CHAPITER NINE 💫

28 0 0
                                    

❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤



(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )






STORY & WRITTEN BY : MEERAH❤💫



Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY






BOOK 1 .................................📚✍✍





[14/08/2024]







♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡







PAGE 9 ❤🔥




▪Zayd




zaune ya kebakin gadon shi ya na rike da wayar shi , ya na sanye da jeans navy blue , da T-shirt white color , amma ya cire bakin glass din shi

ya na a haka Moussa ya shigo Dakin ya na sallama
cen kassan makoshi ya amsa mishi sallamar shi , ko shi kan shi Moussa bai ji amsar ba
Geffen shi Moussa ya tako ya zauna sannan ya ce " Amir ! "

Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce mishi " uhmm ? "

" Amir na yi tunanin maganar da na yi maka za ka saurare ni , wai me ya sa duk abun da na fada maka in dai ba ka niya ba baza ka yi shi ba , yanzu sati guda da ka je gidan su yarinyar nan ka dauko ta amma ko kalma daya ba ka taba ce mata ba , ka ce min akwai binciken da ka ke son yi a kan ta, in ba ta zauna kusa da kai ba ta ya za ka yi binciken , Zayd wlh ba na jin dadin abun da ka ke mata , shin minene laifin ta a ciki, ka na ga karama ce sosai ko ba za ka iya soyayya da ita ba ka kula da ita a matsayin kanwar ka mana "

Shi dai Zayd ko dago kai bai yi bare ya ce mishi wani abu ya na ci gaba da latsa wayar shi

Sai da Moussa ya gaji da zubar shi sannan ya ce " Amir ni ina son in san dalilin da ya sa aka aura maka ita "

Wannan karan sai da ya dago kai slowly ya kale shi kafin ya ce " a kan hakan ni ke bincike "

Dan zaro idanu Moussa ya yi kafin ya ce " ban gane ba kawai malam zowa ya yi ya ce ka aure ta kai kuma ka yarda ? In da ba ka son ta na minene za ka yarda "

Ajiye wayar hannun shi ya yi saman bedside drawer sannan ya juyo da kyau ya kali Moussa sannan ya ce mishi " ba haka ba ne , shekara biyu baya , lokacin ka tafi Abuja dibo company , dai'dai na fito da ga cikin gida na hadu da malam ya na tafiya da sauri ko kallon gaban shi ba ya yi, a haka har ya kai min karo ya yi baya zai fadi , bayan na taro shi ya na yi min godiya kuka ya kubce mishi har da hawaye ya shiga yi min wasu magaganun allamun ya fita cikin hayacin shi , na yi matukar mamaki ya babban mutun na kuka haka kamar karamin yaro , na so na ji dalilin kukan na shi , sai na ja hannun shi mu ka shigo gidan nan na zaunar da shi sannan da hannu na tambaye shi minene ya ke kuka nan ya ke ce min " Zayd kashe min auta ta za su yi yanzu shekara biyu ina boye ta amma ina ji a jiki na wannan karan sai sun gano mu ban San ya zan yi ba , ita ce farin ciki na , ba zan iya jure rashin ta ba Zayd na shiga uku na " ni sam ban gane abun da ya ke nufi, sai na tsaya ina kallon shi ina son in karanci abun da ya ke nufi, sai da ya ida kukan shi sannan ya riko hannu na ya ce min " don Allah Zayd ina son in roke ka wata Alfarma " jinjina mishi kai na yi , ina kallon shi ya mike tsaye ya dawo gaba na ya zube saman guyiwowin shi ya ce min " don Allah Zayd ina son ka auri Inaya " a rude na mike tsaye ina fadin " what aure ? " mikewa malam ya yi ya na zaro idanu ya na kallo na ya ce " Zayd, dama ka na magana ? " ban amsa mishi tambayar shi ba na ce " uncle yi hakuri gaskia babu aure a sha'anin rayuwa ta bare kuma wannan yarinya ta yi min kannanta " komawa ya yi ya zube saman guyiwowin shi ya riko kafafuna ya roke ni da na yarda na aure ta in ba haka ba komai zai iya faruwa da ita kuma duk abun da ya faru da ita da hannu na a ciki tun da na samu damar ceton rayuwar ta amma na ki duk ya bi ya kashe min jiki ba yadda zan yi na yarda , a ranar a ka aure na da ita, limamin massalaci ya zama waliyi na, shi kuma malam na ta , na biya sadaki a ka aura mana aure , duk lokacin da na tambayi malam dalilin da ya sa a ka aura min ita sai ya ce min in bari in lokacin ya yi zan sani , dalilin da ya sa na ce yanzu ta dawo gaba na na dinga ganin ta ko zan gano dalilin da ya sa malam ya aura min ita " ya kai karshen ya sauke ajiyar zuciya ya dan lumshe idanun shi dan ba karamar wuya ya sha ba wajen yin wannan maganar duka , ji ya yi kamar harshen shi zai fado kassa

EXILED PRINCE 🔥Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon