Page 15.

127 9 0
                                    

*IDAN AN CIZA..!*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*

*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*

Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.

*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*

Zaku sameta  a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0

*Page 15*

Baba Ɗanjuma kuma sai maimaita faɗin" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" kawai yake  yi shi kan shi ba domin yana namiji ba tashin hankalin da suke ciki ba zai saka ya iya mallakan kansa ba. Ba shi ya haifi Mansoor ba amman da gaske yake yi ya karɓo amanarsa kuma yana jin sa kamar Mu'azzam ne shi a wajensa.
Tabbas Baban Inna ya janyo ma kansa fitinar da tafi karfinsa haka Inna Meri da Baba Ɗanjuma ke ta raya acikin ransu saboda ganin samudawan Sojojin dake tsaran gidan Major fuskarsu ba fara'a daga gani ba su san wani abu wai shi Imani ba sun fi gane yaren umarnin wanda ya ijiyesu.
Su kansu kafin Sojan dake tsaren get ya amince su shiga sai da Alhaji Hamza ya kira Yayan na shi da kansa ya yi masa mgana sannan ya kira wayar sojan sannan aka buɗe musu get suka shiga cikin gida.

  Har da Yaddiko a ka zo sai ga su kowa ya yi zaman sanyi a cikin falon gidan Major Kabir, Inna Meri tana shan kuka lokaci ɗaya tana riƙe da hannun Mu'azzam, Mimi kuma ma na jikin Mami tana wani irin kuka mai ban tausayi. Hajiya kuwa girgiza jiki kawai take yi ta kasa mgana domin kunyar su Inna Meri take ji, tun bayan gaisawar da suka yi da Mommy ga shi an kawo musu ruwa da lemu amman zullumi ya hana kowa motsi.
Hajiya ta kalli Alhaji Hamza lokaci ɗaya tana faɗin" Wai ba ka ga ya ma Kabiru har da ni aka zo ba ne?.
Cikin ladabi ya ce" Na gaya masa Hajiya, ya ce ga shi nan tahowa."
Sai kawai ta jinjina kai wani abu na taso mata acikin kirjinta.

  Murja ta kalla da ke rike da ƴarta itama daga gani ta sha kuka ba ta cikin natsuwarta. Cikin tsausayi Hajiya ta ce" Murja har ke Kabiru bai saurare ki ba ko? Kuma ba ki san inda ya sa a ka kai yaron mutane ba ko? Mommy ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Ba irin rokon da ban yi masa ba Hajiya ɗan uwansa  ma yana kuka ya roƙonsa amman bai saurare mu ba, bai sa an fita da shi ba ya na nan acikin Kurkunsa na cikin gida, ba wanda ya isa ya sa su fito da shi sai in har shi ne ya ba su umarni Hajiya." Yaddiko ta yi kasaƙe kafin ta ce"Kai jama'a kurkuku kuma ?
Mommy ta gyaɗa mata kai kafin ta ce"Eh ya na da wani ƙaramin ɗaki da bai wuce tsawon gajerun mutum ba, sannan ba shi da faɗi kuma a ƙasan yake, akan sanya mutum a ciki in ya yi wani laifi domin a yi masa horo."

  Gabadaya sai Inna Meri da Baba Danjuma su ka kara ruɗewa, Yaddiko ta saka salati Hajiya ta karishe ma ta shi ko Alhaji Hamza kai ya girgiza kafin ya ce" To duk me ya yi zafi? Wannan lamarin da duk an bi shi a hankali da an warware komai cikin sauƙi"
Inna Meri ta zube a kan kafafunta daga saman Kujera ta haɗa hannayenta waje ɗaya tana faɗin"Don girman Allah Hajiya kin yi min rai ki saka a saki Baban Inna wlh na yi miki alkwarin ko hanyar gidan ki bazan kara kallo ba har abada,ni dai ku saka ya sake shi kuma shima in sha Allahu ba zai kara kusantar Inda ƴar ku take ba, laifin yaro ne tunaninsa ba ya ba su abu dai dai in da ace yayi tunanin shi kanshi ba zai janyo ma kansa rigimar da ta fi karfinsa ba.".
Tana mgana tana kuka Mu'azzam na taya ta sai aka rasa mai lallashinta ballantana ya ce wani abu, Hajiya ke sharan kwalla a ɓoye Mommy kuma na tausayin ƴarta ne.
Ana cikin wannan halin sai ga Major kabir ya shigo cikin kakinsa na aiki wani Soja na mara masa baya.  Yana shigowa cikin takunsa na zafin nama na cikakkun mazan jiya, sai ya ɗaga ma Sojan hannu fuskar nan ba rahama shi kuma sai ya juya ya fita bayan ya sara masa.
Baba Ɗanjuma kallo ɗaya ya yi masa shima tsoronsa ya kamasa sai ga shi shima zube kan kafafunsa kusa da Inn Meri ya na rawan jiki  da na zuciya.

IDAN AN CIZA..!Where stories live. Discover now