Babi na 28

1.5K 67 0
                                    

Adil yace Baba bari naje na karbo yara kar Ummi ta tafar min da su.
Baban yace hakan yana da kyau.
Adil ya shiga cikin gida ni kuma na tashi na yima Baban sallama na tafi mota na zauna. Ina jira ya fito naji ko nayi gaba ko kuma na tsaya.

A cikin gidan har 'yar uwar Ummi tazo dukansu fuska ba annuri. Kanwar mahaifinta ce tana tayi mata fada akan me ta aikata ta jama kanta wannan masifar. Ummi tana ta kuka ba kakkautawa Adil yayi sallama, suka gaisa, yace 'ya'yansa yazo karba dan ba zata tafar masa da su ba. 

Ummi ta fara dagewa ita ba zata bar yaranta ba. Kanwar mahaifinta da take gurin ta ce mata ai kuwa dole ki bashi 'ya'yansa. In kin tafi dasu gidan uban wa zaki kaisu? Taita zaginta tana mata fada. Ya kwaso yaransa suma suna kuka za'a raba su da mahaifiyarsu ya zo ya bude mota ta ya ce su shiga mu tafi shi akwai guraren da ze je kuma be gama hira da Alhaji ba. In ya gama ze zo ya samemu. Nace to se ka dawo. Ya dago mana hannu muka fice shi kuma ya koma ciki.

Sun gama hada kayanta kaf wurin yamma likis suka sa aka saka musu a mota suka kwasa suka nufi gida.

Asalin ummi 'yar cikin gari ce wata unguwa zage. Kusa da kasuwar kurmi. Anan iyayenta suke. A zagen ma a cikin lungu can kasa suke. Gidansu gidan gargajiya ne tun ginin kasa na da wanda kaka ya mutu ya barwa iyaye kowa ya yanki gurinsa bayan an raba gado. A gidan kannen Babanta da matan su da yaransu gaba daya suke. Mutum ba ze taba tunanin akwai irin gurin a cikin babban gari kamar Kano ba.

Mahaifiyar Adil da yake iyayenta 'yan unguwar ne, amma su daga bakin titi gidansu yake. Anan ta san mahaifiyar Ummi, tare sukayi islamiyya da makarantar dare. Saboda ta yaba da tarbiyyar mahaifiyar Ummi ne yasa take son danta ya auri Ummi. Kuma har da burinta na bata so ya auri 'yar boko ta mallake mata da.

Tun a mota kanwar mahaifinta hajia Salame take mata fada ba kakkautawa. Tace ai kinyi wa kanki.

Iyayenta duk da fama da talauci da suke mutanen kirki ne. Suna da tarbiyya da karatun al qurani. Itama Ummi duk da iyakacinta secondary tana da ilimin arabiyya sosai saboda yawan islamiyoyin dake cikin gari da kuma iyayenta masu son karatu ne.

Suna isa gida ta shiga jikinta a sanyaye, idanunta se zubar hawaye sukeyi. Dama tunda tayo waya gida tana kuka, lokacin salame na nan. Baban nata mal Haruna yace salame tashi kije ki ji me ke faruwa da Ummi. Baban yana son Ummi saboda sunan mahaifiyarsa aka saka mata shine suka boye. Kowa yayi jugum jugum yana jiran yaji me ya faru tayo waya tana kuka.

Tana shiga gidan tana kuka duk suka mike suna me ya faru?
Ummi ya ya akayi?
Salame ta shigo tace ta wuce ciki ta zauna tukunna tana jira Yayanta ya dawo daga masallaci se tayi bayani.

A dakin mahaifiyata, Salame take cewa Hajiya ladi(mahaifiyar Ummi) an sake ta. A tsaye ladi take, bata san sanda ta saki abin hannunta ya fadi ya zube ba, itama tayi da6ar a kasa, idonta ya fara kwalla. Tana ta kiran innanillahi wa inna ilaihir raji'una.

Suna zaune kowa yayi jugum malam Haruna ya shigo ya ce ya naga ana ta shigowa da kaya? Na menene? Ya gansu duk sunyi jugum suna salati ga hawaye fal fuska.
Ya nemi wuri ya zauna yace da su lafia? Ba wanda ya ansa seda ya sake magana da tsawa yace ina magana duk kunyi shiru ko bakwa jina ne?
Nace daku lafiya?
Me ya faru?
Salame tace ai se kiyi magana Ummi.
Ki fadi me ya faru daga farko har kashe.

Malam Haruna yace bana son shashanci gaku iyayenta a gurin kuma se nayi magana da ita? Bayan ke nace kije kiji me ke faruwa kuma kya dawo kice nayi magana da yarinya?

Salame tace yaya mijinta ne ya sake ta. Ya doka wani dogon salati.
Yace garin yaya?
Me ya faru?
Ina yabon yaron nan da halinsa amma ya rangada min wannan mummunan aiki?
Salame tace shiyasa nace maka tayi bayani. Ga miciji a nuna masa ja?
Ai ita zata zayyano dukkan abubuwan da suka faru daga farko har karshe muji dalilinsa nayin hakan. Ai ruwa baya tsami banza.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now