Babi na 24

1.4K 59 2
                                    

Muka dinga wa junan mu kallon kallo.
Amna kuma ummi yake ma magana kuma ya kirata da Amna?

Adil duk ya zuge ya rame ya yi kamar marar lafiya. ALLAH me iko.
Alhaji yace masa kai Adil wannan Ummi ce ga Amna nan ya nuna ni da hannunsa. Da ya kalleni se ya taso, ya zo kusa dani, ya kalleni yace Amna! Nace na'am Adil! Se Adil ya fadi a gurin.

Dukanmu muka rude muka rasa yadda zamuyi. Ni na je na kamashi inata jijjigawa ina cewa Adil tashi... ina ihu ina salati ina kuka a lokaci daya.

Shi kuma Babanshi duk ya rikirkice a gurin banda innanillahi... ba abinda yake yi.

Yaya ne yayi karfin halin fita nemo taxi din da za'a daukeshi.
Se da ya samo sannan masu gadi suka ce bayan ga motoci, tunda shima kansa a mota yazo ya ze kira ta haya, sannan ne yaya ya fara dawowa tunaninsa na sosai.

Hankalinsa da kwata kwata ya gushe. Mamaki kawai ya ke na irin wannan yanayi. Aka bawa me taxi hakuri ya tafi.

Ummi ba wanda ta yiwa magana, kawai tashi tayi ko a jikinta ma ta wuce cikin gida abinta.

A motar yayana aka dauki Adil, ina zaune a baya tare dashi, babanshi ya shiga gaba, yaya yana jan motar muka nufi asibiti.

A asibiti muka samu likita aka ce emergency case ne, nan da nan aka sami daki aka sashi aka fara dubashi.
Likita duk gwaje gwajen da yayi bega komai ba. Bamu yadda ba, muka sa ya sake dubawa nan ma yace shi be ga ko wace matsala ba.

Muka daukeshi a fusache muka nufi wani asibitin. Nan ma hakane abinda ya faru. Duk gwajin duniya da ya kamata ayi anyi amma an ce ba abinda da yake damun Adil.

Kowa yayi jugum jugum. Ga Adil a kwance ga tunaninmu duka ya dauke, hankalinmu yayi wani wajen.

A raina cewa nake me kenan to?
Wannan wace irin masifa ce?
Ni ban taba ganin yanayi irin wannan ba tunda nake a rayuwata.

Yaya ma abinda yake ta sakawa a ransa kenan. Kowa acikinmu ya rasa me ke masa dadi.

Ga Adil ya farfado amma be san inda hankalinsa yake ba. Kallonmu kawai yakeyi sama sama kamar ma baya ganin mu sosai.

Banda kuka ba abinda nake, ina ta jijjigashi amma beya iya yi min magana. Ga idanunsa sunyi ja jazir kamar garwashi kanshi yayi zafi amma an kasa gane meye matsalarsa.

Ya salam!!! ALLAH ka kawo mana dauki ya ALLAH.

Ina cikin wannan addu'ar a raina naji Alhaji yace Mahmuda mu koma dashi gida semu nutsu mu san ta inda zamu bullowa abin.

Hakan kuwa akayi. Aka samo mutane suka taimaka wa yayana aka daukeshi aka sashi a mota.
Ba me cewa komai a mota, dukanmu munyi shiru munata jimami, ni har yanzu hawayena be dena zuba ba.

A gidan aka kwantar dashi a parlourn Alhaji. Muka kara zama dukanmu kowa na kallonsa.

Chan Alhaji ya dakko wayarsa yace bari ya kira limamin da yake jan sallah a nan masallacin kofar gidan ya nemi shawara, yace tunda ance ba na asibiti bane gara mu nemi shawara daga masu ilimin addini muji ya zamuyi.
Bayan sun gama magana ya masa bayani dalla dalla iya abinda ya sani se limamin mal Umar yace gashi nan zuwa.

Muna zaune zaman jiranshi ni dai ina ta kuka. Alhaji yace Amna kiyi hakuri kinji? Komai yai zafi maganinsa ALLAH kuma ita rayuwa ba'a yinta ba jarabawa acikinta. Dolene kiga ALLAH ya jarrabi bawanshi ta ko wace hanya idan yaso saboda ya gwada imaninsa. Mu dauki wannan a matsayin jarabawa dukanmu mu kuma rungumi kaddara da hannu biyu.

Yace kai kuma Mahmuda ka tashi ka tafi gida naga lokaci na ja kuma kar iyalinka su nemeka.
Yaya yace a'a Alhaji ai lokacin komawata daga aiki be ma yi ba. Zan dai kira wurin aikina na sanar dasu bazan sami damar zuwa ba yau. Amma ai bazan tafi na barka kai kadai ba Alhaji a cikin wannan yanayi. Abinda ya shafi Adil ai dukanmu ya shafa. Alhaji yaji dadi mutuka da zancen yaya.

❤MAHBUBI❤Where stories live. Discover now