Page 06

151 9 0
                                    

*IDAN AN CIZA..!*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*

*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*

MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT

SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA

HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU

INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM

INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI

INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL

INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
  08066726866

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z

*Page 6*

Mu'azzam bai shigo gidan nan ba sai bayan la'asar Hibba har ta gaji da jiransa, sanda ya shigo har lokacin Jummai tana bangaren Inna Meri ba ta tafi ba daman Mu'azzam ɗin take jira ko za ta samu kuɗi a hannunsa.
Tsaraba kuma sauran wanda ya rage na bangaren Inna Meri ta raba gida biyu ta ba ta rabi, daman dankali ne sai wake da garin rogo, sai siga da ya kan zo da shi a raba ma yan gida da makota.

Turamen zani guda biyun da ya zo da shi yace ɗaya Inna Meri ɗaya kuma Magajiya kuma an kai mata nata amman a inda Mariya ta sauke kayan kallon banza ta yi musu ta kauda kanta nan suka kwana kuma ba ta kauda su ba, ballantana ta ga abin da ke ciki. Ita babban bakincikin ta ita ce mace ta farko da ta auri Danjuma a matsayin saurayi da budurwa tun ya na matashin sa, amman yau daga karshe ita ce koma baya a cikin gidansa. A ce har wata banzan bassakwata ta zo ta fita matsayi aciki gidanta da tun tana da kuruciya take cikin shi. Sannan karin takaicinta gabaɗaya inna Meri ta siye kowa na gidan da kirkinta, sannan ƴaƴan gidan masu kuɗin duk ta tattare su a ɗakinta ita sai abin da ta raba ta aiko mata da shi.

  Ai in da gaskiya acikin lamarinta Mu'azzam ɗan Danjuma ne, ba ita ta haife shi ba  in ta rike kayan da AGOLAN ɗanta ya kawo mata tana kan daidanta, amman na wajen Mu'azzam ko na wajen Amina ko Halima ba ta da hakki a kansu tunda ba ita ce uwar su ba, Magajiya duk ta manta lokacin da uwarsu ta rasu da Ɗanjuma ya ce ta rike su tsalle ta da ka ta ce ba za ta iya rike ƴaƴan wata ba. Itama nata sun isheta duk ba ta duba wannan ba sai yau da suka zama wasu take tunanin ba a yi mata adalci ba.
  Tana tsakar gida tana jajjagen kayan miyan abincin dare da za ta ɗora Mu'azzam ya shigo gidan cikin shigan kananun kaya gefe ɗaya key ɗin motarsa wata bakar Jeep katuwa ne a hannunsa yana tafe yana kaɗawa shi fari ne sai dai bai kai Mansoor tsawo ba da ka ganshi ka ga Baba Danjuma saboda suna bala'in ɗibar kama da shi sosai.

  Cikin ladabinsa ya gaisheta kamar yadda ya saba shi dai ta na amsa masa cikin sakewa ba kamar ɗan uwansa da ta ce gaisuwan reni yake yi mata. Har ya gota ta zuwa bangaren Inna Meri tana kallonsa ji be sa yadda ya zama kato ya yi kiba saboda ya samu duniya. Kwallah suka cika mata ido, kaf ƴaƴanta ba mai jin daɗi a gidan auran sa,  har gwara ma Zuwaira akan Jummai ita Jummai ai kullum a gida a ke ba ta, ba ta kawo ma uwa ba. Sai dai ta bi ta karɓe Auwalu ne Namiji babba shi kuma ya ƙi karatu sai yanzu take jin haushin yadda ta zura masa ido ya ƙi makaranta in da yau ya yi karatu da Meri ba ta isa ta rika mata famkama da kudin su Mu'azzam ba, su ma ai da karatun su ke takama, ba za ta manta yadda Danjuma ya rika fama da shi akan karatu ba  ya ki yi, Ita kuma ta ɗaure masa kugun yin abin da ya ga dama ga shi nan daga karshe sai buga bugan gini ga shi ya yi aure ya tara Iyalai shima fama yake yi da kansa. Saddiqu ne bai yi aure ba har yanzu ya na can garin Ikko ya na neman kuɗi amman sai ya shekara bai zo ganin gida ba sai dai a waya sai sako da ya ke yi musu wani lokacin, shima ba sosai ba tunda Auwalu ya fi shi tausayin iyaye shi kawai domin ba shi da shi ne.

IDAN AN CIZA..!Where stories live. Discover now