Part 19

57 3 0
                                    

🌸🌺 FABEELAH 🌺🌸
🌺🌸                     🌸🌺


   
          

             3️⃣5️⃣-3️⃣6️⃣





       Tunda safe Abban zahra yaje ya samu baban haiam da zance wani kallo ya watsa mishi sannan yace..."inace nan gidanane koh,,toh bazan koreta ba kuma fabeelah yanzu ta fara zama ...haba Alhaji ya kake abu kamar qaramin yaro...akan wannan yarinyar shine kake cewa zaka wulakanta Wani dan Adam toh wallahi kaji na rantse baza'a koreta ba ,me yarinyar nan ta tare muku ne da kuka sata a gaba haka,ita ba shiga harkar kowa take a gidannan ba sannan kuma ita bata damu daku ba amma ku kun damu da ita,nan Baban haiam yayita masifa har saida ran abban zahra ya fara baci kafin daga baya ya mike ya fice daga part din cikin fushi,a bakin qofa kuwa zahra ceh jikinta sai rawa yake jin ance baza'a kori fabeelah ba dakyar ta iya Jan jiki kafin Abban nata ya fito harta bar wajen tayi bangaren da suke Tana zuwa ta fada akan gado zuciyar ta na mata zafi,tunda de baza'a kori fabeelah ba toh ita saita koya mata hankali yanzu yanzun nan wallahi,huci take kamar mayunwacin zaki ,a zafafe ta tashi ta nufi room din fabeelahn tana zuwa kuwa tayi sa'a kofar a bude take ,da karfi ta tura kofar ,lokacin fabeelah ta fito daga wanka da towel a jikinta tayi daure qirji, haiam kuma na zaune gaban mirror tana kallon kanta,ganin an bugo kofa da karfi yasa dukansu a tsorace suka juyo,zahra suka gani tayo gadan gadan kan fabeelah tana kutuntuma mata ashar "ke dan uwarki dawa kike,wallahi bari kiji baki isa kiyi takara dani ba kuma wallahi yau saikin gane kuranki, da baya da baya take ja tana girgiza kai alamar A'a bakinta sai rawa yake da kyar ta iya furta "mm mme na miki...a zuciye tayi kanta ta tsinka mata mari sannan ta fara dukanta har towel din jikinta na shirin kunce wa kasa tayi tana ihu..ganin haka neh haiam tayi kanta itama ta tsinka wa zahra mari guda biyu lafiyayyu Tana huci tace "ke wallahi zahra ki shiga hankalinki idan zakiyiwa kowa na kyaleki baki isa kiyima fabeelah ba,haukane yake damunki ko meh...dafe kuncin ta tayi Tana kallon haiam tare da kan kance ido "ni kika mara akan wannan ballagazar,har kike cemin mahaukaciya..."an gaya miki din me kika isa kiyi haiam ta fada tareda matsowa Tana nunata da yatsa..cikin fushi zahra ta buge ta sannan ta wuce Tana cewa...barina nuna miki haukan yanzu yanzun nan ta fice daga dakin...tsaki haiam tayi sannan tayi kan fabeelah dake durkushe Tana kuka Tana fadin haiam yau wallahi gidanku zan bari bazan iyaba mena mata dan Allah ta takura min haka ..."please fabee ki daina fadan haka wallahi bazata kara ba ,ai na rama miki,kafin su rufe baki sukaji an sake banko kofarda karfi,juyowan da zasuyi sukaga zahra rike da wuka a hannunta tana huci tana cewa "yau zan nuna muku ni mahaukaciyar gaske ce,kansu tayi da wukar,kokawa suka shigayi da haiam sosai ihu haiam ta saki lokacin da zahra ta yanke ta a  hannu fabeela na ganin  haka ta tashi tayi hanyar waje da gudu amma ina zahra ta qaraso inda take,bayanta ta yanka da wuqa sosai wukar ta shigar mata jiki,wani irin qara sannan ta fadi qasa sumammiya jini nabin jinka,da gudu haiam ta tashi ta fita,lokacin Imam ya fito zaije wajen mommynsa ,karo sukaci,da sauri ya Riko ta yana fadin "ke meya faru neh bakya ganin gabanki neh,ganin hawaye a idonta neh ya sashi qara tambayan ta,wai mene kik...ganin jinin dake bin hannunta neh ya zare ido cikeda firgici yace "meya sameki a hannu haiam kalli yanda hannunki yake jini fah,dakyar ta iya nuna hanyar room din,baki na rawa tace "uhmm uhmm fa fa fabeelah,zata kashe ta Imam ka taimaka min ,amana bro dinta ya bani,ta fada tana yarfe wannu,tsayawa yayi yana kallonta ganin bai gane me take nufi bane yasa taja hannunsa da gudu sukayi dakin..suna shiga daide lokacin da zahra ta daga wuka zata soka mata ..wani kukan kura yayi ya yagota ya jefar,da qarfi ya shiga bugunta tun tana ihu harta gaza,saida yaga ta kasa motsi sannan ya juya kan fabeelahn dake kwance a kasa jini na zuba ta bayanta kamar an yanka dabba,da sauri ya debe ta yayi qasa da ita haiam na binsu a baya itama hannun nata jini yake,suna zuwa daide kan step sukaga su mommy suma suna qoqarin hawa saman sanadiyar hayaniyar da sukaji a saman ganin jini a jikinsu gabaki daya yasa duka suka tsaya suna kallonsu cike da tsoro dason tambayan ya akai,ko kulasu Imam baiyi ba ya ra'ba ta gefensu ya wuce haiam na biye dashi ko dankwali bata saka ba,mota ya bude ya sakata a ciki sannan ya shiga shima haiam kuma ta shiga baya yaja motar suka fita da gudu kamar zasu tashi sama...su mommy kuwa kowa ya kasa magana a cikinsu sai kawai suka juya,ihun zahra sukaji daga sama dayaja hankalinsu gabaki daya suna isa dakin suka sameta duk fuskarta a kumbure kamar wanda tayi fada da kura,da gudu suka karasa kanta suna tambayanta ...batace musu komai ba don gani take idanta fadi abinda ya faru to tabbas yauta mutu a hannun Ammin ta,,hawayene kawai yake tsiyaya a idonta ta kasa magana ,mommy ceh da Maman haiam suka taimaka mata suka dagata aka nufi da ita cikin mota,hospital aka nufi da ita,Amminta kuwa tunda suka tapi dakin taganta a halinda take ciki a ranta taji ba dadi amma a fili ta nuna bata damuba,ko hospital bata rakasu ba dan tasan kome ya faru laifinta neh sai an dawo an zauna za'aji komai


   
       Tunda suka isa likitoci suka rufa a kanta ,duk abinda ya kamata a mata an mata har suka tabbatar ta dawo hayyacinta sannan aka mata alluran bacci,itama haiam an gyara mata hannunta ,itade burinta kawai taga halinda bestyn nata ke ciki,doctor ne ya fito yace su biyoshi,suna isa office ya fara musu bayani "a gaskia ciwonnan ya shigeta sosai sabida haka sai tayi kwana 2 a hospital kafin za'a sallame ku,kuma dadin dadawa jininta yahau kadan sanadiyar bugawan da gabanta yayi da qarfi,a razame haiam ta dago tana kallonsa idonta cike da kwalla sannan tace "na shiga ukuna ni hayyuma yazanyi tareda daura hannayenta biyu akanta,wallahi sainayi maganin zahra,wallahi bazan qyaleta ba ,Imam kalli abinda tajama yar mutane fah,wannan de biki nawa baizo da Alkhairi ba wallahi,tunda yarinyar nan tazo kowa yasa mata ido, hankalinta ta dawo dashi kan doctor sannan tace "yanzu ya jikin nata doctor hope she's getting better? ...murmushi yayi sannan yace...,"don't worry dear she will get well very soon,shikam Imam kasa magana yayi yana tunanin wannan wani irin rashin hankali neh zahra keda shi,me yarinyar mutane ta mata da har ta dace da wannan hukuncin,lallai kuwa zai taka mata birki akan fabeelan inba haka ba kuwa saiya mata abinda bata taba zata ba, "doctor how can we see her please.."she's getting rest now buh you guys can go, da sauri ta mike shima Imam yabi bayanta suka nufi room dinda fabeelah ke ciki,baccinta take amma kaida gani kasan bana dadi bane ,da sauri haiam ta qarasa kusa da ita sannan ta shafa fuskarta,hawaye nabin kumatun ta tace "please bestie get well very soon..shima Imam kallonta ya tsayayi yana kallon yanda tayi haske tayi kyau sosai ba kamar farko daya ganta ba ,aji yar zuciya ya sauke sannan yace "haiam zaki iya tapiya gida sabida anjima kunada event "no wallahi bazan iyaba Imam just leave me here,i'll surely take care of her,,da mamaki yake kallonta yadda ta marairaice kamar zatayi kuka yana tunanin wannan wani irin sone haiam kema fabeelah,Ana bikinta amma akan kawarta ba lapiya zatace bazata koma ba ,..."haiam mana please get up and go,i promise to take care of her..,"no please ta fada Tana kallonsa,,shiru sukayi duka kafin daga baya yace kawai suyi waya a turo yar aiki sai suje gida ta dauki excuse a wajen su dady,haka kuwa akayi..,lokacin da suka isa gida ba kowa su dady ma basa nan gabaki daya,,,su mommy kuma sun tapi kai zahra hospital...ganin ba kowa gidanne yasa dukansu suka zauna a Parlour wanda ba mutane a ciki,takowar mutum sukaji,Ammin zahra ceh ta shigo tana tambayan su yame jiki "da sauki duka suka answer mata sannan tace su fada mata meke faruwa...kin fada mata suka ,sukace mata tayi hakuri sai an zauna gabaki daya sannan zasuyi bayani,,,bata musa musu ba haka ta kyalesu sannan haiam ta mike ta shiga kitchen tasa masu aiki su hadama fabeelah ruwan tea a flask da kuma abincin da zataci sabida yanzu suke so su koma hospital din ,ba'a dade ba suka gama komai suka kawo,sannan tayi musu umarni da sukai abincin cikin mota gasunan zuwa

Sumie London 💄👛

FABEELAHWhere stories live. Discover now