❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BOOK 1 ……………………………📚✍✍
PAID BOOK : 200
FREE PAGE !!!!!!!
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 14 ❤🔥
Da gudu Nesrine ta tunkaro ta ta na kwalla mata kira amma Inaya ta ki tsayawa
Har sai da ta karaso wajen ta ta na fadin " ke Inaya ki na ji na za ki kyale ni "A hankali Inaya ta dago kan ta, ta kali Nesrine da ke ta faman haki saboda gudun da ta yi ta ce " lafya ki ke nema na haka ko yanzu ma kin zo ki ci zarafin yaya Zayd ne ? "
Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " Inaya wlh ba ki da kirki yanzu kennan duk son da ki ke ma yaya Zayd dan kin san gaskiyar shi ba makaho ba ne , ba kuma kurma ne ba amma ki ka shanye ki ka ki fada min "
Tsaki Inaya ta ja kafin ta juya ta fara takawa ta na fadin " ni ban san maganar me ki ke ba kin fi kowa sanin yaya Zayd kurma shi ne za ki zo min da wata magana cen daban kin ga ni don Allah kyale ni sauri na ke na koma gida "
Da sauri Nesrine ta bi bayan ta , ta dafa kafadar ta
Cak Inaya ta tsaya ta juyo ta na kallon ta" Inaya ki na son ki ce min ba........." kut maganar ta yanke sakamakon wata mota da ta tunkaro su da gudu
Sarai Nesrine ta gane waye ke cikin motar , har sai da gaban ta ya fadi ta na zaro idanu
Kallon ta Inaya ta yi sannan ta juya ta kali motar da ta nufo su da mugun gudu
Dan rumtse idanun ta tayi sannan ta bude a kan motar dai'dai lokacin da ta ke jan wani wawan burki har sai da kura ta tashi
Motar na tsayawa Hafiz da Moctar su ka fito da ga cikin motar
Inaya na ganin Moctar ta saki tsaki ta kauda kai gefe , ta juya za ta bar wajen
Da sauri ya sha gaban ta ya na fadin " ina kuma za ki je ko gaisawa ba mu yi ba"
Hararrar shi ta yi da ga sama har kassa ta ce " ka ga malam ka bani lafya na fada maka ni matar aure ce "
yar karamar Dariya ya yi kafin ya ce " yo ai ni ma mijin aure ne "
Tsaki ta ja ta raba ta geffen shi za ta wuce
Da sauri ya riko hannun ta ya na fadin " ki tsaya ki ji mana ! "Cikin zafin nama Inaya ta juyo ta wanka mishi wani gigitacen mari ji kawai ka ke tassss
YOU ARE READING
EXILED PRINCE 🔥
RomanceKaddara Ita ce silar faruwar wannan labarin , Soyayya ita ce ta dauki nauyin labarin , tsarawa da shirya wa kuma na bar wa izza da Mulki , ba da umarni bakin ciki da Hassada