Babi na 29

1.6K 63 0
                                    

Haka rayuwa tai matukar canzawa Ummi kullum cikin dana sani.

Dama haka kawaye suke, su kaika su baro ka, kuma ba lallai su sunayin abinda zasu saka kayi ba, inma suna yi to su sun kware se ka zuba musu ido domin in wani yayi rawa a kasuwa...

Mun koma gida nida yara. Su kai ta yin murna suda su Hamid. Dama tun a hanya na tsaya na saya musu ice cream sukayi shiru.
Kowa se tsalle yake dama sun dade basu hadu ba.
Dakunansu dama suna nan yadda suke kawai dai kokari nayi a cikin sati daya nida Minal da Jamila da Ai muka fito da kayansu duka. Muka ware wanda suka musu kadan. Na bama su jamila wasu daga ciki sauran muka kai orphanage home.

Rayuwa ta canza mana duka. Adil ya koma aikinsa nima na koma nawa. Munyi kuma shawara akan yasa a dakko wani daga cikin 'yan uwan Babanshi me amana me kuma kirki acikinsu yazo ya zauna a cikin gidan saboda kar abar Alhajin shi kadai, kadaici yazo ya masa yawa gashi dama ba cikakkiyar lafiya ba. Haka kuwa akayi...

Yusra na bama order kayan yara. Da cikinta tulele ta zo ta kawo a mota nasa aka shigo da kayan. Kowa nashi a ledoji daban se kawai nasa Minal ta je ta jera ma kowa nashi a wurin kayansa.
Muka zauna muke shan hirar da muka dade bamuyi ba nida kawata 'yar uwata. Har take bani labarin anzo Tambayar Minal da Aida. Naita mamaki da jin haushi a lokaci daya. Har na kira Minal na kwakwkwaďeta.

Nace 》ina gidan tare dake baki fada min za azo tambayar ba se a bakin Yusra.
Yusra tace 》gani ni kuma bare ko?
Tace 》aiku bakwa 'yanta mutum. Duk daďewarsa acikinku se kun nuna masa wariyar launin fata.
Naita dariya nace 》ba haka bane. Aike yayar mu ce.

Minal taita bani hakuri tace 》 kuma yaya Amna Bilal din da kika sani ne fa. Shi kadai nake magana dashi. Takurawa yayi shine dana fadawa su  yaya sukace ya tura. Kuma dama gidansu a Abuja yake. Shine aka tura wurin su Yaya aka kai kudi akan za'a koma sa rana. Kuma lokacin yaya Adil bashi da lafiya shiyasa ba'a fada miki ba.
Nace 》to amma dana dawo ai se a fada min.
Tace 》ai baki nutsu ba yaya Amna kiyi hakuri.
Nace 》naji amma zan kira su yayan nayi mita.
Mukai ta dariya.

Bayan yusra ta tafi na kira su yaya dukansu daya bayan daya nayi mita ta duk suka bani hakuri sannan na tambayi waye na Aida tunda nasan na  Minal.
Yaya yace 》 na Aida dan uwan Mukhtar ne shima a can Canada suke tare yake sonta.
Nai mata murna sosai.
Da na kira Manal seda na mata ta tas akan sun boye min zancen. Taita bani hakuri har seda Mukhtar yasa baki sannan na hakura.

Na sa an maida su Ra'is makarantar su Hamid Cresent. Saboda sun dawo gurina da zama. Islamiyyar ma duka an maida su, tare ake kaisu a dakko su. In juma'a tayi za'a kai su Hamid da Habibti gidan kakanninsu(dan ban yadda akai su gidan baban ba, sedai yaje wurin Hajiarsa ya gansu) suma su Ra'is nasa Adil ya yadda adinga kaisu gidan su Ummi in yaso se suma a sama musu tahfiz acan wadda zasu dinga yi.
In zasu tafi haka nake hada kayayyakinsu na ci da sha su tafi dasu yadda ba zasu dorawa Ummi nauyi ba.
Ummi da kanta ta kira wayata ta nemi gafarata wai mahaifiyarta ce ta sa tayi hakan saboda yadda suka ga ana kula musu da yaran.
Nace 》ba komai ai da na kowa ne kuma da dukiya da da ba:a wulakantasu.

Rayuwa taci gaba nida Adil kullum kara kaunar juna muke. Ya zama mun samu fahimtar juna fiye da tunani. Komai yake so na sani nima komai nakeso ya sani. Muna gudun bacin ran juna sosai. Komai ya fado hanyar mu se munyi nazari akanshi sosai kafin mu yanke hukunci. Kullum se Adil ya shi min albarka."

In nayi kwalliya Adil ze ce kinyi kyau Amnata, kamar na daukeki na gudu.
In shima  yayi zan ce kayi kyau Adili na kamar na boyeka mata su dena kallar min kai.
Se yace ai sedai su kalli gangar jiki dan kuwa zuciya kin gama mallaketa.
Se in kyalkyale da dariya.
Fadan mu baya wuce yace na fiya tairin kai, in na so abu ba a isa a tankwara ni ba.
Shikuma ince kafiya da dagiya. Shi lallai komai nasa daidai ne, baya laifi.
Rayuwar soyayya akwai dadi.

❤MAHBUBI❤Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon