Page 49 & 50

311 29 0
                                    

             Yau sati daya kenan da hatsarin su Leemah, Affan ya warke se dan abunda baza'a rasa ba, Leemah dai tana nan ko yatsama yanzu bata dagawa, badan kayan computer dake dakin yana nuna bugun zuciyarta ba da se dai ace ta mutu, likitoci sunyi bincike har sun gaji amma sun kasa gane abunda yasa har yanzu bata tashi ba bayan komai nata yana functioning amma tashi ne dai taki tashi yanzu suna planing fita da ita waje a dubata, Aryan duk yabi ya lalace kaman bashi ba, ya tara gashin gemu yaki ya aske, gashin kanshi dake samun gyara kullum yanzu beda lokacin su, office ma ya daina zuna kullum yana wurin Leemah, Dr Farouq kuma al amarin Leemah ya fara daure mai kai dan yasan yaci ace ta tashi kuma gashi a hannunshi case dinta yake abunda be sani ba shine duk sanda yazo ya dubata yamata allura Dr Sudais ze dawo ya mata nashi kuma shi overdose dinta yakeyi shiyasa kwata kwata kome aka mata jikinta baya karba, sunso kiran Dad din Leemah amma suka fasa saboda karsu daga mai hankali, su Shamsiyya ma hankalinsu ya tashi ganin kwana biyu Leemah bata dawo gida ba seda Aryan ya daure yaje yamusu bayani sannan har asibiti sukazo suka dubata.

        Yau ya kama Monday wanda a ranan ne kawai ake ganin MD din asibitin, Dad ne ya bukaci ganin MD akace baze samu ganinshi ba se nan da awa biyar, jira yayi har awa biyar din ya kai sannan aka mishi izinin shiga inda office dinshi yake first floor of the building, dattijon mutum ne gashi da fara'a cikin lokaci kankani yasa Dad ya sake, nan Dad ya mishi bayani matsalan Leemah yace "Doc yarinyar nan har yanzu taki tashi ko motsi batayi, dan Allah ka fadamun in ba abunda zaku iyayi mu fita da ita a duba ta", azijiyar zuciya doctor ya sauke sannan ya cire medicated glass dinshi ya kalli Dad yace " nima lamarinta na kullemin kai kuma yana damuna shiyasa ma nayiwa wani abokina waya, shima doctor ne kuma bature ne,yace min cikin satin nan zezo Nigeria wani project inyazo ze dubata in ba'ayi nasara ba se a fita da ita", sosai Dad yaji dadin wannan zancen yace "nagode da kokarin da kake mana doctor, na gode", doctor yace ba komai nan yace suma je tare ya dubata, suna shiga ga mamakin su sai sukaga Dr Sudais yana injecting dinta a cinya yana murmushi sosai abun ya daure musu kai Doctor yace " Dr Sudais dama kaine akan case dinta nazaci Dr Farouq ne", zeyi magana Dad yayi saurin cewa "kwarai Dr Farouq shi ke dubata ni wannan banma taba ganin shi ba", bam bam gaban Sudais ya fadi yayi saurin cewa " Dr Farouq yana wani aiki a lab ne shine yace nazo na dubata", sosai doctor yake mishi kallon baka da gaskiya, nan ya karasa ciki ya mika hannunshi yace "dora min dayan alluran a nan tunda biyu ne", hannu na rawa ya dora Doctor ya kalleshi sannan ya fita be zame ko ina ba se lab yaga ba Dr Farouq nan ya basu alluran yace su gwada mishi wani irin injection ne wannan kuma yanason result in less than 30mins sannan ya fita ya koma dakin still Dr Sudais na wurin yakasa wucewa saboda tsareshi da Dad yayi dan shima be yarda dashi ba.

          Doctor ne ya dawo yace "to my office now", sannan ya fita Dr Sudais yabi bayanshi gumi duk sun gama jikashi, wata nurse doctor ya gani yace " call me Dr Farouq ", sannan ya wuce sama ba dadewa se ga Dr Farouq sosai yayi mamakin ganin Sudais ya gaida doctor yace " u called for me", doctor yace "yes, i want u to explain why u hav to hand ur duty of a patient as a doctor wen u ar less busy", Farouq da kanshi ya daure yace " sorry sir but i can't remember handing my duty to anyone, and who's d patient", Doctor na kallon Sudais yace "Haleemah, nd Sudais here claims dat u asked him to check on her cus u hav something serious to handle in d lab, i went to d lab but u ar nt der can u pls explain", Dr Farouq ya kalli Sudais yaga alaman rashin gaskiya yace " Sir i didn't ask him to check on her cus i did that earlier before now and throughout today i didn't visit d lab", da sauri Sudais ya kalli Farouq yana ganin a matsayinsu na abokai ya kama ta ya rufa mishi asiri amma beyi haka ba, juyowa doctor yayi ya kalli Sudais yaga alamun rashin gaskiya a tattare dashi, zeyi magana akayi knock ya bada izinin shigowa wata nurse ce ta shigo ta mika mishi result din test din ya kalla tace "sir d injection happens to b lethal injection", da sauri doctor ya dago ya kalleta yace " if am nt wrong it causes unconsciousness nd paralysis??", tace "yes sir", nan idon doctor yayi ja ya dago yana kallon Sudais wanda ya sunkuyar da kanshi kasa yana tunanin abunyi, kallon kofa yayi sannan yayi yunkurin guduwa amma Farouq ya riko shi ya kai shi kasa yana naushin shi yana cewa " dama injecting dinta kakeyi shiyasa taki tashi", da sauri doctor ya kira en sanda sannan ya daga Farouq daga kan Sudais wanda bakinshi har ya fashe yana jini,waya doctor ya dauka ya kira Dad yace yazo office dinshi, ba dadewa se gasu shida Aryan, doctor ne ya kallesu ya sauke kai saboda kunyarsu sannan yace "wannan mutumin banzan da kuke gani shiyakewa Haleemah allura taki tashi, alluran da yake mata yana janyo unconsciousness da paralysis", Aryan ne ya kalli doctor yace " kana nufin Leemah tayi paralyse?", doctor yace "am not certain yet amma koda ta tashi ba lallai jikinta suyi aiki ba", jin haka hankalin Aryan ya tashi yayi wani kukan kura yayi kan Sudais yana kai mishi naushi ko ta ina ido rufe, da kyar aka kwaci Sudais daga hannun Aryan lokacin en sanda har sunzo, handcuffs suka sa mishi a hannu suka jashi, daidai gaban Farouq ya tsaya yayi kasa murya wanda Farouq kadai yaji abun yace " if i hav to go down den u go down wit me, remember we ar in dis together ", sannan yayi wani murmushi yayi gaba asibitin kowa kallonshi sukeyi suna mamakin me Dr Sudais yayi aka kamashi, shikuma Farouq tunani yake yi dan be gane we ar in dis together dinda Sudais yace ba tunda shi yasan bashi da hannu a ciki, Aryan kuwa zama yayi ya hada kai da gwiwa yana kuka ba wanda yayi yunkurin lallashin shi saboda ansan d pain he's going tru is much.

      Yanzu dai muna da hope akan Leemah amma me kuke ganin Sudais zema Farouq? Comment.

      Don't forget to comment, share nd vote
Vote
Vote

Luv yah😘

Poshleemah


Mzzdaddy💋

POSHLEEMAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora