Page 1 & 2

1.3K 62 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

💅🏻 *POSHLEEMAH*💅🏻


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCAITION*

QUOTE:-" Life is not about people who act true to your face. Its about people who remain true behind your back."

     _I dedicate dis page to Asy Khaleel, u will always b my ladder, tnx for d luv nd support😘_

1⃣ & 2⃣

     Makeken parlour ne babba sosai wanda aka kashe ma kudi, tsayawa fadan kyan parlour bata lokaci ne, yarinya ce wacce bazata wuce shekara shida ba fara sosai kaman balarabiya idon ta fari tas se kwayan idon golden, lips dinta dan karami pink se hancinta me shegen tsini wanda ya kayata kyakyawan fuskan ta tsaye da pink Teddy dinta a hannu wanda tsayinsu da Teddy din daya, sanye cikin uniform din school din su inner white se pinafore navy blue, kanta an mata kalaba manya wanda ya zubo har bayanta sannan akasa roba aka kaman kasan saboda kar ya kwance dan santsin gashin, kuka takeyi bil hakki ita inba Dad dinta ze kaita school ba bazata ba.

     Nanny dinta dake tsaye tana aikin lallashi tace "princess bari Mati ya kaiki school karkiyi latti, Dad dinki yana hanya kinga gobe seya kaiki", da karfi yarinyar tace " No Nanny, just leave me alone", lallashinta Nanny keyi aikuwa ta kwanta kasa tasoma birgima tana cilla kafa tana kuka uniform din da aka goge duk ta bari yayi squeeze seda Nanny ta mata tsawa sannan ta tsagaita kukanta tana jan numfashi Nanny tace "princess ki bari Mati ya kaiki, in kin dawo zan kaiki park kiyi wasa", kallon Nanny tayi sannan cikin karamin muryanta tace " promise", Nanny ta kada mata kai tareda mikar da ita tagyara mata kayanta da fuskanta ta dauko lunch box dinta  da school bag suka fito makeken compound din gidan, kiran Mati Nanny tayi ya karaso tace "gata kuyi sauri dan ta riga tayi latti", yace " toh", tareda karban kayan hannun Nanny sukaje parking lot.

    
     Seda na rufe ido na sake budewa na murza idona dan in tabbatar da abunda nake gani, motocine sunfi ashirin anyi parking dinsu a parking lot din, inda naga wurin guda shida daga ciki special plate number ne da sunnan  *LEEMAH 1* har zuwa *LEEMAH 6*, tsayawa sukayi Nanny tace "princess wani mota kikeso ki shiga", (nace lallai, motan ma se wanda ta zaba), cike da shagwaba ta nuna wani KIA ja aikuwa Mati ya bude kofan Motan yasa bag da lunch box dinta ciki sannan zata shiga Nanny tace " toh princess da teddy din zaki sch", ba tareda ta kalli Nanny ba tace "yeah", tareda shiga ta hakimce a bayan mota taga boss.😎 Nanny ganin tanaji da rigima yasa ta kyalle tana daga mata hannu har suka bar gidan sannan Nanny ta koma ciki cike da tausayin wannan yarinya.

     Nigerian Turkish suka nufa har an rufe gate din sch din saboda lokacin tara ma ta wuce, horn Mati yayi gateman din sch din ya bude mai gate ya shiga yayi parking sannan ya fito daukan ta yayi saboda har ta soma bacci dan taji dadin dan tafiyan da sukayi, jin alamun an dauke ta ne yasa ya bude ido ganin sunkai sch seta bata rai Mati ko kallon ta beyi ba ya kaita class dinsu nursery 2, sit dinta yaje ya zaunar da ita teacher dinsu duk da yare ce amma tanajin Hausa tacewa Mati "wato yarinyar nan bazata daina latti ba koh, me takeyi a gida da bata zuwa da wuri, bata taba assembly ba a sch din nan ba tun da nasanta"(yarinya tun kina karama kin ajiye record bravo👍🏻), Mati yace " ayi hakuri bazata sake latti ba", teacher tace "naji", sannan ta juya taci gaba da aikin ta,mota ya koma ya dauko mata lunch box da jakan ta da teddy dinta ya dawo ajin, dayake sch din masu kudine shiyasa ba takura saboda haka koda teachern taga Teddy din ba abunda tace.

     Tun da taje sch ba wanda tama magana, shiru tayi ta zauna a sit dinta amma duk abunda ake koya mata yana shiga kuma ya zauna daram, ana break teacher dinsu Mrs Martina Alex tazo ta budewa kowa lunch box dinshi ta ajiye musu a gabansu, Leemah kallon abinci ta tayi chips ne har da ketchup, se yoghurt da  chocolate, bata taba abincin ba chocolate din ta dauka tana ci, suna fita playground taje zata hau swing da teddy dinta taji an fizgo ta juyawa tayi taga Affan tsaye yana kallon ta "Hi", yace mata ta harareshi ta juya ya kuma janyo ta yace "let's play wit ur teddy", " no way", tace mishi sannan ta bar wurin ma gaba daya amma seda ya bita ya kiranta "Leemah wait for me, let's play together", bata tsaya ba amma seda ya cimmata yace " u knw Mrs Alex said we should b frnds since we ar sit mate", hada rai tayi tace "who cares", sannan ta wuce class ta zauna tasa teddy dinta gaba tana wasa da ita.

    3:30pm aka tashe su, jakanta ta dauka tasa a baya tasa lunch box dinta a wuya ta dau teddy dinta ta fito, zama tayi akan wani counter tana jiran Mati, nan ta dinga kallon yaran da iyayensu sukazo daukan su, Affan ta hango yazo ya wuceta da gudu ya nufi Mom dinshi tareda rungumeta sannan yace "I miss u mom", " miss u more my baby", mota suka shiga suka wuce, me Leemah zatayi inba kuka ba tana maimaita "Dad wer ar u, come pick me up", muryan Mati taji yana cemata " wai ke yaushe zaki daina wannan kukan", harara ta watsa mai sannan ta mike tareda barin jakanta da lunch box tayi gaba, daukan kayan yayi yana girgiza kai wai ace karaman yarinya ke mishi rashin kunya, shi badan salary din da ake bashi ba daya bar aiki, amma yanzu in yace ze hukuntata ya rasa aikinshi ya gama, shiga motan yayi ya bar harabar sch din.

     Suna zuwa ta shiga ciki ya biyu ta da jakanta a parlour ta cire takalmi da sock da uniform ya rage daga ita se singlet da pant kuka ta zauna tanayi Nanny dake kitchen taji kukan ta da sauri ta fito tace "princess lfy, daga dawowa se kuka, ke bakya gakiya da kuka kullum", shiru tayi ta kalli Nanny tace " Nanny Mom da Dad dina ba sona koh",(se a yanzu naji tayi hausa nace ashe dai tanajin hausa), Nanny cike da tausaya tace "waya ce miki haka, suna sonki mana", " if dey luv me, y ar dey nt here wit me", Nanny a zuciyar ta tace "yarinyar nan badai wayo ba", sannan a fili tace " saboda suna neman abinda zasu baki comfortable lyf dashi", cikin tsawa tace "i don't need a comfortable lfy, all i need is my parents", sannan ta tashi ta haura sama ya shiga dakinta tayi banging kofa tana kuka.

     Kyaleta Nanny tayi dan tasan ko ta lallashe ta baza tayi shiru ba, ta riga ta saba da rigiman Leemah shekara shida kenan suna abu daya, ba rana ta Allah da Leemah bazata tambayi mahaifanta ba wa'anda su ko lokacin ta ma basu dashi, kayan da ta wastar a nan parlour Nanny ta kwashe sannan ta shiga kitchen dan ta karasa abunda takeyi, Leemah tayi kukan har ta gaji bacci ya sureta se fitar da numfashi takeyi dagani kasan baccin wahala takeyi 4:30 Nanny tazo ta tashe ta, ta mata wanka tasa mata riga da wando three quarter ta bata abinci taci, sannan tace taje tayi assignment, tana gama assignment malaminta na zuwa nan tasa dan karamin hijab dinta ta fito zuwa wani daki dake compound da aka ware mata tana karatun islamiyya a ciki.

     Da sallama ta shiga dakin tace "ina wuni mallam", yace " Haleemah ykk", seda suka gaisa sannan ta zauna Qur'ani ta fara karanta mishi, se kunji kira'an ta kowani harafi tana bashi hakkinshi, tana gamawa ya kara mata sannan ya mata fiqhu, dama subject biyu yake koya mata daga hadisi se fiqhu sekuma Qur'ani, karfe shida suka gama karatun su a ranan sannan ya mata en nasihohi ya sallamate ta shiga gida. Koda ta shiga kallo tayi har akayi sallan magrib ta tashi tabi Nanny sukayi sallah seda akayi isha sannan sukaci abinci, Nanny ta dinga bata tatsuniya har barci yaudake Nanny ta kaita ta kwanta.


*ASALINTA*

     _Meyasa kuke ganin iyayenta sun barta hannun nanny ba en uwanta ba ko a hannunsu?, comment 😎_


     _Mzz Daddy💋_

POSHLEEMAHTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon