24

59 2 0
                                    

🌸🌺 FABEELAH 🌺🌸
🌺🌸                     🌸🌺






           Ummu Ja'afar
              Mom neehal
                 Sis Hafsie
        ❤️saudaukarwa gareku😘



    
                4️⃣5️⃣-4️⃣6️⃣





       Tun daga lokacin aka shiga yima zahra gyaran jiki ba qaqqautawa,tayi kyau tayi sumul da ita abin sha'awa,mommy ceh tasa aka kira mata Imam "Imam na mance ban fada maka ba,kaje wajen zahra ka tambayeta duk abinda take so,next week neh za'a daura muku aure tare Dana haiam mun riga mun tsayar da zance nida Abbanta, a razane ya dago yana kallonta "mommy ban gane me kike nufi ba ,Zare ido tayi tana kallonsa sannan tace "ina kuwa zaka gane,aiba shawaran ka nake nema bah,kuma dole kayi abinda nace,idanni na cika uwarka wanda na haifeka kuma idanna isa dakai kabi umarnina Imam, da idanunsa wanda sukayi ja lokaci daya yake kallonta cikin tashin hankali,anya kuwa mommy ba wani abu aka mata,kode ba mommynsa bace,Mommyn sa bazata mishi haka ba,duk abinda yakeso shi take mishi,...."kayi shiru,tunanin me kake,ka tashi kaje ka samu yarinya ku tattauna,kuma ban yarda ko kallon banzane ka mata ba bare harka mata magana mara dadi ehe,tashi yayi jiki ba kwari ya mike zai fice tace "baka jiba, ya juyo yana kallonta "wallahi idan ka sake bata mata rai ban yafe bah,ido ya zaro yana kallonta harya juyo zaiyi magana ta daga mishi hannu,da sauri ya fice a wajen,room dinsa ya wuce yayi Wanka sannan ya dauro Alwala,sallah ya farayi sannan ya dade Yana Addu'ar Allah ya kawo mishi sauki a wannan abun ya kuma huci zuciyarsa,tashi yayi sannan ya shirya cikin qananun kaya dukda ba wani dressing yayi ba Amma yayi kyau sosai,kai tsaye wajen Daddyn haiam yaje suka gaisa,nan yake tambayan sa "ya jiki ashe bakaji dadi ba ,eh wallahi Amma ba wani rashin lapiya bane,aina warke ya fada yana dan sosa kai ,"toh Allah ya qara sauki, "Amin yace sannan ya mike zai fita Daddyn ya kirashi,komawa yayi ya zauna "Imam kaje wajen yarinyar nan kuwa kun daide ya, gabansa ne ya fadi donshi baison ko maganar ta ayi bare a ambaci sunanta "no daddy banje ba ,Amma yanzu zanje, "toh kaje kaji,kayi biyayya ga mamanka,insha Allah hakan shi yafi Alkhairi,Allah ya maka Albarka,tashi ka tafi,shide kawai kai yake gyada mishi sannan daga bisani ya fice a room din,yana fitowa sukaci karo da sistrn zahra,kiranta yayi sannan yace mata taje ta kira mishi sistr dinta tace yana garden yana jiranta,sanda sako yazo wajen zahra kamar zatayi hauka don dadi,da sauri ta tashi ta shiga kwalliya ,tayi kyau ba karya,sannan ta nufi wajensa,tun daga nesa ya hango ta tana tahowa,wani abune yaji ya tokare masa a zuciya Amma saiya daure daya tuna abinda mommynsa ta gaya masa dazun,shi yasan bazai taba son yarinyar ba Amma haka zai daure maybe watarana zai sota,kusa dashi ta zauna kamar zata shige jikinsa ,cikin wata irinyar murya ta fara magana tareda kama hannunsa "Hubby na gani nan,naji ance kana nema nah, "yes inaso ki yimin list neh na abinda kike bukata,komai da komai,,,wani farin cikine ya mamaye zuciyanta,ji take kamar yau take sallah "ohh okay tohm shikenan zan yi tunani saina fadawa mommy kawai, nande taita zansa da hira badan yanaso ba yake biye mata har suka dan Saba kadan,tana fada mishi yarda abinzai kasance,Lokacin da Abbanta yazo ya gansu shima ba qaramin dadi yaji ba ganin Imam din ya saki jikinsa da yartasa,mommy ma taji dadin ganin hakan



    
        Cikin wani blue din material wanda haiam ta bata ta shirya tsaf da ita,haiam na gefe ta saki baki tana kallonta ganin yadda ta zage tana fesa turare tako ina, tayi kyau sosai Amma ba wani Makeup tayi ba "gaskia kinason moha dinnan dayawa,yanzu dan zaizo shine kikeyin wa'annan abubuwan "Ahh sosai ma kuwa,idan banso shiba wa kikeso naso,wallahi nayi missing dinshi kinga kuwa dole naci mishi kwalliya kuma yace yau zamu dan fita fah, "Ahh lalllai kam dole kici mishi kwalliya,toh Allah ya bada sa'a ,mude yan kallone,murmushi ta mata sannan ta dauki mayafin ta tasaka sannan ta dauko wayanta ta fice don tuni moha din ya kirata yace yana parking lot,tun daga nesa ta hango sa,a hankali take takawa harta karasa inda yake,sunyi farinciki da ganin junansu sosai sannan sannan moha yace "baby rufe idonki,rufe ido tayi tana jiran taga me zaiyi,ce mata yayi ta bude,wani murmushi neh ya kubce mata lokacin dataga waya a hannunsa wanda saida haqwaranta suka bayyana "babe phone dinda na miki alqawari neh,bai kamata ace kina rike irin phone dinnan ba ya fada tareda karbar nokian dake hannunta, IPHONE 7 ceh JET BLACK mai kyau sosai,Amma sai naga kamar wannan yamin girma koh? Ta tambayesa, "no wallahi bai miki ba,naso babbansa ma na siya miki Amma kawai shine na fasa sai mun kusa aure "Tohm thank you so much sweetheart I love you, ta fada tana kamkame hannunsa,wani irin dadi yaji sannan yace mata "I love you more princess,hira suka cigaba dayi har ya juya kan motar suka fita daga gidan,duk abinda sukayi Akan idon Imam sukayi shi,ji yake kamar ya fashe da kuka sabida yadda zuciyarsa ke masa,lokacin sun rabu da zahra ta shiga cikin gida ,shima gidan ya shiga kai tsaye dakin haiam ya wuce "haiam Ina  yarinyar nan zataje itada moha, "wallahi nima ban saniba kawai de naga tanata zabga uban kwalliya,kuma tacemin yau yawo zasuyi sosai "kuma shine Kika barta ta fita,bakisan riski bane abar mace da na miji su fita su biyu ba kuma ita tasan waye moha neh da zata bishi,kuma da iyayenta suka baki amanarta sunce ki barta ta kula wanine,fada yakeyi sosai har jijiyar kansa na tashi,da mamaki take kallonsa "tohm mezai mata,ba abinda zai mata ,kuma fabeela da kake gani yarinyar ceh mai hankali bazata taba yadda ya mata komai ba ,tasan abinda takeyi kuma zasu dawo nan bada dadewa ba ,ba abinda ya isa ya mata wanda Allah bai mata shi ba,dukde na ganeka,kishi neh ya janyo hakan koh ta fada tareda qarasowa inda yake tana daria "ba wai kishi bane haiam inde kishine me sauki neh,ni nasan halin moha tun muna school,baijin magana,idan yaga kyakyyawar mace burinsa kawai yaji a dandanonta yake neh,toh kinga kuwa dole hankalina ya tashi,sosai haiam ta tsorata dajin abinda Imam din ya fada Amma saita dake tace "nooo Imam please stop saying that insha Allah nothing will happen ,Allah yasa yace mata "Imam ya zancen zahra kuwa,murmushi yayi sannan yace mata yanzu muka rabu da ita,da mamaki take kallonsa tace "bade ka fara sonta ba "hmm haiam kenan yazanyi ko banso taba maybe wataran zansota,na zauna nayi tunani akai,kuma mommy da Daddyn ki sunmin magana dole na hakura nabi abinda takeso,tausayinsa neh ya kamata tace "Allah sarki Imam yanzu ka hakura da fabeela kenan "no ban hakura da itaba ,mata biyu zan aura,daria tasa sannan tace "waya gaya maka zahra zata yadda ka qaro mata kishiya,kuma kishiyar ma ba kowa ba sai fabeela,tab rikici kenan,tabe baki yayi sannan yace "aiba gida daya zan hadasu ba kede kibar komai hannuna,i know what i'll do,hira suka cigaba dayi na yan uwa har lokacin ransa bai dena baci akan abinda ya gani ba ,yaci alwashin idanta dawo saiya mata magana



      
     Waka ceh ke tashi a motar me suna ME AND YOU ,dukansu shiru sukayi,ganin yayi shirune tace "ina zamuje neh, "duk inda kikace nan za'aje,murmushi tayi sannan tace "aini bansan ko ina ba kaine zaka fada ,murmushin shima ya maida mata sannan yace don't worry yanzu zakiga inda zamuje, BRISTOL PALACE sukaje,wajen ba karamin kyau ya mata ba ,pool side sukaje,wajen ya bata sha'awa sosai ,waje suka samu suka zauna sannan wani waiter yazo yana tambayansu me zasuji,ganin taki fadane yasa yayi mata choosing the same da nasa, sundan jima kadan kafin waiters din suka shiga jero musu Abubuwan da sukayi order,Burger and cheeps neh sai Wafles and chocolates,sai kuma ice-cream don ita tace mishi batajin hunya sai kuma chapman,bata wani ci sosai ba dan magrib ya sawo kai ,nanta takura masa Akan su tapi,waiter ya kira sannan ya ciro ATM card dinsa aka cirin kudin ta P.O.S,sannan suka fito,parking yayi a gefen titi ya tsaya yana kallonta,da mamaki take kallonsa sannan tace "babe me ka tsayayi Ana ,mu tapi mana , "inason ki rakani wani waje mana.,,"kai gaskia yanzu dare yayi saide gobe,ina zan rakaka "gidan wani friend dina zaki rakani ,ido ta zaro tace "kaii gaskia bazan je ba ka kira Imam mana ya rakaka "no ni ke nakeso ki rakani ya fada lokacin da yake matsowa kusa da ita, da sauri taja baya tareda zaro ido "mene haka kuma kakeyi "I just wanna kiss you babe ya fada tareda qara matsota,kuka tasa sannan tace "na shiga uku please bazan iyaba ka kaini gida kaji "fizgota yayi sannan ya kwantar da seat dinda take ya shiga shafata,ihu tasa,sannan ta turesa da qarfi,janyota ya sakeyi zai hada bakinsu,batasan lokacin data watsa mishi wani Mari ba TASS,a razane ya dago yana kallonta idanunsa sunyi jaa, "ke ni kika mara, "na mareka din,mayaudari kawai,daman wani abun kakeso bani ba ,toh Wallahi Allah ya isa tsakanina dakai tana gama fadin hakan ta bude motar ta fice da sauri,yana ta kiran sunanta Amma taki ta juyo,har taga wani mai keke napep sanann ta shiga ganin da kudi a jakar da haiam din ta ara mata,wayarta ta ciro sannan ta kira haiam din tace tayi mata kwatancen gidansu don ita ba sanin ko Ina tayi ba ,da mamaki haiam take tambayan ya "ke Ina moha din bazai dawo dake ba "kede ki bari idanna dawo zan fadamiki koma mene kikeso kiji,har get din gidan yayi dropping dinta sannan ta sallamesa ta shiga gidan kai tsaye dan masu gadin sun gane ta,tapiya mai tsayi tayi sosai kafinta shiga gidan sabida gidan ba karamin girma neh dashi ba ,tana shiga kai tsaye dakin haiam ta wuce,tura kofar tayi tana ganin haiam din ta fada kanta tana nishi sama sama ,wani kuka tasa tana fadin "haiam ashe moha ba sona yake ba ,akwai abinda yakeso a wajena,moha ya cuceni saida yasa na fara sonsa mesa zaimin haka ,toh fah ga maganar Imam nan yazo ta fada a ranta "me ya miki fabee,cikin kuka ta kwashe komai ta bata labari sai a lokacin ma ta tuno da wayar da ya bata nanta dauko jakar ta ciro phone din ta nuna mata ,"kin min daide da kika maresa,shege dan iska,matsiyaci ki maida masa da wayarsa ba'aso, nan haiam taita fada sannan taita rarrashin fabee hartayi shiru,daga bayan kofa kuwa Imam neh a labe yana jin abinda suke cewa ,daman tun data shigo ya ganta ,da yayi niyar ya shiga daki ya mata magana jin sautin kukanta neh ya dakatar dashi sabida yasan idan ya shiga bazata fada a gabansa ba ,ransa ba karamin baci yayiba da jin labarin da fabeela ke bawa haiam ,wani sabon tsanar moha yakeji a ransa,shi daman yasan zai akata tunda ya sanshi tunda ba yanzu ba,da haka ya juya ya koma Parlour ya zauna yana kallo Amma hankalinsa ba'a kai yakeba,jira yake fabeela ta fito ya titsiyeta

SUMIE London 💄👛

FABEELAHWhere stories live. Discover now