Babi na 14

2.1K 60 0
                                    

Amna dan ALLAH kiyi hakuri. A raina nace lallai Nasar yana da son kansa. Wato dai so yake ya maidani jaka ko shashasha.
Kawai nace masa idan kana son ganin yara kasan hanyar gidan nan, na shige gida na barshi anan.
Bansan sanda ya gaji ya tafi ba.

Ranar na dawo dakin mami na karkade ko ina na sa kayana na zauna.

Ba na ma san komawa ko kwaso kayana daga gidan Nasar shiyasa duk na bada na bayarwa.

Ina zaune da yamma naji Jamila ta dawo, naita murna daga daki kamar an sani a aljanna. Ta shigo muka gaisa sannan ta ce inda abinda zata min nace mata ba komai sedai ko zuwa anjima. Ta tafi wurin su Saratu suke hira.

A daren ranar nayi sallar dare sosai, na tsaya na kira sunan ALLAH nayi Masa kirari na gode masa da sunayen Sa guda 99. Nayi sujjada kamar bazan dago ba ina godiya ga ALLAH na. Saboda yadda abin ya faru har kowa yabi bayana nasan ALLAH NE YA tsaya min.

Washegari da wuri su yaya suka shirya zasu wuce, mukayi sallama da su muna daga musu hannu har suka fita daga gate. Dan uwa me dadi se mukai tajin dama su zauna kada su tafi.

A ranar na fara tsara wani babban buri na. Dan yanzu ba aurene a gaba na ba kuma. Ba na ma tunanin sa kwata kwata. Na dakko littafi na fara zane na da lissafi na.

Dan fili nake nema a inda bazeyi wuyar shiga ba ga kowa. Unguwa me saukin zuwa. Inaso na cika burina. Burin nawa kuwa be wuce san bude wata 'yar kungiya ta taimakon mata masu irin matsala ta ko makamanciyar ta. Matan da akewa wulakanci, ko wadanda ake tozartawa, ko wadanda ake dannewa hakki da sauransu. Kuma inaso a hankali ta habaka mu fara maida su(wadanda suke da sha'awar komawa karatu amma basu da yadda zasuyi kuma miji ya hana saboda mugunta) makaranta. Mu kuma fara ilimantar da matan hausawa akan mu'amala da mutane da fitowa ko ina su fadi abinda yake ransu.

Washegari container ta tazo. Na dinga tsalle ina murna. Nace komai yazo min yadda ya kamata. Alhamdulillah!
Kamar yadda aka ajiye ta restaurant dita a gida haka wannan ma muka ajiye ta a sultan road.

Washegari nasa aka samo min mutane wadanda zasu tayani gyara gidana. Haka muka fara kamar yadda mukayi wancan. Zamu fito da komai mu ware, sannan mu dinga dauka daya bayan daya muna kaiwa ana jerawa.

A guest room dinmu na saka wani coffee gado wanda be cika ado ba da brown curtains da brown carpet na saka.

A guest room dinmu na saka wani coffee gado wanda be cika ado ba da brown curtains da brown carpet na saka

Oops! Ang larawang ito ay hindi sumusunod sa aming mga alituntunin sa nilalaman. Upang magpatuloy sa pag-publish, subukan itong alisin o mag-upload ng bago.

Sannan parlour na, na 'kasa na masa brown, coffee and green.

Sannan parlour na, na 'kasa na masa brown, coffee and green

Oops! Ang larawang ito ay hindi sumusunod sa aming mga alituntunin sa nilalaman. Upang magpatuloy sa pag-publish, subukan itong alisin o mag-upload ng bago.
❤MAHBUBI❤Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon