***************
Cikin wata biyu an gama gini tsaf, anyi tiling ko ina, ansa fittings din, an gama komai.
An min swimming dina me murfi. Yana rufewa in ka danna wani button.
Gurin wasan yara komai yayi.
Yanzu furnishing gida ne ya rage kawai. Visar mu ma ta fito nida yara.Ranar wata juma'a muna zaune da Nasar nake ce masa
"Baban Hamid dan Allah inaso muyi magama ta sulhu".
Yace "Ina jinki". Amma fuskarshi a turbune, kuma da hira muke cikin kwanciyar hankali. Seda ma naga ransa a sake na fara maganar, amma se naga ya bata rai. Saboda shi ba abinda ya tsana irin kace zakuyi magana me mahimmanci bare in yasan inda kake zuwa.Na ce masa "So nake na tambayeka wasu tambayoyi da na saba yi maka a baya".
Yace "um hum".
Na fara da tambayarsa akwai wata matsala da nake da ita yake treating dina yanda yake min?
Na ce mishi ko na gaza ne ta wani bangaren?
Na sake ce masa ko so nane baka yi?Duka yace shi ba komai.
Se nace to kasan ina da hakki ko bani dashi?
Se ya fara fada. Aiku mata bakusan meya kamata ba, komai akayi muku bakwa ganin daidansa. Ya dinga masifa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
Kawai nace mishi "Allah ubangiji ya huci zuciyarka ya sanyaya maka ita". Sannan nace masa inshaAllah komai ya kusa karewa.Duk su yaya sunzo sun ga gida. Da naso na boye musu se rannan aka kai gulma wurin yayana wai an gina filina na Tukur road shine yaje gani, yai maza ya kirani. Se naita dariya na kuma wayance nace ai Yaya nice nake ginin kuma na boye muku ne saboda so nake nai surprising dinku.
Yaita min fada na bashi hakuri.Kowa yace gini yayi kyau, saura kayan gida, yayana harda dukana wai 'yar banza waya baki plan din nan me kyau haka? Mukai ta dariya.
Ranar naje gida na zaunar da Minal da Yusra na nuna musu komai a kan restaurant, duk yadda nake gudanar da aikin da yadda nake biyan ma'aikata da yadda muke komai da ribar mu da kuma yadda nake kula da customers din.
Sannan bani da matsala da ma'aikata na saboda duk sun iya girkunan da mukeyi a gurin.
Nace Yusra zata zama manager, Minal kuma asaistant dinta.
Duk cikin dabara da wayo.Yusra tace ke kina ina?
Nace mata so nake na huta. Laulayi na fara, kuma Nasar yace na huta kada na wahalar masa da baby, nace amma zan dinga zuwa supervision. Sukai ta tsalle suna murna wai zan kara haifo mana baby.Na fada ma yusra abinda zata dinga dauka daga cikin kudin a matsayin albashinta.
Minal kuma dama da albashinta tun tuni.
Nace sauran a dinga zuba min a account dina na restaurant din. Dan ban hada shi da na sauran savings dina ba.Da muka koma cikin gida na ce Minal ki dinga kula da Aida sosai, a rage fada. da kuke yawan yi. Ki zama babba. Tace min to Yaya Amna inshaAllahu. Na kara mata nasiha akan maida hankali da nutsuwa.
A gidana kuma na fara hada kayana a hankali. Tunda yanzu bana zuwa restaurant se supervision nake dan zuwa yi.
Nasar na fita nake dakko kayana na fara gyara su daya bayan daya. Na ware na bayarwa kaf, na bawa Jamila wasu sannan nakai wasu gidan marayu tare da dinbin kayan abinci da na siya na hada. Suma yara na ware kayansu tsaf. Duk wani abuna me amfani na kwashe shi daga gidan, na bar marassa amfanin.Ko sa insa dena yi nayi da Nasar. Zaman lafiya kawai kamar koda yaushe.
***************
Ranar wata juma'a na hada yara tsaf suka tafi makaranta. Na sa Jamila ta kai min wasu kaya mota, ta sa a baya. Na dakko kudi da yawa kimanin 200k na bata nace ta ciri kudin aikinta sauran ta nemi sana'a ta dinga yi ta juya kudin su zama wani abu.
Ta fara kuka tana tambayata ko wani abun ta min, nace wallahi ba komai Jamila tafiyace ta kamani a gaggauce kuma bansan ranar dawowa ta ba shiyasa.
Taita kuka wai bata son rabuwa dani. Na bata hakuri, na hada mata goma ta arziki sannan da zan tafi dakko yara muka rufe gida, ta debi kayanta itama, nasa me gadi ya kira mata taxi ta zuba kayanta a ciki ta tafi.
Munyi rabuwar rashin jin dadi dan ina son Jamila.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
❤MAHBUBI❤
RomantizmLabari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...