Page 79 & 80

334 23 0
                                    

         Washegari aka kira uncle din Ni'ima aka sanar mai da auren yace baze samu zuwa ba amma a samar mata wakili saboda haka Mallam Maddo ya mata wakili limamin garin kuma yama Al Hussain. Ranan Juma'a ana saukowa daga masallaci aka daura musu aure suka dawo gida nan Mallam Maddo yasasu gaba ya musu nasiha me ratsa jiki sannan suka wuce saboda a ranan zasu koma Abuja, duk ana ta musu fatan alkhairi.



       Washegari su Al Hassan suma suka dau hanyar Abuja amma banda Leemah dan Inna wuro tace wurinta zata zauna har ayi biki saboda tanaso ta gyara jikanta, Aryan beso ba amma dole ya tafi duk da zasuyi kewan juna, a ranan da suka tafi a ranan Inna wuro ta fara gyara jikanta itakam Leemah kome aka bata sha takeyi saboda zakinshi bata damu da tambaya ko meye wannan ba, haka naci ma ci takeyi duk da batasan dalilin da yasa ake dura mata kayan zakin ba, kullum se sunyi waya da Aryan ba safe ba rana ba dare gashi wani kyau takeyi fatan jikin ta har wani tsantsi yakeyi kaman ka taba jini ya fito, sosai suka sake da Mallam Maddo dan duk zafinshi bayayi ma jikokinshi, kullum kuwa seta sha zallan kindirmo da nama shiyasa tayi bubul abunta ba abinda ya dame ta, sukanyi waya da Dad amma ko yaba maman ta bata fiya sake mata ba.



       Aryan ya gama gininshi se jiran amarya, sosai gida yayi kyau, ada ana cewa gidan Ashraf (in baku manta Ashraf din Zynah na toh shi nake fada), neighbor dinsu one in town amma yanzu gidan Aryan ne ya koma one in town dan kap unguwar babu gidan da yakai nashi. Furnitures da electronic gadgets da kitchenwares komai na gidan bana Africa duk Romanians ne komai daga Rome akayi order dinshi, gida  duplex ne me 6 bedroom ba yawa se 2 parlour da kitchen da store gabadaya dai tsarin gidanshi ya fita daban koma ba abunda babu aciki (naira masu gidan rana idan akwai ta ba abinda mutum baze iya yi ba).



 
       Mom din Aryan da Mom din Leemah sukaje Dubai sukama Leemah siyayyan kayan lefe da kayan amarci suka dawo naija, Aryan da Leemah kam zumudi ba'a magana dan sunfi kowa daukin wannan auren har basu iya boyewa, Affan da Zeebaby suna can suma suna nasu planing din dan suma baza'a barsu a baya ba, su shamsiyya an kai musu anko iyan shamsiyya tace ta dau nauyin yin kayan cincin dasu dubulan ba tare da ta karba ko sisi ba, biki fa kowa shiryawa yakeyi babu wanda keson a barshi a baya saboda aure ne bana kananan mutane ba aure ne na  POSHLEEMAH daughter of the richest yahoo boy during his young age and greatest doctor ever and ARYAN son of the greatest business tycoon.


        Farouq yayi nadama iya nadama da yabari shedan ya rudeshi ya kasa yafewa Leemah, gashi yanzu garin daukan fansa shi ya end up a prison kaman wani criminal, kullum yayi sallah seya roki Allah ya dauki ranshi dan a gurinshi gwara ya mutu da ya zauna da wannan bakin cikin, duk yayi baki ya tara suma wanda ba kyan gani , ya rame kaman bashi ba gashi yanzu his no longer a doctor tunda an karba license dinshi. Shi kuwa Sudias ya zama boss a cell dinsu, su takwas ne a ciki amma shine boss se abunda yace gashi kullum cikin mishi fifita suke ba abunda ya dameshi duniya taimishi dadi bashi da matsalan komai dan duk a tunaninshi har yanzu Leemah bata tafiya.



       Yau biki saura sati daya kacal saboda haka Al Hussain yaje har yola dan dauko Leemah da Inna wuro dan Mallam Maddo yace se ana gobe daurin aure zezo, wannan ne karo na farko da inna wuro tazo Abuja, gidan Al Hussain ta sauka saboda Leemah, en uwansu na yola duk an fara hallara gida ya fara cika haka side din Aryan ma en uwan  Dad da Mom dinshi duk sunfara zuwa, news, magazine, radio TV stations ko ina anyi announcing wedding din, se jiran rana.


      Leemah na shiga dakinta ta kira Zee da Affan da Aryan duk ta shaida musu ta dawo, sukace gasu nan zuwa sannan ta tashi ta shiga wanka, Zee ta rigasu zuwa sanda taga Leemah sakin baki tayi tana kallonta sannan ta kai yatsanta ta taba Leemah saboda ganin yadda duk ta canza tace "Leemah kece ko kuwa bake bace", wani kallo Leemah ta mata tace " kurwana ne a nan 'yar rainin sense", Zee ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah na halitta, irin wannan kyau haka aise Aryan ya rude, ke kin ganki kuwa, me kike ci kike sha kikayi wannan kyan, gabadaya se kika fito a balarabiya babu ma wanda ze ganki yace kin hada iri da Fulani", itadai Leemah murmushi tayi tace " ki daina zuzutani dayawa, ba wani kyau, kawai dan baki ganni kwana biyu bane", "hummm", shine kadai abunda Zee tace wayan Leemah yayi ringing ta dauka taga Affan ne yace mata yana garden tace gata zuwa, seda tasa nikab saboda kar a gane ta sannan ta fito ita da Zee suka tafi garden din, cire nikab dinta tayi Affan seda ya hadiye miyau daya ganta, tsayawa yayi yana kallonta amma da yayi la'akari da Zee na wurin seyace " amarya kinsha kamshi", tayi murmushi tace "Affan long time no see", yace " ba kin gudu kin barmu ba", "toh ai gashi na dawo", ta fada tana murmushi, zama sukayi su uku sunata hira ita kuma se kallonta agogon hannunta takeyi saboda kar a nemeta ba'a ganta ba gashi kuma Aryan bezo ba, nan su Zee suka gayamata cewar sun hada mata party dan ita Leemah cewa tayi daga walima ba abunda za'ayi amma bata musa musu ba tace shikenan, Affan yayi receiving call Mom dinshi na neman shi Zee ma tace zata wuce saboda akwai abunda zatayi saboda haka Leemah kadai ta rage a garden din tana jiran Aryan.



            The next chapter will b d wedding chapter, I'm glad d story is finally  coming to an end, who's eager about the wedding?

       Kindly vote, comment and share

Luv yah😘


Poshleemah


Mzzdaddy💋

POSHLEEMAHOnde histórias criam vida. Descubra agora