🌸🌺 *FABEELAH* 🌺🌸
🌺🌸 🌸🌺*RIJF Dad, InshaAllah you are in a better place 🙏🏻😢 May your gentle soul rest in perfect peace😭💔*
*Wattpad:👉🏻 SUMIE_London*
7️⃣1️⃣🌺7️⃣2️⃣
"Kai kasan kuwa ni bana zuwa koh ina sabida yayana baya barina Ina zuwa ko ina" ta fada lokacin da take tsugunnawa zata dauki wani dan qaramin dutse, murmushi kawai yake yana kallonta,komai tayi kyau yake mata,barema yanzu data saki jiki dashi,bai taba zaton haka take faran faran sosai bah, harta taso bai dena tunane tunanensa bah ,tsayawa tayi tana kallonsa tareda leka face dina sa tace "Imam lapiya kuwa?" Shi sai a lokacin ma ya tuna labari take basa,murmushi ya qara yi mata sannan yace "lapiya qalau Habibty,me kikagani" ajiyar zuciya ta sauke lokacin dataga yayi murmushi, tace "Imam kasan mene kuwa?" Imam yace "A'a saikin fada" dariya tayi tareda rufe fuskar ta da hannayenta guda biyu tace "Nide kunya nakeji" daria yayi ganin yadda take wasu abubuwa kamar wata wawuya sannan yace "Please mana,tell me menene" washe baki tayi sannan tace "idan kayi murmushi kana kyau sosai tabarkallah" tana gama fadin haka tasa gudu zata bar wajen,shi dariya ma ta bashi daman abinda zata fada kenan taketa wannan jin kunyar, da sauri ya riko mayafinta lokacin da yaga zata gudu, yace "ba inda zakije saikin kalleni kin gayamin" runtse idanunta tayi tana daria tana cewa "Dan Allah kayi hakuri ka sakeni kar wani yazo ya ganmu a haka" Imam yace "Waye zai ganmu Nide saikin fadamin" da qarfi ta qwaci kanta ta sake rugawa da gudu,shima binta ya rinkayi suna gudu suna daria, gudu take sosai tana daria,ji tayi ta daki wani abu kamar mutum,daria take tana cewa "Na shiga uku,taya akayi harka sha gabana,ta fada tana daria tare da haki" jin shiru neh yasa ta bude ido,tsaki taja lokacin da taga meshi ita a zatonta Imam neh ma,bi tayi ta gefensa zata wuce ,da sauri ya damqo hannunta tareda zare mata ido yace "Ke zonan" buge hannunsa tayi tana haki tace "Jabir ka fita daga harka ta,Ana dole neh? Ha'a" Imam neh ya qaraso sannan yace "Fabee meke faduwa neh,waye wannan" wani harara Jabir ya mishi sannan yace "Kai Malam dalla dakata banason shisshigi,ka tapi ka bamu waje" wani banzan kallon Imam ya mishi sannan yace "Kai kasan wace wannan a wajena kuwa?" Wani daria jabir ya sheke dashi tareda tafa hannayensa sannan yace "Waye kai inba wanda yazo maula akan mace ba,daman na dade Ina jin labarin ka,daman inata Allah Allah mu hadu sai gashi yau Allah ya hadamu,toh wallahi kayi gaggawar barin garinnan inba haka bah zaka rasa abu biyu" Tsaki Imam yaja sannan yaja hannun Fabee yace "Fabee mu tapi gida Please dan naga is almost 6 yanzu" tare gabansa jabir yayi sannan ya daki qinjin Imam yace "Kai Amma bakasan koni waye bah koh?,toh idan baka sani ba barina fada maka,ninan daka ganni banida mutunci zan iya sassaraka ba ruwana kuma in zauna lapiya kuma bari kaji na gaya maka ,nine wanda zai Auri Fabeelah,Akanta ba abinda bazan iya bah" Wani murmushin takaici Imam yayi sannan ya fara kallonsa qasa Da sama, kallon fabee yayi sannan yace "Dan Allah bakaji kunyar fadan haka bah,da alama bakuda mirror a gidanku koh,toh dan Allah kaje ka kalli mirror sosai ka kalli suffar ka,sannan ka sake dawowa ka gwada kanka Da Fabee sai kaga ko kun dace ,Amma wallahi kaida ita kunyi hannun riga,Fabee tawa ceh ni kadai InshaAllah" Wani kururuwa yayi zaiyi kan Imam,da sauri Fabee ta shiga tsakaninsu tace "Kul jabir,Kul wallahi,karka sake ka tabashi inba haka ba wallahi saika gwammace kida Da karatu,kuma ai baiyi qarya bah a abinda ya fada,Gaskia ya gaya maka,kalle ka dan Allah wani mummuna dakai,ga shaye shaye,gaka ko ilimin kirki bakada,kamar yadda Imam yace kaje ka kalli mirror,bama saikaje bah kazo nizan baka mirror ka duba kanka ka gani,Qazami kawai,kuma karka sake tunanin koh zaka mallakeni,inma mafarki kake kayi gaggawar farkawa" tana gama fadin haka taja dogon tsaki sannan taja hannun Imam suka wuce suka bar Jabir tsaye a wajen yana cizon yatsa
Zuwa yanzu kuwa mommy ta lalace,tayi baqi ta rame sosai ,daka ganta zata baka tausayi,ga damuwar rashin Imam a kusa da ita ga na Daddyn Imam da yaki sauraron ta,ta kirashi ta kirashi Amma baya responding,ko kwanciya Da tayi a hospital bai kirata ya mata ya jiki ba bare akai ga zuwa dubiya,yanzu ya dena kula da ita kwata kwata ,kamar ba shine wanda baison bacin ranta ba kwata kwata,ada tace bazata nemesa ba har saiya kawo kansa,ta jira tajira harta gaji,yanzu ma gashi tana memansa baya kulata,gashi number din Imam bai shiga,ta kira cousins dinta harta gaji ba wanda bata kiraba amma kowa cewa yake bai gansa bah,hasali ma wasu har gori suke mata suna cewa ,"keda bakyaso aga dan naki kamar wani gwal,ko barinsa shiga yan uwa bakyayi,toh Allah daiya baiyanar dashi kuma Allah ya kyauta" sosai abin ke damunta,yaude ta yanke shawarar cewa zata samu yayanta wato Abban haiam zata mishi magana, Parlour dinsa taje bata gansa bah sannan ta tafi garden,a zaune ta gansa yana karanta wani Littafi,gefe ta samu ta zauna ,sosai yake kallonta tareda kankance idanunsa,Amma baice mata komai ba dan yafi kowa sanin abinda ke damunta, yace "Ya Fateema meke tafe dake" Murmushin karfin hali tayi sannan tace "Ahhm yaya babu komai daman cewa nayi" can kuma sai tayi shiru "ki fada mana Fateema,you're welcome" bayani ta masa akan Daddyn Imam rashin daukan wayanta Da bayayi and all ,tana fada hawaye na zuwa,shi kansa ba qaramin tausayi ta bashiba,rintse ido yayi don baiso yaga qanwarsa tana kuka Da wuya kaga fateema na kuka,duk abinda zaisa fateema kuka toh ba qaramin abu bane,ajiye littafin yayi sannan ya dawo da hankalinsa kanta yace "Fateema mene na kuka kuma,ba sau daya ba sau biyu ba nasha ce miki ki denasa kanki cikin damuwa,kokin manta da cutar dake damunki neh?Eh fateema" girgiza mishi kai kawai tayi alamar "A'a" tareda share majina ,sannan ya cigaba da cewa "Toh ki kwantar da hankalin ki InshaAllah komai zai daideta,tunda Allah yaga zuciyarki kuma yasan kinyi nadama ba kadan bah,mijinki da Danki zasu dawo gareki InshaAllahu,Ina nan ina tayaki Addu'a kema kuma ki dage da Addu'a" kai kawai take girgizawa sabida ko maganar ma idan tana kuka kasashi take,mikewa tayi zata tapi taji yace "Fateema" juyowa tayi Da jajayen idanunta tana kallonsa, yace "Ki shirya nanda next week na biya muku kujera keda Matata zakuje saudiya,daga nan saiki roki Allah sosai akan ya yake miki kuma ya biya mikikudin bukatunki kinji,daganan kuma zaku wuce Dubai" godia tai mishi sosai sannan ta shige cikin gida rai a cushe,ita Konan dacan bason zuwanshi takeba Amma tayi appreciating abinda yayanta ya mata ,dan taga shima ya damu sosai akan halin Da take ciki,sai a yanzu take nadama sosai akan abinda ya faru a baya
Yanzu ko abin ya zamewa zahra jiki bataji bata gani ita a dole saita nemo fabee ko za'a kasheta itama saita kasheta,haka kawai take tsarawa a ranta,itama yanzu ta sake ramewa akan nada,kullum idan tana kuka data bude baki cewa take daddy ta ya cuceta,kuka kam tashashi har idonta ya kusa fitowa,har visa daddynta yasa aka mata na tapiya london ko idan taje zata manta da komai Amma fafur taqi tace Allanka tafar ba inda zataje tana nan har Imam ya dawo a maida aurensu,daddy ba irin hakuri Da rarrashin dabai mata ba Amma ta kyankyashe idanunta ,dan yanzu koshi ba kyalesa tayi ba rashin kunya take masa, yaude da sassafe yazo room dinta tana kwance ya tashe ta,Tana ganin shine tayi tsaki zata koma Da sauri yace mata "Zahra ki tashi ki shirya zamuje garinda Imam yake zamu fara bincike akan komai" firgigit ta mike kamar an cikareta tace "I'm i dreaming" Murmushi yayi yace "No" tashi tayi da sauri ta shiga toilet ko minti goma batai ba ta fito ta saka kaya ko kwalliyan nan da aka saba ba'aa yisa ba ,komai a jaka ta hadashi harda kayan makeup da kuma kaya kala uku sabida taji dad dinta yace zasuyi kwanaki acan,dukda taji ance garin babu dadi Amma ba ruwanta inde za'a kwato mata Imam dinta,shap shap ta gama shiri ta fito,tana kallon Amminta a Parlour Amma ko sallama ta wuce,itama daman Ammin bata damuba,tasaba,tana fita taje inda aka faka motoci wanda zasu tapi dasu,bude mata na tsakiya akayi wanda daddynta ke ciki sannan ta shige aka rufe,saida kowa ya shiga mota sannan aka fara ficewa daga gidan,suka dauki hanya
SUMIE London💄👛