Page 87 & 89

911 34 10
                                    

              Washegari da safe na koma dan dauko rahoto na kuwa samu kofan a bude, Leemah ce kwance cikin bargo banda kuka ba abinda takeyi Aryan kuwa ya rike kai da hannu bibbiyu ya rasa me zaiyi dan yayi lallashin amma kaman kara tunzurata yakeyi, wayanshi ya dauka ya kira Dr Zynah yace dan Allah tazo emergency, cikin kankanin lokaci tazo bude mata kofa Aryan yayi ta shigo tana tambayarshi lfy, sosa kai yayi yace "gaskiya ba lfy",  tace " meyafaru?", beyi magana ba se leading dinta da yayi zuwa dakinshi, ganin Leemah a kwance ga stain a kan gado yasa ta gane wainar da aka toya, murmushi tayi ta mishi alama da yaje waje ya fita ya basu wuri ita kuma ta shiga bathroom ta hada mata ruwan dumi ta fito tace "Leemah kukan ya isa a haka, ko wace macce fa dole ne tayi passing through dis stage, so stop crying , anyi na farko the rest won't hurt", shiru Leemah tayi da taimakon Zynah ta gasa jikinta ta fito ta shirya tayi sallah sannan Aryan ya hada mata tea tasha, tasha magani se bacci.



          Suna zaune parlour shida Zynah tace " da alama Leemah nada shegen raki, take it slow ok her next time", murmushi yayi ya sunkuyar da kai dan kunyarta ma yakeji, sallama sukaji Shamsiyya ce ta shigo ta kawo abinci, Zynah kuma ta musu sallama ta wuce gidanta, Leemah na tashi taji ta warke ba kaman da safe ba, kasa ta sauko Aryan maganan duniyan nan ya mata amma ko kallonshi ba tayi banda harara ba abinda take aika mai shi har dariya ma take bashi, abinci taci ta koma daki tayi sallah La'asar tana idarwa taji ana danna door bell, ko kafin ta sauko Aryan ya bude Zynah ce tazo duba lafiyan Leemah, Leemah na saukowa Aryan ya basu wuri ta tambaye ta jikinta Leemah tace "da sauki", sannan suka fara hira bata jima ba tace ita zata tafi, har bakin gate Leemah ta rakata inda suka sake ganin Shamsiyya ta kawo abinci Leemah tace " Shamsiyya shiga ciki ina zuwa", tana wucewa Zynah tace "niko Leemah har yanzu baki fara girki bane?", shiru tayi kaman bazatayi magana se kuma tace " girkin ne ban iya ba", Zynah ta jinjina kai tace "baki iya ba", Leemah tace " eh, a gidanmu bame koya min sedai a dafa naci", "toh kinada sha'awar koya", Zynah ta tambaya tace " inamaso nayi enrolling a catering school ", murmushi Zynah tayi tace " kije ki tambaye mijinki in zai yarda zan dinga koya miki, duk abinda yace ki kirani a waya ki fadamun", dadi sosai Leemah taji harda rungumeta sannan sukayi sallama ta wuce Leemah kuma ta shiga gida.





       Koda ta shiga parlour Aryan da Shamsiyya ta hango a dinning saboda haka ta karasa wurin su itama ta zauna Aryan se kallon ta yakeyi ita kuwa ta dauke kai, tunawa da tayi zata tambayeshi permission na koyan girki wurin Zynah yasa ta juyo tace "dama akwai maganan da zamuyi", yace " ina jinki saurauniyar kuka", shareshi tayi tace "zan fara koyan girki wurin Dr Zynah meka gani", murmushi yayi yace " Good idea, Allah ya bada sa'a", tace "ameen", sannan ta dau wayanta ta kirata ta tagaya mata ya yarda saboda haka gobe zasu fara.



         Washegari Leemah ta soma koyan girki ba laifi tana kokari saboda she's determined to learn, a kwana a tashi ba wuya cikin wata daya Leemah ta iya African dishes dayawa wanda tanayi a gida kuma Aryan naci har yata santi, itakuma dadi takeji intaga yana santi, suna waya da Dad dinta amma har yanzu bataba mahaifiyar ta wannan daman ba, Aryan yanaso Leemah ta koma school amma tace ita ta daina ya bude mata shopping mall kawai wanda haka kuwa akayi, Affan da Zee se abinda yaci gaba dan yanzu iyayensu ma sunsan da zamansu, bangaren Dr Farouq saura wata biyar a fito da shi amma ji yake kaman shekara biyar, shikuwa Dr Sudais ba'a ma magananshi dan nashi da saura sosai.



       BAYAN WATA UKU

     Yau Leemah ta tashi da zazzabi wanda yasa hankalin Aryan tashi ba yanda beyi da ita ba akan suje hospital amma ta kiya gashi bata iya cin abinci, ko ruwa tasha seya dawo, kwatakwata bataso Aryan yazo kusa da ita wai turarenshi na sata amai, gashi Dr Zynah nada appointment a hospital dole su jira ta dawo tunda tace bazata hospital ba, haka yasa ta gaba se kallonta yakeyi duk ta gallabaita ta fita hayyacinta kaman ba itaba. Waya ya kara dauka ya kira Zynah wanda wannan lokacin ya samu ta dauka ba secretary dinta bace saboda haka ya shaida mata halin da ake ciki tace ya bata 30mins gata zuwa. Cikin minti talatin ta karaso, ko ita yadda taga Leemah ta zabge lokaci daya ya bata tsoro dama gata abu ba jiki ba, nan da nan ta shiga gwada ta wanda gwajin farko ya shaida mata da tana dauke da ciki ne na wata biyu da sati daya, murmushi tayi bayan taba Leemah magani ta mata alluran bacci sannan ta fita wurin Aryan wanda keda pacing a corridor din wurin tace "albishirinka", murmushi yayi dan shima yasan abinda zatace seyaci " goro", tace "Leemah na dauke da ciki har na tsawon wata biyu da sati daya", dadi kaman ya kashe shi he's gonna be a father soon, kallon Zynah yayi cikin jindadi yace " kinada tukwaicin albishir ina zuwa", dakin shi ya shiga ya fito da roba wanda dabinon ne a ciki me danko ya bata tareda cewa "for now abinda nake dashi kenan", murmushi tayi tace " na gode ", yace " ai nine da godiya, zan iya zuwa ganin ta", tace "kashiga amma tana bacci", kai kawai ya kada tareda shiga dakin itakuma tayi murmushi ta wuce dan mijinta ya kusa dawowa gida.



POSHLEEMAHHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin