa.Cikin Marairecewa ta ce"An ya Baban Inna ba za ka hakura da neman Sojan nan ba kuwa? Abu kusan shekara uku da gama sakandirin ka, kana zaune gida ba cigaba abokan karatun ka tuni sun san matakin da suka taka, ni tsiyana da kai nacin tsiya ba ka jin shawara ka yi ta kafiya kan abu ɗaya har ga ƙanin ka nan shima ya gama shekeran da ta gabata shima yana so ya biye ma ka da sai ya zama ɗan ƙwallo tunda naku burin Allah bai yarda ya cika ba sai ku watsar da ra'ayin ku, ku nemi zaɓin Allah ku samu in da kuka laɓe domin gyaran goben ku."
Ta ke faɗa cikin bayyana yadda abun ke damunta Baban Inna fa shekarunsa uku da gama makaranta amman ya ƙi cigaba ya ki kuma zuwa wajen sana'a ya na ce shi sai ya je makarantar Sojoji, kuma an yi nema har an gaji ba sa'a a wanchan shekaran wani kawun su Mu'azzamu har hanya ya yi masa ya je kaduna ya yi jarabawa amman da ta fito sunan shi bai fito ba, duk inda ya san za'a samu yaje amman ba'a dace ba shima Mu'azzam ya gama wanchan shekaran shima ba yadda Alhaji Mustspha matsayin uba yake a wajen mahaifiyarsu bai yi da shi ya nema masa jami'a ya cigaba da makaranta ba ya ce shi Ɗan ƙwallon kafa ya ke son zama yayansa kuma ya ɗaure masa kugun cewa a bar shi ya bi ra'ayinsa.
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI