Ina mata dariya ta kwada min duka, wai banza meye na dariyar? Nace ba dole nayi dariya ba.
Yusra ce fa!
Dan Allah ba dole nayi dariya ba masoyan asali a helping hands, kuma wai itace ta ki cike file. Nace mata meyasa kika ki cike file, wai bataso yayana ya sani. Yanzun ma dan baya nan ne tazo kawo min tata matsalar yadda kafin ya dawo an samar mata mafita.
Na dinga dariya saboda har ga ALLAH abin dariya yake bani. Kuma ban taba zaton irinsu suna da matsala ko kwayar zarra ba. A matsayin komansu daidai yake tafiya ni nake ganinsu.Nace da ita me ya faru? Inayi ina dariya. Se dakyar na nutsu sannan nace ina saurarenki.
Tace: Amna ni bani da matsala da yayanki dan ba abinda baya min na hakkina kuma duk abinda na nema ina samu agurinshi ba keta ba mugunta. Amma Amna ni takaici na daya yayanki son mata ne dashi yai ta kashe murya yana magana dasu har a cikin gida, ina yawan jinshi kuma in nayi magana se muyi fada, gashi se inga ba abinda bana masa wanda yake so, gashi kuma yai ta min kulle baya barina naje ko ina.
Tunda nake restaurant dinki da kika bar min kula dashi ne kadai ya taba barina nake zuwa. Kuma inada sha'awar dan yin business ko yin aiki a wata ma'aikatar shi kuma duk bayaso, sedai naita zaman gida ina kula da gida.
Dan Allah a sama min mafita ya barni nayi life dita freely nima na dan samu na dinga mu'amalolina yadda ya kamata. Nayi alkawarin tsare masa mutuncinsa da nawa mutuncin.
A yau zamu fara tattaunawa da mata shiyasa na nutsu sosai na manta cewa ma na santa kawai nai focussing akan aikina tare da fatan amfani da dan ilimina da kuma experience. ALLAH Ya bamu sa'a.
Na nutsu na sa ido na akanta sosai.
Nace: da farko ya kamata na fara miki tambayoyi amma kuma alhamdulillah base nayi mikin ba tunda kin fadi dukkan alkhirinsa kafin sharrinsa. Saboda haka ki saurare ni.
Nace: "yusra na farko son matansa da kulasu da kashe musu murya ba abin damuwa bane. Of course ze dameki kuma dole zakiji haushi a cikin ranki saboda son da kike masa, amma life can never be perfect Yusra".
"Kuma as far as ba kulasu yake ta fannin zina dasu ba ki daga hannu ki gode ALLAH".
"Da zakiji matsalar wasu da kinsan a rahama kike a hakan ma".
"Dole ne mu fuskanci wasu matsalolin saboda ALLAH ya yafe mana wasu kurakuren da muke tafkawa kuma matsawar ka daukesu a kaddara kuma ka karbesu hannu bibbiyu zakaga alherinsu a sannu domin ubangiji ba ya dorawa bawansa abinda baze iya ba ko kuma abinda ba alkhairi bane a rayuwarsa".
"Namiji baa taba rabashi da son mata. Indai ya gani ze kula ko yayi sha'awa, amma that does not mean baya sonki, ko yana yi ne dan ya bata miki rai. Duk da nasan akwai masuyi dan su cusgunawa matan nasu".
"Kisa dukkan wannan mu'amalar a gefe kisa a ranki in ya auro wata fa? Ya zakiyi? Kuma kinsan ALLAH ya halatta masa".
"Ki ta masa addua ALLAH Ya kareshi daga sharrin su matan masu sharri Ya kiyaye miki shi a duk inda yake".
"In kina soma kice ALLAH Ka mallaka min shi ni kadai. ALLAH maji roko ne ze iya ansa miki".Amma a rage yawan bacci a dinga yawan ibada ana kara kusanci da ALLAH. Sallar daren nan da azumin nan da karatun Qurani da yin Azkhar yana yaye damuwa.
Sannan akwai yayata watarana data taba bani wata shawara tace min ki ma mijinki addu'a yadda kike ma 'ya'yanki. In yana bacci ki masa ki tofa a hannunki ki shafe masa jikinsa, in kuna zaune ki dakko ruwa a gabansa ki tofa addu'a ta kariya da kara soyayya ki bashi ya sha.
In ze fita ki masa addu'a ki shafe masa jikinsa. Sannan ki masa addua kice "ALLAH Ka karemin wane Ka hana idonshi ganin kyan kowace mace duk kyanta, Ka hana zuciyar shi sha'awar kowace mace Sannan ka dawo min dashi gida lafiya".Se abu na biyu kulle.
Bashi da dadi gaskia takura mace kuma duniya taci gaba. Sannan ai yana da amfani barin mace ta fita ta shiga cikin duniya ta dinga mu'amala da mutane da yawa, ta nan zata sami mutane wadanda zasu amfaneta ta wurare da dama itama ta amfanesu. Ita zamantakewa ta mu'amala da mutane ake koyarta. In kana jin labarai kuma kana haduwa da mutane kuna tattaunawa dasu, kana jin nasu matsalolin se kiga kana karuwa da yawa ta hanyoyi da dama kuma kana sanin yadda zaka na tafiyar da lamarikanka. Saboda ko kogi ai be ki dadi ba. Kuma ilimi a kullum karuwa ake dashi.
YOU ARE READING
❤MAHBUBI❤
RomanceLabari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...