page 7 & 8

408 37 4
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


💅🏻 *POSHLEEMAH*💅🏻


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)


*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*


QUOTE:-" The beauty of life is, while we can't undo what is done, but we can see it, understand it, learn from it and change."


7⃣ & 8⃣

Leemah gudu take ba tare da ta waiwayi baya ba saboda tsabar tsoro batama san ina ta dosa, fitowan ta yayi daidai da zuwan wani mota wanda saura kadan ya bigeta, wani wawan birki me mota yaja itakuma tsayawa tayi jikinta har rawa yakeyi, fitowa yayi daga motan yana tambayarta ko bataji ciwo ba amma ga mamakin shi se gani yayi tana mishi murmushi, be gama mamaki ba yaji ta rungumeshi tana cewa "Dad wen did u come back?".


Seda yaji wani abu da ta rungumeshi lokaci daya ya sake kallon ta, ji yayi tace mishi "Dad", seda ya maimaita " Dad" a zuciyarshi sannan yace mata "sorry bt am nt ur Dad maybe u mistake me for ur Dad", baki bude ta tsaya tana kallonshi galala, ita tana ganin duk da ba wani sannin Dad dinta tayi ba amma ai tasan kamaninshi kuma gashi a gabanta amma yanace mata shi ba Dad dinta bane, sake kallon shi tayi seta fashe da kuka tana cewa " no, u ar my Dad, u ar my Dad", ganin wannan da gaske take a zuciyarshi yace "toh kodai 'yar Al Hussain ce, bari dai in tabbatar", kallon ta yayi yace " ok stop crying baby, cry no more", shiru tayi tana goge hawaye yace mata "ya sunanki", kallonshi takeyi tana mamakin ya za'ayi Dad dinta yace besan sunanta ba, ganin kallon yayi yawa yace " look seriously am nt ur Dad, amma kila ina kama da Dad dinki ne shiyasa kikace nine Dad dinki, yanzu fada min sunanki kinji", cikin kuka tace "sunana *HALEEMAH AL HUSSAIN MADDO*.



Nan take yaji ya tsani kanshi ace 'yar shi a gabanshi amma besani ba, gashi da alama Al Hussain baya zama tareda ita, toh a hannun wa take, tambayan da yama kanshi kenan ganin ba amsa yace mata "sorry am nt ur Dad bt u can call me Dad as well uhmm", kuka takeyi sosai ita bata yarda ba babanta ne ganin tana neman tara mishi mutane seya dauke ya kaita wurin security yace in sunji ana cigiyarta su mika ta shima a waje ya ganta, mota ya koma ya dora kanshi kan steering yana tunanin badan yama su Malam Maddo alkawarin cewar baze sa hannunshi a harkar Al Hussain da 'yarshi ba da ba abunda ze hanashi karbanta ba hannun komawa take, amma baze iya ba saboda kwanciyar hankalin family dinshi yakeso, gashi da gani yasan tana cikin hutu dan ko kadan ba alaman wahala a tattare da ita sedai she made clear tana missing din Dad dinta, ganin tunanin ba inda ze kaishi seya kira matarshi yace suzo su wuce yana bakin gate, su kuma alokacin suna wurin security saboda ance musu a ganta kuma koda sukaje kuka kawai takeyi tambayan duniyar nan ba wanda basuyi mata ba amma taki cewa komai, da haka Mom din Aryan tawa Nanny sallama suka wuce Aryan se waiwayanta yakeyi jikinshi duk yayi sanyi saboda yadda take kuka, a mota shiru yayi Dad dinshi yace " my boy ya kayi shiru, ba magana", yace "Dad nayi kawa a park, bt she got missing, yanzu muka ganta nd she was crying kuma taki ta fada abunda aka mata", kallon matarshi yayi me suna Hajara duk da yasan yarinyar da Aryan ke magana akanta amma se yayi kaman be sani ba yacewa matarshi " wata frnd kenan danki yayi", tace "wlh wata kyakyawar yarinya ce wai sunanta Haleemah koni ta shiga rai na", shiru yayi can kuma seyace " toh kai kuma ai tun da anganta bashi kenan ba", Aryan yace "bt Dad she was crying", Dad yace " kila saboda ta bace ne take kuka", shiru Aryan yayi ganin mahaifinshi baze gane ba, da haka har suka karasa gida.



Leemah har sukaje gida kuka takeyi dan ita har yanzu bata yarda ba ita tasan Dad dinta ta gani saboda haskensu daya, tsayin daya, kamaninsu daya, maganan su daya, komai iri daya amma kuma wai yana ce mata shi ba Dad dinta bane, ranan da ciwon kai ta kwana dan har tayi bacci bata bar kuka ba Nanny tayi lallashin duniyan nan amma Leemah taki tayi shiru, shima Aryan ranan gashi nan daine, koda ze kwanta hotun da ya dauki Leemah yaketa kallo da haka barci ya dauke shi, Mom dinshi ta shigo duba shi taganshi rungume da iPad dinshi yana barci tace "dan rigima har anyi baccin", ita duk a tunaninta game yakeyi, a hankali tacire iPad din daga hannunshi se a lokacin taga ashe hoto yake kallon, murmushi tayi ta gyara mishi kwanciya taja mishi comforter sannan ta fita. Shima Al Hassan ranan suku suku ya kwana saboda Leemah ta tsaya mishi a rai kaman kaya, duk yadda yaso ya cire tunanin ta a ranshi abu yaki ci sema kara tunanin ta daya keyi, a ranan Nanny takira Dad din Leemah tagaya mishi halin da Leemah ke ciki sosai hankali shi ya tashi ya tambayi kanshi toh me yasata irin wannan kukan, nan yacewa Nanny Insha Allah a cikin wannan week ze zo ya dubata, sosai Nanny taji dadi dan tasan ko ba komai zata dan huta da rigiman Leemah.



Washegari da zazzabi Leemah ta tashi wanda ya kaita ga kwanciya asibiti nan doctor yake cewa Nanny suna bari stress na mata yawa ace karaman yarinya kaman wannan tasan tinani, nan Nanny ta shaida mishi rashin iyayenta a kusa da ita ne ya janyo, amma Insha Allah za'a kiyaye nan gaba, yace toh a kiyaye, nan Nanny ta sake kiran Dad din Leemah ta sake shaida mishi halin da ake ciki yace zuwa Friday zezo, kwana uku tayi aka sallameta suka koma gida.


Allah sarki Leemah😔

Reader me zakuce akan abinda Al Hassan yayi, kuna ganin abunda yayi ya dace ko be dace ba? Comment😎.


_Mzz Daddy💋_

POSHLEEMAHWhere stories live. Discover now