🌸🌺 FABEELAH 🌺🌸
🌺🌸 🌸🌺0️⃣9️⃣ - 1️⃣0️⃣
Haiam ceh ta shigo tana murmushi ""Bestie yane ta fada tareda qarasowa inda fadeelan take nan fadeela itama ta maida mata da murmushi amma batace komai ba""wai fadeela meke damunki naga tunda kikazo gidanmu bakya wani sakewa sosai ""daria fadeela tayi kafin tace ""wallahi ba komai bane kawai de ina missing yaya nane kinsan tunda na tashi ina yarinya har nakai i yanzu ban taba rabuwa dashi ba ""yanzu idan kikayi aure kuma ya zakiyi ai dole ki rabu dashi "cab aini aure ba yanzu ba sai nan gaba ...keda kikaga zaki iya saide ince Allah ya baku zaman lapiy..."hayam ceh ta katse ta da cewa ke kuwa fadeela kinada ma saurayi kuwa ta fada tana kallon fadeelan dake qoqarin cire kaya zata shiga toilet amma saita fasa .."inada saurayi mana amma wallahi haiam ba sonsa nakeba kawai yaya nane ya zaba minshi kuma kinsan bana iya yiwa yaya musu ta fada cikin ban tausayi ""kiyi hakuri fadeela insha Allah yaya bazai miki zabin tumun dare ba insha Allah ma shine Alkhairi a gareki ta fada tana dafa kafadarta,,,haka suka cigaba da hirarsu abin ban sha'awa daga qarshe fadeela ta tashi ta shiga toilet domin wanka sabida yanzu za'azo musu makeup
A bangaren mommyn Imam kuwa tunda sukazo ake haba haba da ita sbd duk cikinsu ba Wanda yakai mijinta arziki ""suna zaune a parlor gabaki dayansu Ana ta hira""wasu suka shigo su hudu ""wata hadaddiyar budurwa na hango a gefensu tanata faman shan qanshi ""mommyn Imam ceh ta tashi ta nufi wajen daya daga cikinsu Wanda kana ganinta kasan itace babar yarinyar,,matar ta hadu iya haduwa kana ganinta kasan kudi sun zauna,,tarbarsu aka shiga yi inda naji matar tana kirar burwar da suna Zahra bakiga mutane ba ..bazaki gaishe suba nanta fara gaidasu tana murmushi Wanda ya baiyyana dimple dinta ya fito ""haka aka zauna Ana hira cikin aminci inda ""Ammi wai Ina sis haiam neh naga har yanzu ban ganta ba ta fada tana kallon Side dinda step yake """daskarewa tayi ta kasa motsi ganin Imam ya taho ta bude baki tana kallon shi ,,ya lura da kallon da take mishi don haka ya hade rai sosai ""Imam bakaga su Ammi ba 'bazaka gaishe suba nan ya qaraso ya durkusa har kasa ya gaishe su sannan ya miqe ya nufi wajen baban zahra ya gaishe shi cikeda Fara'a ya amsa mishi har Imam ya bace zahra bata bar kallonsa ba ""Ammi wannan waye please ta fada tana kallon ammin
""Dan gidan Hajiya Fateema neh meya faru ""no ammi ba komai kawai de na tambaya neh ,daga nan taja bakinta tayi shiru tana ta sake sake a zuciyarta (toh fah wannan shi ake kira love at first sight)Tun daga time din zahra ta kasa sukuni har mommyn su fadeela ta kira wata mai aiki ta rama zahra wajensu haiam a part dinsu,,,nan suka tapi tana tape tanata waiwaye ko Allah zaisa taga Imam amma Sam bata ganshi ba haka ranta ba dadi ta qarasa wajen su fadeela,,nokin ta shiga yi da qarfi kamar zata cire door din....budewa aka zo aka yi ..fadeela ceh cikin wani gown pink color yayi fitting dinta sosai hips dinta ya bayyana ba karya ni kaina Dana ganta na zaci itace amaryar dukda ba'a fara mata makeup ba haiam ake yiwa yanzu shiyasa ita ta taso ta bude door din..a yamutse take kallonta sannan ta fadeela ta bata hanya ta shige ""Amarya kinsha qanshi ta fada tareda qarasawa cikin room din,,jin muryar zahran ne yasa haiam ta dakatar dame makeup ta tashi da hanzari sukayi hugging juna cike da murna sosai a fuskokinsu ""amma haiam bakida mutunci yanzu ace ni Ina yar uwarki shine zafi fi fita bare akaina ai yaci ace dani za'ai komai kuma ma in tamabayeki wace waccen yarinyar data budemin door ta fada tare da ture haiam din tana juyawa ko zata ga fadeela,,,haba zahra mene hakan dan Allah kinsan wace fadeela kuwa ?bestfriend ditace fa tun muna yara and kuma da kike cewa na fifita bare akanki ai tuni na kira amminki a waya nace mata kizo za'a fara biki tacemin kince bakida time yanzu amma shine ke kikeda bakin magana ta fada tare da juyawa wajen me makeup din da zauna a kan kujera ...maganganun zahra sunyiwa fadeela zafi amma dayake bamaison rigima bace kawai ta share kamar batasan me sukeyi ba da nufi gaban mirror tana taje gashinta mai tsayin gaske daya biyo bayanta ""haka suka zauna zahra itade da haiam kawai take magana don farkon ganinta da fadeela taji ta tsaneta tsana mai tsanani
Haka mai makeup tayi musu makeup su uku inda fadeela ba qaramin kyau tayiba kowa ya ganta saiyace masha Allah dukda daman tuncan da mai kyau ce ita na ajin farko ,,idan banda kayan amarya datasa Ana gani mai tsada neh da cewa zakayi fadeela ceh amarya dukda makeup dinma dakyar ta bari aka matashi badan tasoba haiam ta uzzura mata amma idanka kalleta sau daya saika sake kallon ta ""haiam ceh cikin wata gown white me mugun kyau da sheqi an saka mata hular queen akanta an fito mata da gashinta an tafkeshi da sama tayi kyau sosai ta saka hill shoe ""fadeela kuma pink din gown ta saka Wanda yabi jikinta sosai dukda kunyar da takeji haka ta hakura ta fito dashi sabida takurawar da haiam ta mata akan saita sakashi wai yafi yimata kyau ,,hill shoe neh a qafarta me kyau sosai sannan tadan ratayo wani qaramin jaka sannan aka gyara mata gashinta yazo har baya
""Zahra kuma cikin wata yellow din gown da hill shoe black sai black din pours data rike itama tayi kyau sosai...haka suka jero abin sha'awa amma idan zahra taga fadeela wani abune yake tsaya mata arai amma haka ta daure suka qaraso inda friends din amarya suke anata musu pictures.SUMIE London 💄👛