*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty**SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta🥰kiyi kokari ki killace yaranki awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255
*Page 17*
Kimanin sati uku kenan da rasuwar Major Kabir Sulaiman Dabo, zukata sun fara ɗaukan dangana tuni baki na nesa da na kusa sun gama zaman makoki sun koma gidajen su. Ciki harda Dr. Sulaiman da iyalansa sai Madiha wanda daman mijinta ana yin bakwai ya koma da yara ita kuma sai da akayi kwana goma sannan ta koma.
Khadija kuma sati biyu ta yi sannan itama ta koma, itama dai kamar mijin Madiha ranar bakwai mijinta ya koma tare da yara, sai a ka bar Mimi da Hajiya sai Inna Zainaba sai kuma Inna Ladidi wacce take autarsu mahaifiyar Mommy mai rasuwa ita kaɗai ta rage musu a raye a ɗakin su.Hatta iyalan Alhaji Hamza sun dawo Gombe Hajiya kuma da Mimi sai da aka yi sati uku sannan suka yi shirin dawowa saboda ita Mimi aikinta, ita kuma Hajiya saboda makota suna ta zuwa mata gaisuwa ba ta nan. Mommy dai ta ɗauki dangana amman fa sai ana yi ana lallashi duk sanda ta tuna sai kuka rana ba ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare da ta tuna da yau ta yi rashin miji ba. Ranar da su Hajiya su ka koma sai mutuwar ta dawo musu sabuwa Hajiya ta yi kuka, kukan da ba ta yi ba lokacin da aka yi mutuwar sai yanzu Mimi ma kamar ita kaɗai aka yi ma mutuwar duk ta rame kamar ba ita ba, itama ta kasa gasgasta yau babu Abi gani take yi kamar in ta shiga Bedroom din Mommy za ta ganshi. Sai dai ina wanda ya mutu ba ya dawowa tafiya ce ta har abada sai dai fatan Allah ya haɗamu a darussalam.
Mommy ma ai ta ga kara daga abokan aikinta Saboda macece mai kirki da fara'a ita Mimi ta ɗauko wajen fara'a da iya mu'amala. Haka su Hajiya suka dawo suka bar Mommy cikin kewa Allah yasa ma ga Inna Zainabu da Inna Ladidi, ita dai Inna Zainabu ana yin arba'in za ta koma kano Inna Ladidin ne za ta zauna da Mommy har ta fita takaba. Tun da suka dawo daga Abuja yan anguwa da makota su ka ji Labarin Hajiya ta dawo a ke ta shigowa yi mata gaisuwa daga bangaran abokan siyasar Daddy ma suna ta zuwa waɗanda ba su samu zuwa can Abujan ba, har da yan'uwan su Anty da Mama da suma ba su samu zuwa can ba duk jin Hajiya ta dawo ya sa suke ta zuwa yi mata gaisuwa tare da yan'uwan mijin Yaddiko da sauran mazajen ya'yanta da ba su zuwa can Abuja ba, daman ita saboda ba ta jin daɗi kwana takwas ta yi ta biyo Alhaji Hamza suka dawo gida.
Ita Mimi ana zuwa mata gaisuwa daga wajen aikinta harda wasu mutanen da ba ta taɓa sani ba kiranta kawai a ke yi ace ta ba da address, ita kam ai ta ga kara kuma har acikin ranta taji daɗii Rukayya kaf da iyayenta sun zo mata gaisuwa har Bibi sun zo tare da Usman kamar ta yi masa maganar Aji amman sai ta fasa. Saboda ta na da tabbacin ya ji labarin babu amfani ta ci gaba da bibiyar ya sani ko bai sani ba tunda ita da ta tura masa sako da hannunta tana da tabbacin ya sani. Tun da suka dawo ba ta koma ma wajen aiki ba so take yi sai ta samu yar natsuwa.
A halin da ta ke jin zuciyarta a lokacin ba za ta iya samun wani sukunin komawa wajen aiki ba. Sai dai ta yi ta kwanciya a gida da kumburarrun idanuwana ba ta da aiki sai tunani Hajiya kuma kullum da carbi tana falo ita da Baaba Uwani, ita da ba ta nan ma aka yi rasuwar ta je kumo.
Hajiya ce ta koma ma lallashin Mimi in ta ganta cikin damuwa ta kan ce ma ta"Binta ba kuka ko damuwa Kabiru ke bukata yanzu daga garemu ba, addu'armu ita ya fi bukata shi ya sa na ce gwara ki koma wajen aiki zai rage miki zaman kaɗaici da tunane tunanen rayuwa."
YOU ARE READING
IDAN AN CIZA..!
RomanceLABARIN WASU MASOYA GUDA BIYU, DA SUKA FUSKANCI KALUBALEN RAYUWA TA FUSKAR BAMBAMCIN MUHALLI DA ASALI