Page 9 & 10

447 34 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


💅🏻 *POSHLEEMAH*💅🏻


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)


*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*


QUOTE:-"und you was smiling. Live your life so that when you die, you’re the one smiling and everyone around you is crying."


9⃣ & 🔟

     Ranan Friday Dad din Leemah yazo Nigeria as promised, Mati ne yaje ya dauko shi a airport ya kawoshi gida, tana kwance a kan carpet din parlour din rungume da Teddy dinta amma ba barci take ba, jin alamun tsayuwar mota yasa ta tashi zaune tana tunanin waye yazo dan ita a sanin ta bata taba ganin wani yazo gidansu ba, bata gama tunani ba taji sallaman Dad dinta, tsayawa tayi tana kallonshi ba tareda ko ta motsa ba saboda tana tsoron taje ya kuma cemata shiba Dad dinta bane.


     Karaso wa yayi kusa da ita yana kallon ta yace "my beautiful princess won't u hug ur Dad", seda ta kalleshi tsaf sannan tace "u ar my Dad ryt", kallonta yayi yana tunanin kardai ace har ta manta shi, kada mata kai yayi azuwan eh ai kuwa ta dane kanshi tana murna duk tabi ta makalkale mishi wuya shikuwa se kokari yake yaga ta sakeshi amma abu ya gagara, ganin haka seya mike tareda ita yace mata " princess my neck", se a lokacin ta tuna ta sake shi tana dariya, Nanny ce ta fito tagansu murmushi tayi ta mishi sanda zuwa sannan tace "toh yau ga Dad dinki, yau dai za'ayi bacci cikin nutsuwa", kada kai tace " uhum", sannan Dad dinta ya shiga cike dauke da ita a hannu shi.



     Dakinshi ya shiga ya sauke ta kan gado sannan ya zauna ya riko hannunta yana kallonta, can kuma yace "princess ya jikin ki", tace " am fyn", yace "Nanny ta cemin kullum se kinyi kuka, kuma wai bakya cin abinci sosai,why", cikin sanyin murya tace " toh ba kai bane baka zuwa ba, baka sona, kullum en school dinmu parents dinsu ke kaisu su dawo dasu, amma ni kullum Mati ke kaini, kuma....", ganin ta fara kuka ne ya janyo ta jikinshi yana lallashi har tayi shiru sannan yace "princess amma ai kinsan ur Dad luv's u more anytin in dis world nd ur Dad is a busy man dats y bana samun zuwa, ai kema kinsani koh", kada mishi kai tayi yace " toh kinga reason dinda Dad dinki baya kaiki school kenan, amma yanzu zan dinga dawowa at d end of every month", tsalle tayi ta dane kan cinyarshi saboda murna tace "promise Dad", kai kadai ya kada mata saboda yasan ya fada ne kawai dan ya kwantar mata da hankali amma badan ze aikata ba.



     A ranan haka suka wuni tanata bashi lbrn school dinsu da wuraren da Nanny ke kaita, nan ta bashi lbrn sunje park kuma ta ganshi amma yace mata shi ba Dad dinta bane, tunani yakeyi indai tace ta ganshi toh ba makawa ta hadu da Al Hassan, nan dai ya share zancen yanajin shirmenta wani yayi dariya wani kuma ya bata amsa, amma duk sanda ya kalleta yana tausaya mata saboda rashin uwa ga rashin sannin danginta, sannan kuma tana tuna mishi cewar itace sanadin rabuwar shi da dangin shi duk da ba laifinta bane shiyasa yake bakin kokarin shi na ganin ya faranta mata rai.



     Da daddare da kyar ya samu ta kyaleshi taje ta kwanta har daki ya rakata seda ya tabbata tayi bacci sannan ya fito ya nufi dakinshi, wanka yayi ya hada coffee ya dauko laptop dinshi yana aiki, yana tsaka da aikinshi yaga Leemah tsaye a kanshi rungume da teddy dinta, murmushi ya mata yace "Princess it's midnyt me ya fito dake", tace " i want to sleep beside u", kallonta yayi yace "princess kinada rigima, toh zoki kwanta", daukan ta yayi ya kwantar kan gado ya zauna wurin har seda ta koma bacci sannan ya koma ya karasa aikinshi, kwanciya yayi a gefenta yaja musu comforter se bacci. Da asuba ya tashi sallah yaga Leemah kwance a jikinshi yace " Haleemah rigima", a hankali ya sauketa sannan ya tashi ya tafi masallaci, koda ya dawo bata tashi ba zama yayi yana kare mata kallo ba inda ta baro mahaifiyar ta komansu daya hatta baccin irin daya, nan take yaji wani tsanar Ni'ima ya darsu a ranshi na barin 'yarshi ta wahala saboda laifin da bata ji ba bata gani ba, kwanciya yayi amma  ba bacci yake ba se tunanin irin lyf din da yayi abaya, gashi yana son zuwa gida amma beda courage din sake tunkarar su, gashi fushi yake da Al Hassan saboda kin karban Leemah da baiyi ba, da haka ya ta tunani har gari ya waye sannan yasamu ya koma ya kwanta.



     Kwana uku Dad yayi yace ze koma ai Leemah ba karamin tashi hankalinta tashiga ba, rokon shi take tana dan Allah kar ya tafi ya barta, ko kuma su tafi tare amma ba yanda ya iya dole ya koma saboda leave din kwana uku ya karba, kuma in yace ze tafi da ita ba wanda ze kula da ita, ba dan yaso ba amma saboda ya zama mishi dole ya tafi ne in ba haka ba daya zauna, sosai ya tausaya mata saboda yadda take kukan, amma haka ya wuce bayan yayi lallashin ya gaji, Nanny ce taci gaba da lallashin ta amma Leemah takiyin shiru a haka ta wuni ranan suku suku, tun daga rana ta rayawa kanta cewar Dad dinta bayason ta ne kawai, da wannan tunanin taci gaba da living saboda haka zuciyarta ya riga ya mutu dan tana ganin bayan Nanny dinta bame sonta saboda haka a halin yanzu kowa haushin shi takeji da haka taji gaba da rayuwar ta har aka koma school, yanzu ma tafi da worst dan zata iya tun safe har dare kala bazata ce ba, koda Nanny take magana daga eh se a'a sekuma toh, sosai halin da ta shiga yake damun Nanny amma ba yadda ta iya haka ta kyale ta.



     Aryan tun daga ranan da yaga Leemah har yau be manta ba, kullum seyama Mom dinshi hiranta, haka in zai kwanta seya kalli hotonta har cewa Dad dinshi yayi a mishi babban frame din hoton da suka dauka tare a cewarsa ya samu er kanwa, Al Hassan ma ya kasa mantawa da Leemah dan har Yola yaje yace dan Allah suyi hakuri su bashi izini ya dauko Leemah ya kula da ita saboda da alama Al Hussain baya tare da ita kuma yarinyar tana bukatar kulawan iyaye amma Malam Maddo yace be yarda ba, ita dai Inna wuro ta fara saduda saboda tasan 'ya mace ce dole tana bukatar kulawa sosai amma tunda mijinta yace a'a toh bazata musa ba, haka Al Hassan ya dawo Abuja zuciyar cike da tunanin Leemah.


*FIVE YEARS LATER*


Manage dis, kafin in gani ko zan iya wani typing din zuwa yamma much luv😘 comment😎


_Mzz Daddy💋_

POSHLEEMAHTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon