TWENTY ONE 🔥

50 0 0
                                    

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
                                    
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

       



( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )






STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥


Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY






TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i









BOOK 1 ……………………………📚✍✍





PAID BOOK : 200




            FREE PAGE !!!!!!!




♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡




PAGE 21 ❤🔥




              Da sauri Moussa ya tsagaita dariyar shi ya ce " ban gane , Amir wai ka na nufin baza ka koma gida ba, me ya sa abun da ya faru ya riga da ya wuce "

Katse shi Zayd ya yi da cewa " Diya na sani , kuma har ga Allah ina kewar Ammie da mamie da kuma Tesnim amma zuciya ta bata yarda na koma ba , ina ji idan na koma wani mugun abu zai faru wanda ya fi na farko , ina jin tsoron komawa ta ga ahali na ya janyo musu assarar sa bazan maye gurbin ta ba , Diya ka fi kowa sanin Malik a ka so a kashe ba ni ba , akasi ne kawai aka samu ranar ni na kwana a part din shi , da yanzu na san shi zai mutu a madadi na , dalilin da ya sa su ka kyale shi yanzu dan sun san ba shi da wanda zai gaje shi , ko ba su kashe shi ba in lokacin shi ya yi dole zai tafi su zauna saman karagar mulkin "

Dafa kafadar shi Moussa ya yi kafin ya ce " na sani Amir , amma dole ka koma ka karbi kujerar ka , yanzu ka na ji ka na gani wani zai zauna saman gadon ka , Amir kai kade ne fa magajin Daular saudiya tsawan shekaru sama da dari biyu duk sarkin da ya hau karagar muliki ba zai taba haifuwar da namiji ba , cikin wani ikon uban giji mai martaba ya same ka , ba ka ji sunan ka ba Nawfel , kyauta mai daraja , ba a banza a ka saka maka wannan sunnan ba "

Jingina bayan shi Zayd ya yi a jikin sofar ya lumshe idanun shi ya ce " Diya na san wannan dukka, amma ba yadda zan yi kassan ba zan iya tafiya na bar yarinyar nan ba ko "
Ya kai karshen ya na bude idanun shi ya kali Inaya da ta sharar barcin ta kamar babu ita a wajen

" shikenan yanzu ina son ka fada min za ka koma masarauta ko kuma ba za ka koma ba " Moussa ya tambaye shi

Dawo da kallon shi ya yi kan Moussa kafin ya ce " za mu koma Diya, za mu koma amma ba za mu zauna ba , tafiyar tsaye za mu yi "

Ya na gama fadar haka Inaya ta fara motsi ta na son tashi 

A tare shi da Moussa su ka dawo da kallon su saman ta

A hankali ta ware idanun ta , ta fara karanto adu'ar tashi da ga barci , ta fara bin wajen da kallo

Idanun ta na sauka kan Zayd ta saki wani dan murmushi ta mike zaune ta kai hannun ta guda ta na murza idon ta cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd tun da safe na ke ta jiran ku ku dawo mu yi breakfast har kwana ya dauke ni "

EXILED PRINCE 🔥Donde viven las historias. Descúbrelo ahora