Page 39 & 40

313 36 2
                                    

Washegari ta koma gidansu Shamsiyya saboda ta kaita asibiti a duba mata kafan, tun daga waje takejin kamshin abinci nan tayi sallama ta shiga suka amsa mata cike d murna Shamsiyya tazo ta rungumeta, Leemah ta tambaye ta ya kafan tace da sauki, nan suka shimfida mata tabarma ta zauna Mama ta zubo mata dantamalele wanda yaji ya'ji da manja ga tumatur da albasa kamshin manjan se tashi yakeyi, take miyaun ta ya tsinke amma ita tunda take bata taba ganin wannan abinci ba, kallon mama tayi tace "Mama ban iya ci ba, me wannan", Mama tayi murmushi tace " dantamalele ne dandana kiji tukun", sannan mama ta tashi ta fita Leemah zata sa spoon Shamsiyya tayi saurin cewa "Yaya Leemah karkici da spoon,yafi dadi da hannu", Leemah ta kada kai sannan tace " toh kawo min ruwa in wanke hannun", ruwa ta kawo mata cikin kwanon samira wadda duk yayi tsatsa, haka Leemah ta wanke hannunta sannan ta fara ci, sau daya ta tai baki ta lumshe ido, ta kai na biyu a haka ta dinga ci duk da zafinshi amma bataso ta daina saboda dadinshi, mama ce ta shigo da ruwan gora Leemah tace "Mama ai da baki wahalar da kanki ba", Mama tace " yata karki damu, ya kika ji abincin", tace "Mama dadi", nan taci gaba daci bata ankara ba seji tayi Mama na cewa " a karo miki", kallon plate din tayi taga ta cinye kwano take tsidewa,tayi murmushi tace "na koshi mama, na gode", tace " ba godiya", seda ta wanke hannu sannan tasha ruwa tace "toh tashi muje kar dare ya mana a hanya", nan sukawa mama se sun dawo ta rakasu da addu'a sannan sukaja mota suka wuce.


Suna cikin tafiya Leemah ta tambaye Shamsiyya tace " Shamsiyya wai ku kadaine a gidan nan", tace "eh mukadai ne, tunda babana ya rasu aka koremu daga gidan da muke saboda dukin hayanmu ya kare, shine wani mutumi ya taimaka mana da wannan gidan, yace muyi maneji kafin mu samu wani gidan, toh yanzu ma mutumin yace yanaso ya gyara gidan saboda danshi zeyi aure kuma nan zasu zauna da matan", Leemah tace " kenan nan ma zaku barshi", Shamsiyya data fara hawaye tace "eh", Leemah ta tausaya musu tace " share hawayen ki,kina zuwa sch", tace "a'a se islamiyya, shima islamiyyan malaminmu ne ya dauke min biyan kudin laraba", Leemah ta jinjina kai a zuciyarta tace " lallai a yayinda rayuwa kewa wasu dadi lokacin wasu ke cikin kunci, amma Insha Allahu sena taimaka musu", nan ta cewa Shamsiyya "karki damu, da kinsamu lfy zan saki sch", dadi sosai Shamsiyya taji tanata zuba mata godiya ba adadi.




Sunje asibitin Faruoq na duba wani saboda haka seda sukajira kuma da gangan ya dade saboda yasan Leemah ce yanaso ya kullar da ita, iya kuluwa kowa ta kulu saboda seda sukayi zaman kusan awa daya be fito ba, office dinshi suka shiga bayan yace su shigo yauma yana nan ya rufe hanci Leemah a zuciyar ta tace " wannan dan iyayi ne", zama sukayi Shamsiyya ce kawai ta gaishe shi saboda Leemah ta kulu shiyasa ko kallonshi ba tayi ba, shikuwa se satan kallonta yakeyi yana murmushi, ya gama dubawa ya cire bandage din yace "kidinga hankali da kafan saboda kisan karaya kika samu, in ba haka ba slight mistake zakiga ya goce", tace " toh na gode" sannan suka mike suka fita shikuma ya koma ya zauna tareda bin bayansu da kallo.





Suna zuwa gida Leemah ta zauna takalli Mama tace "Mama inaso muyi wata magana", mama tace "inajinki" tace "inaso ku dawo gidana da zama inyaso se ki dinga min girki ina biyanki duk wata dan masu abincina basu kaiki iya girki ba", Mama tace " ke yar nan, iyayenki kuma suce me", tayi murmushi wanda zamu iya kiranshi da yake tace "bandasu" mama tace "bangane ba", nan Leemah ta bata lbrn komai akan iyayenta da yadda take zaune ita kadai a gida, sosai Mama ta jinjina alamarin tace " shikenan, ba matsala, yaushe kikeso na fara", tace "ko yau ne", mama tace " a'a kinga dare yayi, gobe se muzo, bamu address dinki", tace "a'a zan aiko a dauke ku, bari na kama hanya se goben, amma mama dan Allah da safe zakizo", tace " ba damuwa Allah ya kaimu goben", ta amsa da ameen sannan ta wuce, mama kuwa har rawa tayi dan murna se dadi takeji tanasawa Leemah albarka, nan Shamsiyya ta fada mata tace zatasa ta sch, murna wurin su mama ba magana.



Washegari seda Mama taje wurin me gidan ta mishi godiya sannan Mati yazo da yake Leemah ta bashi address, ya dauke su ya kaisu, se kallon gidansu sukeyi suna zuba kauyanci, mama tace "aljanar duniya", har ciki Mati ya kaisu Leemah da murnarta ta tarbesu sannan ta kira duka en aikin gidan ta shaida musu cewar mama ce sabowar cook din gidan yanzu amma su sani ita kadai zata dingawa girki, sukuma tsohuwar cook dinsu taci gaba da musu suka amsa da toh sannan suna watse suna kananun maganganu, daki Leemah ta kaisu tace Mama ga dakinku nan, sosai suka mata godiya sannan suka shiga suka kimtsa dakin harda bayi a ciki, seda mama ta canza kaya sannan ta fito ta shiga kitchen tana tunanin abunda zata dafa mata da rana, danwake ne ya fado mata a rai nan ta kwaba flour ta shiga sassaka danwaken ta sauran se gulma sukeyi suna dariya a ganinsu Leemah bazataci danwake ba. Tana gamawa ta jera kan dinning sannan ta aika Shamsiyya ta kirata, Shamsiyya ta kirata suka fito tare sosai tayi mamakin ganin danwaken dan bata sanshi ba, nan Mama ke cemata danwake ne da flour akeyi, ta kada kai tareda zama ta sumaci, sosai ya mata dadi tana gamawa Aryan na shigowa gidan da murmushinta ta tarbeshi sannan ta fada mishi ga mahaifiyar Shamsiyya kuma sun dawo gidan da zama yayi murna shima at least princess dinshi bazata dinga zama ita kadai ba, shima danwaken yaci yana santi su kuwa se dariya suke mishi, yana gama sukaje garden suka zauna.




Suna zaune yace "princess", tace " na'am", yace "Dad dina yace yanaso ya ganki, so tunda gobe Sunday gobe zamuje", gabanta taji ya fada tayi shiru yace " bakice komai ba", tace "tsoro nakeji kar yayi disapprove din relationship dinmu", yayi murmushi yace " my Dad is nt dat kind of a person, so karki damu" tace "shikenan Allah ya kaimu goben", nan suka ci gaba da hiransu amma ita gabadaya hankalinta baya wurin, tambayan kanta tayi " mesaya takejin tsoron haduwa da Dad din Aryan, meyasa gabanta ke faduwa, mesaya takeji kaman bazasu karbeta ba", nan ta dinga tambayan kanta questions (ni kuwa nace amsa na wurin Mzzdaddy).




Dan dan dan, der is fire on d mountain, run run run🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀, finally d page everyone is waiting for is her, comment non stop nd i will update d next page today, so it's left for u to decide🤷🏻‍♀.


Don't forget to share,comment nd vote
Vote
Vote



Luv yah😘




Poshleemah



Mzzdaddy💋



POSHLEEMAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora