Page 43 & 44

311 26 1
                                    

             Da sallamansu suka shiga gidan yace mata ta zauna sannan ya shiga ya kira iyayenshi, Mom ce ta fara saukowa da murmushin ta tana cewa "ai ni nayi fushi, ko a kawomin ziyara", sunkuyar da kai Leemah tayi tana murmushi, Mom na zama Leemah tsugunna ta gaishe ta Mom ta amsa tareda cemata ta koma kan kujera ta zauna, sannan ta kira me aikinsu tace ta kawo mata abin sha, sosai mom ke janta da hira dayake Mom batada matsala kuma cikakkiyar yar boko saboda haka komanta tana yinshi ne according to civilization, suna nan zauna Dad ya sauko Leemah tunda ta kai idonta kanshi bata dauke ba, a hankali tace " Dad", duk sun jita suka juwo suna kallonta itakuwa se cigaba tayi da "Dad dama family biyu ne da kai, shiyasa kayi dumping dina", gabadayansu kansu ya daure banda Dad da tun kiran farko data mishi yagane yar Al Hussain ce ko bata fada ba, Aryan ne ya kalli Dad din shi yace " Family biyu kuma?", murmushi Dad yayi yace "ni ba Dad dinki bane, amma zan ita cewa ni second Dad dinki ne", gabadayansu kallonshi sukeyi, ya nemi wuri kusa da matarshi ya zauna sannan ya kalli Leemah yace " Haleemah ykk,ygd", shiru ba amsa se binshi da ido da takeyi dan aganinta ko shakka babu wannan Dad dinta ne, murmushi yayi ganin batace komai ba yace "rayuwa kenan, har na cire rai akan sake ganinki se gashi dana kuma cousin dinki ya kawoki har gida wurin en uwanki", kallon juna sukayi itada Aryan sannan suka kalli Dad a tare sukace " cousin?", ya kada kai, gabadayansu kansu ya daure hatta mom batasan inda ya dosa ba sannan yace "Haleemah yata zoki zauna kusa dani kiji dumin mahaifinki.



           Kallon mom tayi mom ta mata alama da ta zauna, a hankali ta taso ta zauna kusa dashi ya rungumota jikinshi yace " ya dan uwana Al Hussain", da sauri ta daga kai ta kalleshi tace "en biyu ne ku", yayi murmushi yace " kwarai, mahaifinki shine Al Hussain, nikuma Al Hassan", tace "amma Dad dina bataba gayamun ba", yace " ai baze gayamaki saboda wasu daililai wanda zan sanar dake nan gaba", tace "indai Dad dina kaninka ne kenan kasan mom dina", gabanshi ne ya fadi ya kada mata kai kawai batare da yace komai ba sannan ya canza zancen da cewar " na dade ina nemanki, yanzu tunda Allah yasa na ganki, ki shirya by next week zamuje Yola garin mahaifinki kiga kakan ninki", wasu hawaye ne yazubo mata a ranta tace "amma Dad dinta be mata adalci ba, dama tanada family shine ya kulleta ita kadai a gida baya kai ta taga family dinta", Dad ne yace ta share hawayenta tunda ya ganta komai yazo karshe kuma yasan yanzu Al Hussain ze nemi hanyar gida, ta kada kai tareda cewa " toh meyasa babana be taba nuna min family dina ba kuma be taba kaini wurinsu", yace "it's a long story, duk ran da mukaje Yola zakiji komai", ta kada kai tareda murmushi a takaice dai ranan su mom sun nunawa Leemah gatan en uwantaka da bata taba gani ba dan har kwana sukace tayi tace tanada test gobe koma bata prepare wa test din ba amma zuwa Wednesday zatazo ta kwana.




          Mom din Aryan ne da Dad a daki tana cewa ya mata bayanin wacece Leemah dan ita kanta ya daure yayi murmushi ya janyo ta jikinshi yace " bana taba gayamiki cewar dan uwana dake dubai ya haihu ba tareda aure ba", tace "eh" yace "toh yarinyar kenan", dum dum gabanta ya fadi a zuciyarta tace " dama itace yarinyar da kowa yayi rejecting dinta", ta kalli Dad tace "har na tausaya mata, yar da batasan hawa ba batasan sauka ba anbi an daura mata laifin da banata ba", yayi murmushi yace " Insha Allahu komai yazo karshe, dan senasa Baba ya karbeta amatsayin jikarshi", tace "Allah yasa ya karbeta kuma Allah yasa Aryan ya riketa da amana", Dad yace " Ameen", Leemah da ta zage tanata hira ta tuna kila fa Affan na mota da sauri ta tashi tace "Aryan ni zanwuce, kasan inada test gobe,kuma zee tace zatazo", yace " tun yanzu, ki dan kara 1hr kinji princess ", tace " a'a bataza iya ba", yace "toh ina zuwa", zuwa yayi ya kira iyayenshi suka sauko sukace " har zaki wuce" tace "eh akwai abunda zatayi ne", sukace " ba matsala suka yi sallama bayan sun hadata da kaya kala kala sannan Mom tace ta tabbata gobe tazo suyi lunch tare tace ba matsala, har bakin mota Aryan ya rakata inda taga ba kowa shiga ta sukayi sallama sannan taja motarta tayi gaba shikuma ya koma gida, a daidai gidan da ta sauke Affan ta tsaya ta kirashi a waya yace gashi nan zuwa, ba dadewa ya fito yace "ai na dade ina jiranki ganin baki fito bane na koma gidan", tace " wlh hira ne ya dauke min hankali", sannan ta tada motan ta fita daga unguwan ta harba kan titi.(Allah sarki tsautsayi na kiran bawane batare da saninshi, inba haka Leemah da baki shiga motan ba).




            Seda sukayi dan nisa sannan tayan motar yabar jikin wheel dinshi ya gangara gefe, Affan yace "Leemah tsayar da motan, hw comes taya ya fita", kokari take ta tsayar motan amma inaaa ba brake, rasa yadda zatayi tayi ta dago ta kalla Affan murya na rawa tace " yaki tsayuwa", gashi sunzo kan bridge, daga kanda Affan zeyi yaga wani mota na zuwa ta direction dinsu gashi sukuma sunyi loosing control da sauri ya kai hannunshi kan steering tareda yin wani wannan u turn a kan bridge amma unfortunately juyarwa da yayi yayi daidai da zuwan wani babban motan wanda ya buge nasu Leemah motan ta ya gangara ya juya upside down, gaban wurin bonnet din ya kama da wuta, da sauri aka taru wurin ana neman ceto rayukarsu Affan aka samu aka fara cirowa saboda kofan side din Leemah yayi lock yaki bude wa, seda aka ciro Affan wanda yake numfashi sama sama sannan aka samu aka ciro Leemah wacce ita da gawa ba banbanci farin jallabiyanta ya koma maroon saboda jini, mutanen wurin har sun soma cewa ta mutu, motocin en sanda ne ya fara patrol a wurin, su sukace a kaisu hospital inda basu zame ko ina ba se DIFF saboda shine a kusa, ana zuwa da sauri akayi emergency dasu dan ceto rayukarsu. Aryan aka kira saboda shine second person da tayi waya dashi dan Affan suka fara kiran wayanshi be shiga ba, Aryan na zauna da Mom da Dad suna hira kan Leemah wayanshi yayi ringing, da sauri ya dauka ganin Leemah amma shock news dinda ya samu yasa ya fadi kasa warwas a sume, Dad ne ya dauka wayan a yayinda mom ta nufi wurin Aryan tana jijjiga shi tana cewa ya tashi, Innalillahi wa innailaihi raji'un kawai Dad ke maimaita Mom tace "wai lfy, meya faru, waye ya mutu", Dad ya kallita idonshi yayi ja yace " Haleemah ce tayi hatsari yanzu nan ", take mom ta daura hannu aka tana cewa " Innalillahi wa innailaihi raji'un", ruwan sanyi Dad ya dauko a fridge yazo ya yayyafawa Aryan, wani dogon numfashi yaja tareda cewa "Leemah!!!".




          Aradu na gaji, Allah sarki leemah😭😭😭 karki tafi ki barmu, we luv u way much, in kika tafi bamusan ina zamusa kanmu ba, fans ko taya Leemah da addu'a🙏🏻, Affan fight for ur life plss.



         Don't forget to comment,share nd vote
Vote
Vote



Luv yah😘



Poshleemah



Mzzdaddy💋

POSHLEEMAHWhere stories live. Discover now