Yanata tunani me zurfi, a ransa yana ta kokonton anya ba karya take ba? Wane ciki kuma?
Yaushe ta samu ciki?
Se kuma ya dinga tuno maganganunmu na karshe da mukayi a matsayin sa'insa. A ranshi ya dinga tuna sanda tace masa "kayi hakuri, inshaAllahu komai ya kusa zuwa karshe".
Ya ce to ko abinda take nufi kenan? Guduwa zatayi dama? Se kuma yace to ai bani da tabbacin ko guduwa tayi ma a yanzu.Yana tunani a ransa, se kuma yaji an ci gaba da magana.
Mamanshi, Hajia Aisha yaji tana magana.
Tace oh ni 'yar nan! Nidai bansan Amna da wani hali na ki ba, duk yanda akayi yaron nan ne yayi mata wani abun, duba da abinda Muhamamdu ya fada.
Saboda haka Alhaji Abdullahi a tuhumi yaron nan muji me ake ciki. Indai ana son gaskia ta fito. Saboda shi ze fimu sanin komai tunda shi yake zaune da ita gida daya. Shi zefi sanin halayenta fiye da kowa anan.Baba Abudullahi yace hakane gaskia, saboda yarinyar ba wanda ze shede ta da wani hali mara kyau.
Yace "kai Nasar muna sauraronka".Nasar ya fara rawar murya, duk abubuwan da yake faruwa tsakaninmu yaita fado masa a rai. Ya rasa ta inda ze fara, se kawai yayi shiru ya sunkuyar da kai yana hawaye.
Sukace kayi shiru, muna saurarenka.
Nasar yana share kwalla ya ce
"Wallahi tunda na san Amna ban taba saninta da wata matsala ko tawaya ta ko wane bangare na rayuwa ba".
"Bata bata min rai haka kurin, in kaga munyi sa'insa to kureta nayi".
"A wurin Amna na samu abubuwa da yawa da maza basu samu ba".
"Bata taba gajia da gyara mana gida ko min girki ko kuma kula da yarana da tarbiyyarsu".
"Amna mutuniyar kirki ce da kadan ne irinsu a duniya".
Yaci gaba, a yanzu ne da ake maganganun nan, da abinda kowa ya fada nake tuna lokacin da mukai sa'insa da ita a kwanan baya akan hakkinta take ce min "komai ya kusa zuwa karshe" inaga shiyasa ta yanke hukuncin guduwa.Kowa yayo kansa cha cha cha, seda ya Muhammad yace dan Allah ayi mishi hakuri ya karasa magana. Se Babanshi da yayyanshi suka hau fada, ba za'a barshi ba. Me ya hadasu sa'insar seya fada.
Yana karkarwa yake bada labarin wasu abubuwan dake gudana a tsakaninmu, amma be nuna laifinshi ko daya ba, kuma be fadi exactly yadda abin yake ba, se ya hahhada magana ya kitsa musu.
Sukace to banda abin Amna daga samin matsala da bata taka kara ta karya ba menene na yanke hukunci me tsauri haka?
Ya dirka karyarshi ya dauke hankalinsu daga ganin laifinshi. Aka yi addu'a aka tashi daga taron.
An yanke hukuncin ci gaba da nema ta har Allah yasa ta bayyana. Dan sunce in an ganta, anga yaran. Shidai yayana be yadda da Nasar ba kwata kwata, amma dai bayason ya nuna hakan yaja hayaniya se kawai yayi shiru. Da ya koma gida yake fadawa Yusra.
Manal kullum se tayo waya gida. Tafi kowa damuwa, kullum cikin kuka take. Ba yanda batayi da Yaya Muhammad zata taho gida, ya hanata, yace mata in kinzo za'a ganta ne? Kawai kita musu addu'a Allah yasa hannu na gari suka fada in ma wani abunne ya faru dasu.
Take cewa Mukhtar ni nasan Allah kure yaya Amna akayi ta yi haka. Don tunda na taso na santa, ita bame tashin hankali bace, ba kuma ta daukan abu da zafi, itace meyi mana fada kuma ita ke nuna mana cewar a duniya hakuri akeyi. Duk sanda na mata waya daga nan kafin muyi sallama seta kara fada min nayi hakuri na dinga maka biyayya ina kwantar maka da hankali. Haka zatayi ta masa kuka yana lallabata yana bata hakuri.
***************
Mun sauka a Dubai, mun fito daga jirgi muka zauna a airport a wurin wa'anda suka sauka a raina ina ta tunanin ina zamu dosa yanzu? Zuciyata ta dan fara karaya. Da muka dan huta muka tashi, na sai sim card, sannan na sama mana hotel a cikin airport muka kai kayan mu zamu kwana daya da safe mu shiga gari na nema mana wurin da zamu sauka.
YOU ARE READING
❤MAHBUBI❤
RomanceLabari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...