❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ❤👑
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BOOK 1 ……………………………📚✍✍
PAID BOOK : 200
FREE PAGE !!!!!!!
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 26 ❤🔥
Da kallo ta ke bin shi cikin zuciyar ta ta na tambayar kan ta wanene Zayd
Ta yi nisa cikin tunanin ta ta cintsi murya shi ya na fadin " konta ki yi barci ina zuwa "
Da to ta amsa mishi sannan ta saki hannun shi ta zauna bakin gadon
Shi kuma ya ci gaba da takawa ya nufi daya daga cikin kofofin geffen dressing mirror
Ya na shiga ta ida Hayewa gadon ta konta
Bayan wasu mintina ya fito daga toilet sanye da bathrobe , bai tsaya shafa lotion ba ya wuce dayan door ya shiga dressing room
Jim kadan ya fito sanye da kayan barcin shi ash colour ma su kyauGadon ya nufa ya Haye geffen guda ya konta ya na fuskantar ceiling
Cen ya juyo da kan shi ya na kallon ta , ta juya mishi baya har ta yi barci
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanun shi ya sake bude su slowly a kan ta
Cikin sanyin murya ya ce " ko na fada miki ba za ki gane ba , asali ma ni da kai na ban san abun da ke damu na ba , amma na san duk lokacin da na ke tare da ke ina jin sauki a cikin zuciya ta , ina ji a jiki wani mumunar abu na shirin faruwa da ni kamar zan rasa wani abu mai mahimanci a rayuwa ta , duk da san ba tabas abun da na ke ji ya faru ba , amma ba ni fatan na rasa ki cikin rayuwa ta , dan a yanzu ke kadai ce family na , na so na yi miki irin son da ki ke yi min amma zuciya ta ta kassa ban san dalili ba "
Ya kai karshen ya na juyo da kan shi ya fuskanci ceiling ya lumshe idanun shi
Kamar da ga sama ya tsinci wannan zazzakar Muryar ta ta, ta na fadin " na sani yaya Zayd ba laifin ka ba ne dan ba ka so na , laifi na ne da na fada soyayyar ka da karancin shekaru na , na yi maka alkawari zan yi kokarin na cire shi da ga cikin zuciya ta "
Cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " ni ban ce ki cire shi da ga cikin zuciyar ki ba "
Slowly ta juyo ta kaleshi, sannan ta ce " me ya sa to baza ka iya so na ba , ba ni da kyau ne ? "
" pleaseeee ni ba wannan ba , kin fi kowa sanin ki na da kyau Masha Allah "
" to minene matsalar yaya Zayd ? " ta fada kamar za ta yi kuka
YOU ARE READING
EXILED PRINCE 🔥
RomanceKaddara Ita ce silar faruwar wannan labarin , Soyayya ita ce ta dauki nauyin labarin , tsarawa da shirya wa kuma na bar wa izza da Mulki , ba da umarni bakin ciki da Hassada