CHAPITER ELEVEN 💋

19 0 0
                                    

⚘ EXILED PRINCE ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥







( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )







BY : MEERAH ❤✌




Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺





TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION

👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY





TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡








PAGE 11 ❤🔥








Dan zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon ta cike da tantama ta ce " wai Inaya me ya ke damun ki ne , inda ya na magana duk shekaru hudun nan da mu ka yi tare da shi me ya sa ko kalma daya ban ji ta fito da ga bakin shi ba , kennan a haka ku ke rayuwa cikin gidan na shi , kennan rayuwa da kurma na yi miki dadi ? "

Mikewa tsaye Inaya ta yi ta dauki jakar ta ta na fadin " kin ga Nesrine ban san me ya sa ba ki son yaya Zayd ba, ni fa ina son shi a haka kuma duk abun da za ki fada bazai sa na daina son shi ba , ku duka kallon kurma da makaho ku ke yi mishi amma ai ni ina gane abun da ya ke fada kuma da makaftar tashi ya ke aiki , kin ga ya fi karfin a ce mishi makaho kin ga idan ba za ki fadi abun al'heri a kan yaya Zayd ba ki daina yi min magana "

" Inaya yanzu saboda wancen banzan za ki fada min haka , minene shi a wajen ki , da ga na fada miki abun ya ke gaskiya "

" Gaskiya guda ce , ina son shi a haka , wai shi makaho ko kurma ba shi da zuciya ne , kafin ki yi min wannan maganar ki je ki fadawa Abba , ai shi ya bawa yaya Zayd aure na , da bai yarda da shi ba , ba zai yarda ya aura mishi ni ba "

marairaice fuska Nesrine ta yi ta na fadin " yanzu Inaya kin fi son wacen mutum a kai na , ni Nesi din ki , me Zayd din nan gare shi da har idanun ki za su rufe a kan soyayyar shi , me ya ke da shi , da sauran mazan duniya ba su da shi , dama zama da makafi na meda mutum makaho ? "

a hankali Inaya ta girgiza mata kai cikin sanyin murya ta ce mata " a'a Nesrine ke ce dai makafniyar , har yanzu idanun ki sun kassa gwada miki , kyakyawar zuciyar yaya Zayd , Soyayya ta ita ce ya ke da , kuma har abada babu namijin da zai same ta , Nesi wai ya ki ka sauya lokaci guda haka ? a sani na ba haka ki ke ba , ba ki kaskantar da mutane kamar haka ko ma dai minene zan so ki sani , yaya Zayd dai miji na , kuma a hakan na ke son shi , a hakan zan zauna da shi , idan ki na jin haushin hakan ki kashe kan ki ki huta "

( TO FA YAU A TABO BABYN ZAYD 🤣🤣🤣🤣 )

Ta kai karshen ta na juyawa za ta bar wajen kawai sai ta ji ta bugi mutun

Dan bayan kadan ta ja ta dago kai ta kaleshi ta ce " sorry "

Murmushi kadan Moctar ya yi kafin ya ce " ba komai "

Da sauri ta raba ta geffen shi za ta wuce
Da sauri ya riko hannun ta ya ce " haba ina kuma za ki je , ni fa wajen ki na zo "

Cikin bacin rai Inaya ta kwace hannun ta ta juya ta fara takawa za ta bar wajen

EXILED PRINCE 🔥حيث تعيش القصص. اكتشف الآن