Babi na 6

2K 71 0
                                    


Nasar kuma tausaya min kawai yake yana lalla'bani.

Baba yafi kowa sukurkucewa be iya komai ba se Mami tayi mishi. Kullum se yayi kuka yayi mata addua.

Ranar naje wurinsa muna hira yake bani labarin ciwon.
Yadda ciwon nata ya kasance, yadda taji jiki. Yace ai Amna Maryam tanada dauriya. Seda aka mata MRI (Magnetic Resonance Imaging) Scan akaga tama fini cuta amma duk da haka bata gajia ba itace me jinyata.

Sanda na kira su Ahmadu jikin nata ne yai tsanani ni a lokacin ma na warware. Yana kuka yace taji jiki Maryam. Ulcer nan muguwar ciwo ce duk ta fatattaka mata hanjin ta ashe shiyasa take yawan ciwon kai.

Muka sha wani kukan muka more. Sannan nace amma Baba sanda tace min jikinka ne ya tsananta ashe nata ne kenan? Se yace eh Amna cewa tayi bataso ki rikita da yawa dan tasan baki san bata da lafiya ba ni kika sa a rai bani da lafiya. In kika ji jikinta ne ya rikice zaki gane akwai wani abun ki rikice kema gaki da ciki kuma bataso ki sami matsala. Shiyasa duk sanda kika kira take kokarin dauka ta miki magana amma dagewa takeyi. Tana sonki da yawa Amna kar ki manta yi mata addua kuma ki kula mata da 'kannenki. Nace to Baba dukan mu muna kuka.

Ya Mahmud yana dakuwa har yanzu dan Yusra tace har yau be 'kara cin abinci ba seta masa d'ura hakama d'urar magani, dan ya kwanta mata sharkaf ga shi ana neman wata biyu.

Tace ko Wurin ayyukan Baba dashi yake kula dasu ma ya dena zuwa ga kuka cikin dare. Tace Amna wanka ma nike masa. Gaskia hubby na ya sha'ku da Mami sosai. Nace mata sosai ma kuwa fiye da yadda kike zato ma Yusra. Harma suka birgeni nayi murmushi na farko a wata biyu. A raina inata musu addu'ar Allah ya bar musu soyayyarsu.

Seda Mami ta shekara lokacin yarinyar dana haifa ta kusa wata goma sha daya sannan ne abin ya d'an ragu a ranmu muka d'an fara walwala amma duk da haka muna shiga d'akinta muke fara sabon kuka.

Sunan Mami aka mayarwa Habibti dan haka nake kiranta ni, su kuma daga me ce mata Saheeba se me ce mata Ummita, wasu kuma Mami ma suke ce mata. Kowa fatan tayo halin Mami yake mata. Baba da dukanmu muna ji da ita fiye da sauran 'ya'ya da jikoki.

Lokaci ya ja sosai yanzu habibti shekararta biyu tana ta guje gujenta ko ina shi kuma Hamid yana upper KG a crescent ya kusa 4yrs, be kai 3 ba na sakashi a lower KG. Kusan ko da yaushe ina hanyar zuwa gida ganin su Minal da Aidan Mami wadda nake matukar tausayawa saboda sha'kuwar da tayi da Maminta, ita Manal ta girma dan level 3 zata shiga yanzu hutun second semester sukeyi. Dad'inta dai Yusra ta zama uwar marayu dan duk safiya seta je ta gansu sannan Baba ya mayar da komai na harkarsu wurin yayana.

Rayuwar yayana da Yusra na matukar bani sha'awa dan basu sa komai a gaba ba se 'kaunar junansu. Suna son junansu sosai. Yusra bata iya cin komai bata rage masa ba. Ko biki mukaje tare seta d'ibarma yayana dukkan abinda taci inma kadanne ta gwammace ta hakura ta kai masa. Har inta tsokanarta ina cewa se an gane ki ance kin fiya d'ibar abinci kamar baku dashi a gida se tace oho dai kema ki d'ibarwa mijinki mana. Kuma kullum ka shiga gidansu suna manne da juna in ma bakai saa ba a gabanka zeyi kissing dinta. Cikin dake jikinta kuwa a gabanka ze d'aga yana kissing abunsa tana masa shagwa'ba.

Suna birgeni sosai inta cewa dama nice.

In ta raya musu kina nan zasu haye sama d'aki su barki anan 'kasa kita jira sedai kiga sunyo wanka sun chanza kaya sun sauko. Allah ya bar kauna don suna matu'kar birgeni.

Yau ma ina gidan yayana zesha magani yace love da 'karfi dan tana kitchen ta amsa na'am hubby dan in kana tare dasu kaji sunayen 'kauna kala kala suna kiran junansu. Yace zoki bani magani tace to dear amma bari nayi muci abinci se na baka kasha ko se yace eh.
To zo na d'an yi kissing sweet lips din nan ta kuwa turo baki yace aaa gaskia ba haka ba me dad'i nake son yi se ta karkata ta gyara sannan ya tsotse abinsa ni kuma ina d'auke kai su kuwa ko a jikinsu.

❤MAHBUBI❤Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin