Ta tashi da safe cikin bacin rai da tsananin kaunarsa, ta rasa abinda yake mata dadi, tunani take a ranta tana cewa yanzu shikenan habibi na, sahibina, abin kaunata za'a raba ni dashi, zaa shiga tsakanina dashi, ya Allah ka kawo min dauki, ka shiga lamarin nan ka hanasu ikon rabamu.Magana take a zuci ashe ta fito fili. Se kawarta tace Amna keda wa kike ta magana haka kuma ga hawaye a fuskar ki. Me yai miki zafi haka? Me ya sa zaki bata hawayenki a banza a wofi? Me ke damunki?
Se ta tashi zaune.
Tace Yusra kinsan so kuwa? Kinsan me ake kira da kauna? Kinsan in kana son mutum fiye da kanka ya kake ji? Kinsan bala'in so kuwa? Bari na baki labarin habibina Adil kuma in ina ce miki Adil ki dinga kallon sunan a ranki kina hango fuskarsa a matsayin Adil din. He is so cute, charming and lovely and i dearly, truthfully and sincerely love him. Yusra tace to bani labarin meya faru? Seda ta numfasa sannan ta fara.Tace Yusra! Tana hawaye. Yusra watarana an aikeni kasuwar tarauni na hadu da Adil. Naje zan sai ma mami kaji zatayi girki, baba zeyi baki. Ya fito kenan da keys din mota a hannunshi ni kuma na shiga hannuna rike da wayata a kunnena ina magana da mami tana sake bani wani sakon. Ya kalleni sosai ni kuma a raina nayi tsaki nace maza se kallon tsiya na wuce.
From the quick glance dana mishi na gane fari ne, kyakykyawa, mara jiki, dogo kuma dan gayu ne sosai.
Da dare misalin 10:00 na gama shiryawa nasa kayan bacci, na yi ma mami good night, Mami tace min ki tashi da wuri Amna saboda kar kannenki su makara a makaranta. Ki tsaya Asabe ta shiryasu, Saratu ta musu abinci, sannan kisa Audu driver ya kaisu school. Dan Allah kada su makara'. Nace to mami.
Night.Na shigo dakina na kashe fitila na kwanta akan gadona. Na rufa kenan se wayata dake charging ta fara kara. Da kamar bazan daukaba se kuma kawai na mika hannu kan side drawer din na dauka ina gyara kwanciyata na kara a kunnena nace 'hello'.
Se naji wata sanyayyar murya tace 'hello anmata' ya kike? Ya gajia? Se nace am fine amma wake magana pls? Yace sunana Adil dazu mun hadu a kasuwa na so na miki magana amma naga kina waya kuma kamar sauri kikeyi, banaso na dameki. Kuma na lura da motar da kika sauka daga, sena karasa na gaisa da driver din na tambayeshi numberki Allah kuma cikin ikonsa ya bani. Shine na kira na gaisheki na kuma ce you are preity and cute!
I was speechless at the moment.
Se yace ya kikayi shiru? Bazaki fada min sunanki ba? Ko bakya so mu dinga gaisawa? Nima Mumma(sunan da yake kiran mamanshi dashi kenan) ce ta aikeni amma naji dadin aiken tunda na hadu da ke a dalilinshi.
Duk maganar da yake na kasa cewa komai. Ina ta sauraron the most sweetest and calm voice da na taba ji a duniya, inata tunani dama akwai maza masu sweet voice haka?
Yace preity princess ba zaki fada min sunanki ba?
A nan ne nace Amna sunana! Thanks for d care, i really appreciate. Amma kayi hakuri yanzu bacci zanyi we'll talk tomorrow inshaAllah. Se yace to goodnight Amnan Adil. Be kara da komai ba ya kashe wayar ni kuma na juya na gyara kwanciya zanyi bacci.Bacci yace inaaaa...
...ai ba ke ba bacci yau dan haka naita juyi naita juyi na kasa rintsawa inata tunanin Adil a yanda na ganshi da soft voice dinshi.
Da naga abu yaki ci yaki cinyewa sena tashi na dauro alwala nayi sallah na dauki Qur'ani naita karatu har asuba. Seda nayi sallah sannan na fita na tashi yara muka fara shiryasu.Kannena uku mata, yayyena uku maza Ya Muhammad, Ya Ahmad da Ya Mahmud kannena kuma Manal, Minal da Aida. Mu 7 ne mami ta haifama baba. Sunan Babanmu Alhaji Kabir Idris shahararren dan kasuwa ne saboda haka ba abinda be wadata mu iyalinsa dashi ba, amma baya daukan nonsense a gurin kowa.
Mami sunanta Hajiya Maryam Kabir. Mace ce me ibada da tarbiya ga 'ya'yanta. Ba abinda tasa a gaba irin yi mana tarbiya da ibadarta dan ita ko shige shigen makota batayi. Se da kwakwkwaran dalili take shiga.
Bayan sun tafi na hada komai da nake hada wa mami as usual saboda inta tashi yi ma Baba breakfast base ta taso ni ba.
YOU ARE READING
❤MAHBUBI❤
RomanceLabari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...