Page 27 & 28

376 35 1
                                    

              Suna zuwa gida Leemah tayi wanka tayi sallah, tana cikin cin abinci wayanta ya fara ringing, ganin Aryan ne yasa ta dauka ta mishi sallama ya amsa tareda tambayan ta "ina kikaje da wannan classmate dinki din?", murmushi tayi a zuciyar ta tace Aryan badai kishi ba, tace bari na kala kular dashi, nan tace " cinema mukaje kallo,daga nan mukaje mukasha ice cream, muka kuma biya park mukayi wasa daga nan mukaje shopping daga nan......", bata karasa ba ya katse ta da "enough, enough ya isa haka, da kikasan kinason zuwa duka wa'annan guraren meyasa baki kirani ba? zaki bi wani daban", cikin fada fada yake maganan muryanshi na nuna alamun kishi, ita da kanta batasan haka zeyi fushi ba da batayi karya ba ta fada cewar cinema kawai sukaje kuma shima harda Zee amma ta makaro, bude baki tayi zata mai magana taji yace " kaina na ciwo gud nyt", kashe wayan yayi ita kuma ta tsaya tana kallon wayan gabadaya se taji tanajin haushin kanta saboda tabatawa Aryan rai, kiranshi tashiga yi amma baya dauka daga baya ma busy ya dinga dannan mata, gaba daya setaji abincin ya fita ranta, tashi tayi ta koma daki taci gaba da kira amma shiru ba amsa daga karshe ma kashe wayan yayi, nan hankalinta ya tashi ta shiga tura mishi message har bacci ya dauke ta, shikuma ba komai yasa ya mata haka ba se dan tasan cewar yana kishinta next tym ta gyara danshi har ga Allah Affan na tsone mishi ido dukda be taba ganin ta shiba.




            Da safe Aryan ya kunnan wayanshi nan ya dinga ganin messages na shigowa wayanshi, seda suka gama shigowa sannan ya fara karantawa duk hakuri take bashi da kuma alkawarin bazata sake ba, kiranta yayi aikuwa kaman dama jira take ta dauka tareda sa mishi kuka wai ya daina sonta tunda ze iya kashe wayanshi saboda bayaso ya mata magana, sosai hankalinshi ya tashi yace "No princess wlh Allah ban daina sonki ba, infact sonki kullum karuwa yake a zuciyata", tace " toh meyasa ka kashe wayanka?", nan ya rasa me zece mata can yace "battery dinne yayi rundown", shiru tayi dan tasan karya yake yace " kina gida ko kin wuce sch", tace "yanzu ma nakesa uniform, banyi ma breakfast tukun, se nan da 30min zan wuce", yace " ok, wait for me zan zo na kaiki", tace "okk",sannan suka kashe wayan, da sauri ya tashi ya canza kaya zuwa black t shirt da black jeans sannan ya dau makullin motarshi ya fito, Mom dinshi ya gani a parlour tana kallon early morning news tace " Baby ina zuwa da sassafen nan?, bayan afternoon lectures kake dashi", zuwa yayi ya zauna kusa da ita yace "morning mom", tace " morning, se ina", ya sosa kai yace "mom zanje na kai Leemah sch ne", mom tace " ohhhh, i can see my son is being a gentle man, i luv dat, yi sauri toh kar tayi latti",  yace "ok se na dawo", tace " a dawo lfy", fita yayi ya shiga motanshi Benz se gidansu Leemah, koda yaje bata gama break ba tare suka karasa amma Leemah taki yarda ta mishi magana se wani turo baki da takeyi ita ala dole tayi fushi, shikuwa murmushi kawai yakeyi dan yasan fushin Leemah bame dorewa bane, suna kaiwa bakin kofan sch ta bude motan zata fita yayi saurin riko hannunta ta juyo ba tareda tace komai ba yace "princess am sorry for nt picking any of ur calls, banson nayi maganan da ze bata miki raine saboda lokacin am boiling wit anger after knwin dat u went wit a guy other than me", kallonshi tayi tace " nd u decided to punish me by nt answering ur phone nd switching it off ryt", sosa kai yayi yace "am sorry, it won't repeat itself", kada mishi kai kawai tayi yace " kin hakura", tace "yes na hakura", yace " den smile for me", ai kuwa ta sake mishi tsadadden murmushin ta shima murmushin ya mayar mata sannan ya shafa kanta yace "Allah ya miki albarka", tace " aishhhh acting fatherly again", murmushi kawai ya mata yace "go inside, so u won't b late d assembly is abt to start", fita tayi sannan ta daga mishi hannu shima ya daga mata, seda yaga shigewan ta sannan ya juya kan motanshi ya wuce.



              Farouq zaune a dakinshi ya dauko notebook dinda Leemah ta mishi rashin mutunci a ciki dan har yau be yarba, saboda d more yake karanta wa d more yake jin son kara daukan revenge akanta, karantawa yakeyi amma ko gamawa beyi ba ya jefar gefe tareda rike kanshi saboda abusive words dinta tayi using, cikin bacin rai yace " Leeemahhhh, u will definitely pay for dis, dat i promise u", kaninshi ne ya shigo yace "Yaya lfy kake ihu, waye Leemah", kallon kanin nashi yayi yace " ihu nayi?", yaron ya kada mishi kai, yace "dawa dawa sukaji", yaron yace " ba kowa", yace "gud, je kayi wasa wanka zanyi", tashi yayi ta shiga bathroom dinshi ba dadewa ya fito ya shirya sannan ya dau takardar yasa a drawer ya dau mukullin motanshi yayi waje, seda yaje ya gaida iyayenshi sannan ya fita zuwa school dan karfe goma yakeda lectures.




            Affan da Zee ne zaune gaban Leemah se tambayan ta sukeyi waye wannan wanda ya kawo ta sch  amma shiru ba amsa sema dora kanta da tayi kan slate dinta dan batason tambaya, Zee ce tasa baki tace " cmon Leemah spill it out, we ar ur frnds ryt", dagowa tayi tace "he's my cousin", Zee tace " wow, so u hav a cousin, bt u've neva told us abt him, i bet his handsome just lyk u ar beautiful", kallonta Leemah takeyi baki sake shikuwa Affan be yarda da abunda Leemah tace ba amma haka yayi shiru, ita kuwa Leemah ji take kaman ta make Zee saboda tana koda saurayin ta. Class teacher dinsu ne ya shigo yana mikawa kuwa jamb form dinshi wanda date da center duka ke ciki, Leemah da Affan suna cikin en first batch kuma center dinsu daya amma ba rana daya zasuyi ba, Leemah zata riga Affan yi, Zee kuma tana cikin en third batch kuma center dinta daban, Leemah ganin saura sati daya nasu yasa tace "i think i hav to start studying", Zee tace " wat, u don't hav to study for jamb, cus jamb is just gambling, just try ur luck, u can read almost every page in every textbook bt at d end of d day u will end up scoring low mark nd those dat didn't read at all will end up getting d high mark so i don't read for jamb its just a waste of tym", Affan yace "i agree wit u Zee", Leemah tace " dats wat u guys think, bt as for me am gonna study hard", Zee tace "suit ur self", Affan yace " will study wit u", kai kawai ta daga mishi saboda tana tsoron sake batawa Aryan rai.


         Manage dis fans, got a lot of stuff to attend to.

        Don't forget to share, comment, nd vote, vote, vote


Luv yah😘

Poshleemah

Mzzdaddy💋

POSHLEEMAHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang