Hasana Umar,
Ita Hasana ba abinda ya banbanta matsalarta da tawa kawai ita tana da karancin shekaru ba tafi shekara ashirin da biyu ba amma itama yaranta biyu duka mata.
Da tana bayani kawai kallonta nake ina tuna Nasar.
Yarinta da karancin tunanin Hasana ya sakata kula wani saurayi ta WhatsApp din nan har suke soyayya. Har tace min suka fara haduwa yana taba ta amma tace ba'a taba abinda yafi hannunta ba kuma mijin be taba sani ba har yau.
Amma tana kuka take gaya min tace aunty wallahi duk abinda nake nasan ba daidai nake ba kuma nasan ban kyauta ba kuma ina dana sanin hakan. Kawai shaidan ne yake min fitsari a zuciyata yake sani aikata wannan mummunan aikin.
Tace har kunya takeji in zatayi sallah se taga kamar abin kunya ne ta kalli ALLAH bayan tana aikata wannan mummunan aiki?
Tace kuma aunty inada tsananin sha'awa amma ban taba bari munyi sex da shi ba sadai kuma ina masturbation(sa kanta jin dadi da kanta).
Tace gashi na kasa fadawa kowa saboda tsoro nakeji.Nace waiyazubillah! Auzubillah!
Hasana garin yaya kika bari shedan ya miki fitsari har haka? Bayan kuma kinsan ba kyau abubuwan da kike aikatawa. Tace wallahi aunty bansan ya zanyi bayanin ba nidai kawai mafita nake nema da kuma kara kusanci da ubangiji na dan se inji in na mutu yanzu kamar baze min rahama ba. T
ace shi kuma masturbation din ina kallon porns ne se nake releasing.Nace saurareni Hasana dakyau.
Shi ALLAH AL GAFURU NE KUMA AR RAHIMU yana gafartawa kuma yana yin rahama kuma ba'a cire rai da rahamar ALLAH.
Ki daure ki dage da ibada da yawan azumi sosai ki sami kusanci da ALLAH.
Ita zuciya mu muke koya mata son yin sa'bo gaskia kuma muke renonta a hakan seta tashi a hakan tafi karfin mu. Amma babban abin godiyar da fatan rahamar Allah shine in kana laifi kuma kasan laifi kake yi kuma kana jin haushin laifin kana dana sanin yinsa har kana son denawa Allah da izininsa ze yaye maka.Yanzu ki dena kallon matsalar mijinki ki fara gyara waannan abubuwan. Ki je ki ta sallar dare, ki dinga azumi ki kuma yawaita istigfari.
A kullum in zaki iya kiyi istigfar dubu. In kinji zuciyarki na kokarin tuna miki se ki dage da auzubillahi. So nake kije kiyi min wannan ki dawo.
Na baki wata uku, ki tabbatar kin dena aikata dukkan wadannan zunuban.Ki fara sanin girman laifinki. Duk da baki zina ba amma kin kusanceta.
Da kinyi jefewa ne hukuncin matar auren da ta aikata zina.
Ki dinga tuna wannan ki nisanceta.
Jikinki yafi karfin tabawar wani wanda be biya sadaki ba.
Darajarki tafi karfin haka.
Kimarki da mutuncinki da iliminki duk sunfi karfin haka.Masturbation yana nisanta mutum da rahamar ALLAH. Kallon tsaraicin wasu yana makantar da ido sosai ki dena. In kayi releasing ta masturbation abin baya fitowa seya kume maka a mara ya sa maka chuta me tsananin as time goes on in baka dena ba.
Har wari gaban masuyi yakeyi kamar na rubewa.
Ki dena ki kuma nisancin aikata hakan. Mukayi sallama akan nanda wata uku zata dawo.Naita tuanin Hasana a raina wallahi ina mata fatan ALLAH Ya mata rahama, Ya agaza mata, Ya yafe mata,Ya kuma kori shedan daga cikin zuciyarta. Ina ta tunanin mijinta ina cewa ALLAH Ya shiryashi amma gaskia mugu ne ace dan shekara arbain da 'yar shekara ashirin da biyu ya dinga mata haka?
Gaskia mugu ne.Zainab Saleh
Zainab ta shigo itama kamar kowa muka gaisa sannan take bani labarin tata matsalar. Ita mijinta ne yake nemanta ta baya be taba nemanta ta gaba ba. Shiyasa har yau basu taba haihuwa ba gashi shekararsu 3 da aure. Tace kuma a gidansu ba'a ganin laifinsa in tayi yaji a ranar ake maida ita ko tuhumar me yake mata ba ayi saboda yanada arziki sosai. Shi yake ciyar da iyayenta. In tanaso ta fadi matsalarsa se a fara mata fada ana cewa ai yana kokari. Gashi tana son haihuwa. Kuma tace har kasa bayan gida take se an mata famfo a asibiti.Nace auzubillah!!!
Ai ba aure ga duk mijin daya nemi matarsa ta baya. Zamu zo da malami da hukuma musa ya sakeki. Malami ze fadawa iyayenki kuskuren da suka aikata akan son zuciyarsu. Hukuma zata sa ya sakeki a take a gurin ki kwashe kayanki a kan idonmu ki wuce gidanku. Se mu nemi yadda zamu tallafa miki wurin tsayuwa da kafafunki yadda ba zaki zame wa iyayenki nauyi ba.
Kuma abu na karshe a kaiki asibiti ayi miki maganin ciwon daya sa miki. Ki yawaita istigfari da godiya ga ALLAH domin duk abinda ya faru da bawa jarabawa ce.
YOU ARE READING
❤MAHBUBI❤
RomanceLabari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...