Babi na 3

2.2K 99 4
                                    


An dan 'bata lokaci amma da yake tana da dan sauri ba'a dad'e ba, na saka kayana aka daukeni da cousins dina a Range Rover Baba aka tafi kaimu wurin biki Fabs.
Ina shiga na gagga friends dina sunsha anko naita mamaki ya akai suka san bikin ma? Ya akai har sukayi anko? Nida na shagalta da soyayya ko gayyatosu ma banyi ba bare na kai musu anko. Se ga Yusra acikinsu itace ja gaba. Yusra childhood friend ditace gidanmu jikin na juna. Tare muka taso komai tare mukeyi har amincin iyayenmu ya karu saboda mu   kuma a gidansu akwai yayyanta abokanan yayuna. Ita kadai nake iya fadawa sirri na, bana 'boye mata komai. She is my best and dearest friend. Muna tare har secondary school se baban ta ya samu aiki a Qatar ya koma can da iyalansa da zama, ba yanda beyi ba Babana ya bada ni mu tafi tare muyi jami'a mami taki.
Yusra tace Amna fuskarta cike da murna da kauna ta kuma rungumeni nima na rungumeta nace yanzu Yusra ko 'yar wayar nan ma babu kuma kinsan bazan san numberki ba se kin kirani. Ta ce sorry! Amare basa fishi ranar bikin su zanyi miki bayani bayan biki. Ta ja hannuna tare da sauran friends dina suka raka amarya har kujerarta tare da wani cool music da yake sani tina Adili na.
Aka sha biki, akai rawa, akaci aka sha kowa alhamdulillah sannan akai closing prayers aka tashi. Kowa inze fita da souvenir dinshi za'a bashi. Dangin ango sunsha karamci sunata godiya suna cewa se munzo dinner su ranar daurin aure muma mukace se sunzo tamu gobe.

Muka koma gida na cire kaya muka zauna hira Yusra dama da akwatinta a gidan zata tayani kwana. Muna hira nasa a kawo min tea nasha se nake tambayar Yusra ya akai bansan tazo ba. Shine take ban labarin yadda mami tace karta bari na sani da yadda mami tasa tayi shirye shiryen wurin biki da yadda mami ta sata ta nunawa friends dina anko da yadda mami tasa tayi min rabon kati. Nace au duk kina gari har tsahon haka amma ki ka qi kibari na sani. Na kwala mata empty kofin tea dina dana shnye. Muna ta hira har bacci ya kwasheni saboda gajia. Ranar ma ban kira Adil ba.
Washegari ma aka tashi da hidima shima ban kirashi ba. Har aka gama biki aka kakkaini gidajen 'yan uwa fada aka kuma ce a bari se lahadi kai amarya gobe kenan. 'Yan uwa duk sun tafi da yake wasu sunje jere wasu kuma an kaisu sun ga gidan kafin amaryar ma. Se na gari ne zasu kai amarya.

Se a daren ranar asabar ranar da aka daura min aure. Hidima ta kare. Ansha biki me suna biki kowa ya tafi yana fatan alkhairi an kuma yi rabuwar alkhairi da kowa tare da fatan Allah ya kaisu gida lafiya. Daga ni se Yusra muna ta hira yau ma har take bani labarin Qatar da yadda babanta ya hanata rike waya da karatun da tayi. Tace Amna kasar larabawa akwai luxury kuma muna kan ganin duniya. Komin jin dadin bature Amna in kaga na balarabe seka sara masa. Haka mukai ta hira muna dariya. Ta bani labarin wani daya takura mata wai zata zageshi tace 'anta majnun' mukai ta dariya. Tace banfa san me nace masa ba kuma ina fada na shige mota na bar wurin. Se wurin 1am muka gama hira muka kwanta saboda yau bazamu iya kaiwa asuba ba mun gaji da yawa. Ranar ma ban kira Adil ba. Tun daga alhamis har yau asabar ga lahadi ta shigo ban kira Adil ba shima be kirani ba.
Washe gari ina farkawa da asuba ina tashi nayi sallah na kira Adil da yake Yusra bata tashi ba tana fashin sallah ni kadai nake buduri na a dakin. Ina kwance na dakko wayata nai dialing numbersa ringing daya ya daga naji yayi wani deep breath daya shiga har cikin ransa am sure! Kafin nayi magana yace Amna kwana na 4 ina jiran kiranki, Amna shikenan an rabamu, shikenan zaki barni. Har 4 good days baki ko tuna dani ba habibti? Me nayi miki Amna? Me nai nayi deserving hakan? Ramawa kikeyi ko? Nasan ban kyauta miki ba a baya amma nafi shiga tashin hankali a kwana hudun nan. Ya ce ya shbhanallah!!! Da karfin gaske sannan yace Amna bani da lafiya, Amna a kwance nake kwana hudun nan ko masallaci bana iya zuwa komai a daki nake yinsa saboda zazzabi da ciwon so. Dakyar na yadda Baba ya kaini asibiti jiya na karbi magani saboda numfashi na daukewa yai tayi.

Kullum chajin wayata nake na sa ta a vibration na dorata a kirjina ina jira ko zaki kira se yau Allah yayi. Gashi na hana kaina kiranki dan kar na takura ki ko naje wayar bata ma hannunki. Ya kara cewa ya Salam!
A sannnan ne na dawo hayyacina na gane cewa na lalata komai, nama tuna cewa bikina ma akeyi, na tuna mantawar da nayi da Adil. Se nima na fara masa kuka ina kuka ina ya Allah na shiga uku. Adil bansan abinda na tafka mana ba se yau yanzun nan na gane inda na kaimu. Inata kallon komai a matsayin wasa amma yau nayi realizing komai gaske ne. Adil ya zamuyi? Ba na son Nasar bana son kowa se kai kuka yazo min da karfi ya hanani kara cewa komai. Kowa yai shiru muna ta kuka  har tsahon awa guda bamuyi magana ba. Chan naji muryashi yana cewa i love you Amna! Loving you is part of me Amna! You are the only person am born to love! I will continue loving you for the rest of my life!
Se yace Amna kina da aure yanzu, bani da hurumin miki magana ko a waya, kisa a ranki munyi sallama, karki sake kirana, daga yanzu ma zan cire sim din na karya dan ki dena samuna koda kin kira. Yanzu ma muce astagfirullah saboda mun keta haddin Allah mun keta layin daya sa mana. Muyi hakuri da juna Allah ya sa hakurin ya zame mana alkhairi. Yace na barki lafiya Amna kima mijinki biyayya ki manta dani dan Allah. Ya ajiye wayar kafin na sake cewa komai naita re-dialling switched off. Ya Salam!!! Anan tashin hankali yazo, anan azabar so ta dawo, anan na shiga radadin rayuwar duniya, anan na zabi mutuwa ta. Nasha kuka nayi na kuma har na gaji na goge hawaye na.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now