Babi na 20

1.6K 75 2
                                    

A gida Adil yake ce wa Ummi zamuyi walima saboda yaran nan da aka samu. Amma ke nakeso ki tsara mana komai, ki shirya mana yadda kikaga ya dace. Ko ya kika gani?
Yace ki yi list din duk abinda kike ganin ya dace da wanda ze isa se ki min magana.
Cikin murna da farinciki tace to Baban Ra'is inshaAllahu. Ta kuma ce amma Amna ba zata ji haushi ka kawo min harkarta nayi ba?
Yace indai itace ba ta da wannan matsalar, ita zata ma fi son hakan.
Ya ce ki same ta kuyi shawara se tai guiding dinki through tunda kinga ita ta san harkar abinci da komai.

Tace to shikenan ba matsala InshaAllahu hakan za'ayi ba. Ta bashi abinci yaci daga nan ya bata duk tsarabarta da wasu daga cikin kayan yara da za'a ajiye a gurinta. Ummi se murna take har Adil ya gane. A ranshi yace ALLAH sarki, yaita tausaya mata sannan ya dinga shi min albarka yana cewa Amna ta gyara abin da ALLAH zeji dadinsa, nima kuma naji dadi kuma mumma ma zata ji dadi. ALLAH yayi mata albarka.

Washegari ya sa aka kawo ta gidana ta zo muyi shawara da lissafi. Muka gaisa ta rike baby daya nima na rike daya sannan tace,
"Dama Baban Ra'is ne yace nazo muyi shawara akan yadda za'a gudanar da zancen walima, tunda ke kinsan yadda harkar mutane da abinci take".
Nace "hakane, to yanzu ke me da me kike so ayi kuma ya kike so gurin ya zama kuma mutane nawa kike so a gayyata?".
Tace "to ban taba hada taro ba, abin ze danmin wahala gaskia. Shiyasa ma nake so ki tayani".
Nace "to ummi daga yau zaki fara kuma in yayi kyau zan daukeki ki dinga tayamu hada na wurina wadanda ake bamu kwangilar hadawa saboda haka challenge ne se kiyi shi me kyau saboda mutane in sun yaba zan ce aikinki ne".
"Kuma amfani zakiyi da tunaninki da abubuwan da kike sha'awa da yadda in kinje wasu bukukuwan kike ganin abinda yake birgeki seki fito da wani abu me kyau out of all that".
Tace "to".
Haka ta dinga kawo shawarwari ina guiding dinta, ina nuna mata wanda suka yi da wanda ba suyi ba. Mun dade a tare ranar har muka gama komai lafiya cikin kwanciyar hankali. A raina ina ta tausayinta tare da jin haushin iyayen da suke hada auren dole ba tare da son 'ya'yan nasu ba.

Ana saura kwana biyu walima baby boy din ya rasu. An mishi huduba da suna Muhammad Ahmad. Allah ya dauke abinshi. Munsha kuka tare da yi masa addu'a. Kullum in zan sama Aysha kaya sena tunashi nayi kuka.

Ba'a fasa walima ba se kawai aka fasa saka kida da gwagwgwaron da muka ce zamuyi. Muka yi kamar wuni muka tashi. Kowa dai yaci ya sha an gode ALLAH.

Adil yaji ciwon rashin danshi amma se na dinga tausar sa ina ce masa ya gode ALLAH tunda be san nufinsa nayin hakan ba. Wani lokacin ALLAH yana jarrabar bawa a cikin rayuwarsa yaga ya zeyi. Saboda haka dole mu dinga rungumar kaddara me kyau da marar kyau. Haka ya hakura muka shiga hidimomin mu ba dan mun manta ba se dan hakuri da tawakkali.

Adil dakyar ya bari na gama wankan jego a hakanma se ya tattabeni ya tsotstsotseni in muna tare.

Da na ce masa ya koma gidan ummi gaba daya har se nayi arba'in din amma yaki. Naga in yazo ba abinda yake samu se dan kadan amma hakan yake so.

In nace nonon baby Aysha ne se yace namu dai nida ita. Kuma ni sam mata ma nayi na dan lokaci. Tayi tayi ma ta bar min abuna. Yace tana shekara daya za'a yayeta ta bar min abuna.
ALLAH sarki Adil ko kyankyami na ma bayaji. Irin wannan halayyar tasa tana kara min sonshi a raina.

Ranar da nayi arba'in yazo ze afka min. Nace masa "in kana yiwa ALLAH ka bari na dan kai ko da nan da kwana biyu ne dan ban gama warkewa ba".

Dakyar ya kyaleni wai wallahi ya wahala da yawa. Ni kuma saboda kar naje na kara samun ciki ne ban shirya ba. Dan ni a rayuwata yara 4 ko uku sun isheni dama. Yanzu kuma alhamdulillah ina da 3 ga na Adil biyu da tare nake kula dasu da yarana 5 kenan ai kuwa haka sun isa.

A washegari naje na fara family planning ban fada masa ba. Kawai dai daya zo ina kwance ya fara shafa ni yana neman harkarsa ban hanashi ba.
Ranar nasha sa albarka kuma ni kaina nasan ya ji dadi dan nasha sumbatu.
Kuma nima naji jiki wajen shan magani dan ban saba sha ba a gida Nasar amma yanzu dole nake sha saboda Adil.
Da se inta cewa magungunan nan basayi, amma a yanzu na gane sunayi. Yawanci in mata sun hadu da mazan da bazasu nuna kyan maganin ne ba se su kasa gane ko yana da kyau ko bashi dashi.

❤MAHBUBI❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora