🌸🌺 FABEELAH 🌺🌸
🌺🌸 🌸🌺
3️⃣9️⃣-4️⃣0️⃣
Tapiya yake yana tangal tangal kamar zai fadi sabida tsabar azabar da zuciyarsa take masa,dakyar ya karasa daki yana shiga,fridge ya bude sannan ya dauko ruwa mai sanyi ya fara sha jin zuciyar tashi taki tayi sanyi yasa ya fara kwara ruwan har kansa,jefar da roba din yayi ya nufi kan gado ya fada yanata zan numfashi da qarfi ,mesa mommy zata mishi haka kode bata cikin hayyacin tane,kode wasa take mishi,noo wannan ba wasa bane,ya bama kanshi amsa,amma kuwa inde da gaske ya zama dole ya koyama zahra hankali,koda kuwa an aura mishi ita bazata taba ganin sakin fuska daga gareshi ba,saita gwammace kida da karatu,abubuwan mugunta kala kala yake tsarawa a ranshi,wasu hawayene masu zafi suka fara gangarowa daga idanunsa daya tuno da fabeelah,bazaiyu ba wallahi bazaiyuba yake fada har maganar ta fito fili,qofar dakin aka turo,da jajayen idanuwan shi ya dago yana kallonta,itama kallon nasa take a hankali take takowa harta karaso inda yake,ba karamin tausaya mishi tayi ba ganin yanayin da yake ciki,zama tayi gefensa sannan ta kamo duka sannayensa tace "Imam please ka dena saka kanka cikin damuwa ,a Gaskia nasan koni akayiwa haka bazanji dadi ba Amman dai please be strong,zahra bata kyauta ba nina sani ,amma ka daure kabi umarnin mommy,insha Allah hakan shiyafi Alkhairi a gareku gabaki daya ,wani murmushin takaici yayi sannan yace "haiam wallahi tallahi bana son Zahra ko kadan,nayi nadamar biyo mommy bikinnan,da nasan hakane zai faru wallahi bazanzo ba,wallahi sai zahra tayi nadamar aurena da zatayi,wannan wani irin bala'i neh, kawai saiya kife kai a cikin Fillo,sannan ya sake dagowa yace "haiam inada wanda nakeso a yanzu ,ni kaina a da bansan soba sai a kanta,Ina sonta so mai tsanani, shiru tayi tana kallonsa yadda duk ya zuge lokaci daya idanunsa sun kada sunyi ja, sannan tace "Imam why not bazaka samu mommy ku zauna kuyi magana cikin nutsuwa ba ka fada mata kanada wanda kakeso,amma dai baka riga ka mata promise zaka aureta ba,ta tambayesa, "ban mata na haiam ,in fact batasan ina sonta ba ,da mamaki take kallonsa sannan tace, "toh fah yanzu toh ka sameta ka mata magana duk yadda kukayi ka sanar dani ,i promise to help you , "kinsan wacece kuwa , A'a ta bashi amsa "Fabeelah friend dinki haiam fabeelah nakeso,kuma ita nakeso in aura, "a firgice ta dago tana kallonsa sannan tace FABEELAH fa kace Imam,kaima kasan hakan bazai yuba,kalli abinda zahra ta mata tun yanzu akanka bare ace kana sonta,kalli ansan zahra bata kyauta ba amma da akazo sulhu sai aka share zancen aka bige da zancen bikinku,ka lura da irin kallon da mommyn ka take mata fah ,haka Imam ka rufa mata asiri mana dan Allah ,I know kuma fabee Gaskia tanada wanda take so ,kuma ba kowa bane inba Moha ba friend dinka,ta fadamin shi takeso shi zata aur...wani tsawa ya daka mata da yasa taja bakinta tayi shiru "Ina ruwana da rashin sonta da basa yi,su zata aura koni zata aura,kuma da kike ikirarin moha na sonta ai ba Wanda ya sani,ko rana ba'a saka musu ba ,inde Ina raye to wallahi saina auri fabeela ki rubuta ki ajiye ni Abbakar imam saina auri fabeela,inasonta haiam ,sai kuma ya matso kusa da ita tareda dafa cinyar ta ,please help me don Allah badan niba ,batace komai ba ta mike ta fice a dakin cike da tausayin sa,ganin ta fitane yasa ya koma ya kwanta nan take zazzabi mai mugun zafi ya rufesa
Tunda ta shiga daki ta bude drawer ta shiga fitoda kayanta Tana sakawa a cikin akwatin data taho dashi,tana cikin hakanne taji haiam ta shiga, "fabeela me nake gani haka ,Ina zakije kuma ,bata kalleta ba ta cigaba dasa Kayan sannan ta dago tace "haiam zan tafi garinmu,zan koma gidanmu,zan koma wajen yayana,haiam zuwana gidannan naku ba Alkhairi bane ,don Allah karki hanani tapiya ta qarashe maganar cikin rawar murya sannan ta zube a wajen tana sharar kwalla, "ohh ni haiam na shiga uku,dan Allah ina kukeso insa kaina,ga imam can yanzu yana cikin wani hali,gashi kema haka ,fabee please stay with us har a gama biki mana ,please don't leave ,I promise ba abinda zai sake faruwa dan Allah ,ta fada tareda rungume ta itama Tana hawaye,fabee i want us to talk about something if you are free ta fada , tashi tayi tana share hawaye sannan tace Ina jinki ,fabee do you have a boyfriend? I mean Wanda kikeso ki aure,let's talk in a serious turn please,I'm not here for kidding, kamar ya ta tambayeta,yes fabee inaso ki fadamin gaskia please, "inada shi haiam amma inajin tsoron ko parent dinsa zasu bari ya aureni, wayeshi? "Moha mana i think i already tell you, hmm tace sannan tace "fabee can you please forget about that moha,I've someone special for you,kuma yanada hankali ya hadu sosai please kimin promise zaki soshi,da sauri ta zare hannayenta daga cikin nata ta mike Tana cewa "haiam what do you mean,are you telling me to break up with moha,no bazan iyaba haiam ,bakya ganin irin sonda moha kemin,yanzu idanna rabu dashi aina yaudaresa,idan kikaga na rabuda moha toh shine yace baya sona,ganin yadda take ta balbala masifa neh yasa haiam taja bakinta tayi shiru sannan tace mata idanta sauko sayi magana