Babi na 26

1.4K 63 0
                                    

Alhamdulillah na fara cewa da karfi na ketare mutane na je gurin Adil nace na'am Adil.

Yace Amna me ke faruwa?

Kawai na fashe da kuka saboda shima idanunsa duk sun cicciko da kwalla yana tambayata cikin tausayawa kansa dani din.

Yace Amna inane nan?
Wane irin kazantace haka a jikina?
Me mukeyi anan?
Me ya sameni Amna?

Duk ban ansa ba na kamo hannunsa ya taso muje daki. Yana tashi ya yi baya ze fadi gashi nima ba kuzarin iya rikeshi duk da dama Adil ba wani kiba ne dashi ba.

Mal Junaidu yace ku tsaya a rike miki shi a kai shi daki tukunna.
Aka kai min shi cikin bukkar mu sannan na karasa kusa dashi na rike hannunsa idanuwa na da nashi fal da hawaye se gangara sukeyi.

Ya rike hannuna kam kam ya kara cewa Amna ina ne nan?
Wai me ya kawo mu nan ne?

A sannan ne na fara masa magana.
Nace 》Adil wurin maganine Alhaji ya sa aka kawo mu nida kai saboda baka da lafiya kuma anan ne da maganin irin cutar. Amma kamin afuwa kar ka sake magana saboda yanzu ba wannan ne ya kamace ka ba. Kayi shiru ka huta, mu kuma jira abinda malam ze fada.

Kamar karamin yaro yace 》toh Amna.

Na dau waya na kira yaya na fada masa yace gasu nan dawowa shida su yaya Muhammad. Sannan nace ya kira Alhajin su Adil ya sanar dashi. Yace toh.

Na fita na samo yaro nace a samo masa madara peak ta ruwa ya sha ko ya dan sami kwarin jiki. Dakyar aka samo seda aka sha wahala sannan aka samo mana. Na fasa masa na bashi yasha gwangwani biyu se kuma bacci. Yaita bacci har su yaya suka zo. Baban shi ma yazo.

Da nace bacci yake mal Junaidu yace kada a tasheshi a barshi ya huta saboda a duk kwanaki ashirin din nan ba baccin kirki yake ba. Da ya fara cikin dare yake farkawa ya kuma kasa komawa.

Anan yayi mana bayanin duk yadda akayi har aka samu wannan bebe me taurin kan jaraba ya fita. Ya kuma ce yanzu ba sauran su a jikinsa amma a dage masa da yin magani. Shi kuma na sihirin yace a hada da ayatul shifa da ganyen magarya.

Na ce 》malam yau zamu tafi?
Kowa ya kyalkyale da dariya a wurin wai na basu dariya.

Yace 》 da dai zaku kara kwana 7. Na zare ido sosai. Kafin nayi magana

Alhajin Adil yace 》a'a kar kasa min 'ya cikin damuwa, yaushe zaka sallamesu?

Se yace 》yau zasu iya tafiya. Zan dai kara musu magunguna da zasu ci gaba da amfani kuma dan ALLAH kar ayi wasa dasu.

Kafin kowa yayi magana nace 》inshaAllahu zamu kula.

Nan ma kowa dariya na bashi.
Ni kuwa naji jiki. Kawai gida nake son zuwa ko na samu bacci na nutsuwa. Tunda nazo gurin nan banyi baccin kirki ba se gyangyadi.
Ko na ga yarana.
Ko na kara shan iska me dadi.
Ko na yi wanka naji dadi.
Ko na ci abinci me kyau.
Gaskia bahaushe yayi gaskia da yace kowa ya bar gida...

Komai da muke amfani cewa nai a barwa Malam Junaidu saboda bama na son amfani dasu ko kara ganinsu ma a rayuwata.
Kayan jikinmu kawai muka tafi dasu. Adil yana bacci aka sashi a mota muka yi sallama da malam muka tafi.

Alhamdulillah ya ALLAH! Nake ta fada a raina. Iskar da naji ta gari da jama'a da nake gani se naji kamar daga kurkuku na fito. ALLAH ya mana rahama.

Alhaji ya juyo yace min 》Amna ina ne gidan naki mu saukeku se mu tafi?

Na nuna hanya har gidan, a raina ina ta cewa na zata ma gidansu za'a kaishi.

Se Alhaji ya katse min tunani yace yana bukatar kulawa sosai kuma ke kadai zaki iya kulawa dashi sosai. Inya warware ya murmure yazo gida.
Nace to.

Suka saukemu suka juya Alhaji yana ta shi min albarka.

Yara na islamiyya. Aysha na bacci. Minal kuma ana restaurant. Haka muka kai Adil daki kan gado aka kwantar dashi duk jikinsa ba kwari. Su Jamila suna ta min sannu da zuwa.
Muka gaisa na musu godiya sosai da kula min da yaran da sukayi, naji dadi sosai.

Jamila tace bazan bari Aysha ta tashi ba har se kin kintsa kin nutsu. Nace yauwa jamila ALLAH ya baki miji na gari. Ta wangale baki tana dariya na haye sama na barta, ban ma ji ko ta ansa ba.

Har naje sama na dawo nace ta yiwa Audu waya yazo ya kaita zasuyo min cefane.
Tace ai ba abinda bamu dashi maama. Baban Al ameen ya yo siyayya da yawa shekaran jiya ya sa an kawo. Harda kayan makarantar yara da su pampers din Aysha. Tace muma ya raba mana dubu biyar biyar.

Dan uwa me dadi. Naji dadi sosai a raina. Nace ALLAH Ya biya yayana.

Ina murushi na haye sama. Ina zuwa na shige wanka. Na kunna ruwa, ba na zafi, amma ALLAH Yasa akwai wuta, se na kunna heater na koma ban dakin na fara shaving. Duka gashin hammata ta dana gabana seda nai shaving. Na dakko scrubs dina kala kala na dinga scrubbing jikina. Inna gama gurza wannan sena gurza wannan. Duk da haka naji kamar ban fita ba. Seda na sa Jamila ta tafaso min ganyen magarya da lalle ta kawo min na karba, na zo na zuba miski a ciki na dinga kwarawa jikina ina gurjewa. Na kunna ruwan zafi heater ta tafasa nayi wanka sosai. Jikina ya fara santsi da kamshi na kara cewa Alhamdulillah!
Nayi brush yafi sau goma.

Aka kawo min garwashi na turara jikina sannan naji wani fresh air na shiga ta. Gashina ne kawai ya rage, shima ina yin sallah zan tafi salon a wanke min shi.

Har yanzu Adil be tashi ba, na sauka nai sauri naje salon aka wanke min gashin. Wash and set kawai nayi saboda magrib ta kusa kuma ina so naje nayi girki.

Ina dawowa Minal ta dawo da yara daga makaranta. Suka taho da gudu suka rungumeni. Minal taita mamaki ya akai na dawo bayan dazu suka barni. Nace mata ya samu sauki an sallamemu.

Duk inda na sa kafa Habibiti da Hamid bina suke. Aysha ta tashi ta dinga tsalle wai taga mamanta kuma taki zuwa gurin kowa, se goyata nayi a bayana muka fara girki. Tare mukayi girki dukanmu a kitchen.

Na mana gashin kaza da fried rice da salad. Adil kuma na mishi soup me dadin gaske ta vegetables amma saboda bansan ko bakinsa ba appetite ba sena markade veges din nayi soup din dasu. Na masa fruit salad na kuma dama mishi kunun madara me cinnamon da corn flour da inibi aciki. Saboda yaji dadin bakinshi.

Na hau sama wurin isha'i be tashi ba se na tsorata sosai na hau saman gado na dago kanshi nace Adili! Adil! Baban Ra'is! Na jijjigashi sosai na kara cewa Adilin Amna! Sannan yace na'am yana mika.

Nace gaskia tsami kake muje ayi wanka se muyi sallar isha'i.

Ya bini kamar rakumi da akala.
Na cire kayan jikina na sa dan bum short da bra kawai.

Muka shiga na cika bath din da ruwa ya shiga ciki naita scrubbing jikin nan da sabulu da soso, in na gama na bude ruwan ya tafi na kara wani a haka har muka gama.
Shima seda na masa shaving duk wani gashi wanda yake na kazanta. Adil yayi tas, farin nashi ya fara dawowa. Ya fara jin garau.

Yace 》Amna?
Nace 》 na'am.
Yace min 》 sannu Amna.
Nace 》yauwa Adil.

Na gama mishi tsaf, sannan na bashi sabon brush, dama ina ajiye brushes sababbi a toilet. Ya wanke bakinsa tas sannan ya fito ya daura towel.

Mukaje daki muka tsane jikinshi, na dakko masa jallabiya da singlet da boxer, bayan na  shafa mishi mai ya saka su. Dama munyo alwala. Na cire kayana da suka jike na sa kaya sosai da zanyi sallah dasu. Adil ya jamu sallar isha'i sannan yaita ramuwar salloli. Har wurin 10pm yana salloli. Seda nace ka bari kaci abinci se ka kara yin wasu, kuma gobe ma rana ce ai. Da na fita zanje na debo masa abinci na tarar Aunty Minal tasa yara sunyi bacci.

Na kawo masa abincin daki. Duk yadda bana so a ci min abinci a daki yau ban damu ba saboda Adil ne, yasha soup din nan da kunun nan sosai. Fruit slad yace se anjim in ya idar da sallah.

Bayan ya idar da wasu sallolin wurin 12am ya kashe fitila ya hawo kan gado ya sameni na fara bacci. Be tasheni ba, ya kwanta a  bayana, ya shiga cikin bargon ya kuma sa hannunsa ya rikoni. Harda wata ajiyar zuciya yayi, sannan can shima bacci yai awon gaba dashi.

Da asuba mun tashi munyi sallah yace cikinsa ya rarake, haka na sauka kasa na hado masa sandwich da tea. Seda ya ci yasha sosai sannan ya koma gado ya kwanta.

Ni kuma na fita zan tashi yara in shiryasu su tafi makaranta. Minal dasu Jamila har sun tashi kuma a raina ina ta tunanin ya za'ayi in Adil ya tafi can gurin matarsa?

Kici gaba da binmu....
Umm khalil❤

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now