Page 59 & 60

278 25 7
                                    

         Sun sauka garin Dubai lfy, waje suka fito suna jiran taxi da ze kaisu hotel dinda zasu sauka, Aryan ne ya hango wani kaman Dad din shi an bude mai mota ze shiga, Da sauri ya nunawa Dad dinshi amma kafin su karasa har anja motan saboda haka da suka samu taxi sukace yabi motan, Dad din Leemah gida yaje yana shiga ko zama beyi ba gateman dinshi yazo ya fada mai ana nemanshi, mamakin wake nemanshi yakeyi dan yasan basuyi da wani cewar zezo ba amma haka yace a shigo dashi, haurawa sama yayi dan ya canza kaya, su Leemah kuwa tun daga waje take kallon gidan azuciyar ta tace "dama nan Dad yake, ai dole ya dinga mantawa da ita", shiga sukayi suka zauna inda parlour hotunan Leemah ne a jikin bango sekuma guda daya na wata mata balarabiya, kamshin turaren Dad dinta taji ta daga kai ta kalleshi yana saukowa.


      Seda yazo tsakiyan parlour sannan ya dago kai sosai yayi mamakin ganin Al Hassan da family dinshi ga kuma Leemah kan wheelchair, gabadaya hankalinshi ya koma kanta itakuwa wani kallon tsana takemai ji take inama bashi ya haifeta dan bataga abunda zatayi da uban da bayajin maganan iyayenshi, muryan Al Hassan ya katse musu tunaninsu yace " zo ka zauna muyi magana", be kula Al Hassan ba saboda har yanzu yanada cikinshi Leemah ya kalla yace "meyasa meki haka", shiru ba amsa, ya kara maimaitawa nan ma shiru, Al Hassan ne yace " hatsari tayi", dukawa yayi gaban Leemah ya riko hannunta yace "princess meyasa meki", tace " accident nayi", "garin yaya", kallonshi tayi ta kwace hannunta sannan tace " none of ur business", kallon Al Hassan tayi tace "Dad mu wuce inaso na kwanta", kallon Aryan yayi yace " kuje da ita kamana booking daki, in na gama zanzo", da sauri Al Hussain yace "ina zata bayan tazo gidan mahaifinta, ko tanada gidan da yafi wannan ne", hawaye ne ya zubo mata ba tareda ta kalleshi ba tace " da in zauna da mazinaci gwara na kwana a titi", runtse ido Dad yayi danji yayi kaman ta buga mishi kutsa a kirji ne.



       Shiru yayi bece komai ba dan a halin yanzu beda abunda ze cemata dan yasan ba kulashi zatayi ba saboda da an kalla idonta ansan tana cikin bacin rai, fita da ita Aryan yayi suka samu taxi ya kaisu hotel sukayi booking daki, shikuwa Dad kasa tabka komai se tunanin kalaman Leemah yakeyi a zuciyarshi yace "lallai abunda ya shuka ne yake girba", Al Hassan yace mai "ka zauna muyi magana ta fahimta", zama yayi kanshi na sara mishi sannan Al Hassan yace " mungode Allah da ya nuna mana wannan ranan wanda Family dinmu suka hada kansu har Abba ya yafe maka kuma ya karbi Haleemah", shiru ne ya biyo baya sannan daga bisani Al Hussain yace "a ina kuka ganta kuma ya akayi tasan yadda aka sameta", murmushi Al Hassan yayi sannan ya fara bashi lbrn haduwar Aryan da Leemah har zuwa sanda Aryan ya kawota gida da hatsarin da tayi da yadda akayi kafanta ya mutu dakuma zuwansu yola da yadda sukayi da Mallam Maddo har zuwa sakon da Mallam Maddo ya bashi na ya fada mai lokaci yayi daya kamata ya dawo gida ya daina fushin da yakeyi.



      Hawaye Al Hussain yakeyi dan shi duk ba wannan ya dameshi ba yadda zema Leemah bayanin haihuwarta ne ke damunshi, dan dama guilty ne yake hanashi zama wurinta dan tana tuno mishi da mummunan abunda ya aikata shekarun baya kuma bayaso ta sani shiyasa beyi gigin sake komawa wurinsu Mallam Maddo ba toh gashi daga tafiya course din wata biyar har abunda yake tsoron faruwar shi ya faru ya kare, jin an dafa mai kafada ne yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya tafi Al Hassan yace " yanzu ba lokacin tunani bane, abunda ze faru ya riga ya faru saboda haka tashi zakayi munemawa Haleemah lafiya sannan ka nemi yafiyarta a wuce wurin, ka manta da past life dinka, Allah ya riga ya kaddara abunda ze sameka kenan kuma ya kaddara ta hanyar da zaka samu Haleemah kenan shiyasa kaga hakan ta faru, saboda haka ka sawa kanka salama ka rungumi kaddaran da  Allah ya daura ma, nasan yanzu Haleemah tana fushi da kai amma nan gaba zata sauko", numfashi Al Hussain ya sauke yace "Tnx bro", murmushi Al Hassan yayi yace " it's been long since u called me bro", itadai Mom tana zaune tana kallonsu tana murmushi.

U guys should manage dis yau da ciwon kai na tashi, saboda ban muku typing jiya bane yasa nace bari na muku koda kadan ne.

Don't forget to comment,share and vote.


Luv yah😘



Poshleemah




Mzzdaddy💋

POSHLEEMAHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang