Haka na kwana ranar inata tunani me zurfi gashi likita yace in rage yawan tunani. A raina ina cewa da wani ne ba Adil ba da bani da matsala, da tuni na watsar da rayuwarsa na ci gaba da rayuwata. Gaskia so irin wannan akwai hadari. Sunayen ALLAH nake ta kira ina kara yin innanillahi...
Dana danji saukin ciwon kan se na tashi na dauro alwala cikin dare naita sallar da bansan iya raka'o'in da nayi ba ma. Na idar na koma kan gado ina addu'a ina tunani har zuwa asuba...Washegari yayana kafin ya tafi aikinsa seda ya biyo ya ganni sannan ya ce min da yamma in ya taso ze biyo ya kara dubani nace toh yaya.
Yace amma dan ALLAH Amna ki rage tunani.
Nace toh yaya inshaAllahu...Na rasa me zanyi a ranar gashi ni kadai ce ba me tayani hira, Manal ta tafi CYK, Aysha ce take ta wasan ta a gefe kuma Jamila ta shigo ta dauketa wai za'a bata abinci.
Naita tunani a raina ni kadai na ce wai ga arzikin ga mahallin ga 'ya'yan ALLAH SWT be hanani komai ba acikin wa'an nan abubuwan amma Adil kawai saboda tsabar son da nake masa ya sani na shiga tashin hankali da tsananin tunani da rashin jin dadin rayuwata kwata kwata.
Adil is part of me.
He lives in me.
He makes my world a happy and lively one.
Nafiso kullum yana kusa dani.
No one understands me like he does.
Irin wadan nan tunanikan nake yawan yi har suke sani kuka.Da yamma kowa ya dawo, gidan ya danyi min dadin zama. Mutum rahama. In kana bacin rai mutane na kusa da kai suna hidima yana raguwa. Na shiga cikin yara da Aunty Minal munata hira muna wasa har ina dariya. Nace gaskia zaman kadaici ba dadi yana sa ka tunani har marar kyau.
Manal tayi ta neman wayata bata sameni ba se ta kira Minal. Na dauka mukai ta shan hirar mu. Aida har an kusa gama karatu saura kadan. Har Manal nace min a barta ta dora da masters kawai in ta gama tunda ba wata babba bace kuma ga oportunity. Nace mata ta bari muyi shawara dasu yaya tukunna.
Bayan maghrib muna zaune yara na cin abinci yayana ya shigo. Yazo ya daddaga su suna murna suna ihu sun ganshi. Haka sukai ta wasa tare. Da suka gama Minal ta tafi sa su bacci.
Yaya ya matso kusa dani ya rike hannuna yace》 Amna.
Nace 》na'am yaya.Yace 》Amna me ke damunki?
Na fara hawaye me tsanani ina ta kukan na kasa magana.
Seda nayi me isa ta sannan cikin shashshekaNace 》yaya Adil ne. Bansan me nayi masa ba. Tunda akayi kwana 3 da mutuwar mamanshi ya canza min yaya, bansan me nayi masa ba. Kuma yaya nayi masa kiran duniya baya daga wayata kuma be kara zuwa gidana ba. Ta ya zanyi nasan me nayi masa yaya?
Yaya yace 》auzubillahi... amma Amna kikayi shiru baki fadawa kowa ba? In an tambayeki shi se kice yana nan ko ze zo ko yanzu ya tafi.
Nace 》yaya toh me zance? Me zance yaya? Inna fara kawo matsala za'a ce nice nake creating matsalolin.
Yaya yace》waye ze ce Amna? Ina ruwanki da masu cewa din kuma? Kinfi kowa sanin mutane basu da gadon ka amma suna da gadon maganarka. Kuma mu 'yan uwanki in kin fada mana wa zamu fadawa da har za'a sani?
Nace 》yaya kayi hakuri, banyi zurfin tunani ba kuma bana son damunku da yawan matsaloli na ina tayar muku da hankali.
Yace 》haba Amna haba, ya zaki ce haka? Meye amfanin mu? Kuma an taba rayuwa ba matsala?
Nace 》yaya naga kowa a cikin ku yana rayuwarshi ba matsala, ba me fadar tashi a cikinku 'yan uwana. Kullum in za'aji matsala to tawa ce.
Yaya yace 》Amna ba rayuwa da ake yinta ba matsala, kawai dai ta wani bata kai ta wani ba ta wani kuma tafi ta wani. In abu yana faruwa dake ki dena tunanin abinda wasu zasu ce ki nemi shawara kawai.
Nace 》toh yaya. Kukana ya karu. Ina jin dadin yadda yake tausayi na yana kaunata.
Yaya yace》toh yanzu me kike ganin ya dace? Shawara taki ce Amna. Saboda ni a gani na gaskia ba'a hankalinsa ya ke aikata hakan ba domin idan halinsa ne wulaqanci ze dinga miki a cikin gidanki ko ma inkin kira ya dauka ya miki. Kuma ba haka kurin ze ki daga wayarki ba, duk halin mutum in ka kira sau uku zuwa hudu ai zeyi hakuri ya daga koda zaginka ne yayi yace ka kyaleshi. Amma bance rashin daukar wayar ba laifi bane. Shima ba dadi amma gaskia this is unlike Adil.
YOU ARE READING
❤MAHBUBI❤
RomanceLabari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...