🌸🌺 **FABEELAH** 🌺🌸
🌺🌸 🌸🌺Aunty Ayoosh👅
Fatu❤️
Billylosh👭
Sis Rouker ❤️
**Sadaukar wa gareku **4️⃣3️⃣-4️⃣4️⃣
Washe gari tunda safe fabee ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga black me disign red a jiki,sai red veil ta daura akanta,lips stick kawai ta shafa sai powder sannan ta nufi room din haiam,lokacin dataje bacci take don haka bata tashe taba ta juya ta fice daga dakin domin komawa nata,shirun dataji gidan yayi neh yasata sauka kasa,da mommyn haiam suka hadu a wajen step zata shiga kitchen,durkusawa tayi har kasa ta gaishe ta,da Fara'a itama ta amsa mata sannan ta shiga kitchen din,binta tayi a baya tana tambayan ta ko akwai abinda za'a mata,tace "no my daughter kije ki huta,wai abban haiam neh zai fita kuma baison abincin masu aiki shine zan dafa mashi "laa mommy ki kawo na dafa mishi toh mana,daria tayi sannnan tace "Ayi haka kuwa, itama fabeelan daria tayi sannan ta karbi plate din dake hannun mommy tace "ba komai mommy kije zan dafa mishi ai kema mamata ceh, murmushi tayi sannan tace "toh na gode Allah yayi miki Albarka,kina jina koh?, cheeps and chicken nakeso kiyi masa sannan ki masa kunu,sai kuma ruwan tea, that's all, "Alright tace mata cikin ladabi da biyayya, sannan ta shiga aikin ta ita kuma mommyn haiam ta fice daga kitchen din,ba'a dade ba ta gama komai,tuni gidan ya dumame da kamshin abincin,Nan mommyn tazo tace mata ta debo a cikin flask ta hado komai ta kawo part din dad din haiam ,tana zuwa ta jera komai sannan ta sake komawa kitchen din ta cigaba da aikin, tadan yi shi dayawa sabida itada haiam ,tana gamawa ta kwashe ta nufi room dinta,dakin haiam ta sake komawa sannan ta tashe ta nan ta gama shiryawa suka sake komawa room dinta sukayi breakfast sannan suka sauka qasa, a garden suka zauna suna hiran yadda bikin zai kasance,Wata mai aikice tace wa haiam Ana kiranta,ta mata nuni da wani part, "kije kice Ina zuwa,tashi tayi ta tapi,mommyn Imam ceh a zaune kusa da wata qawarta suna hira,tana shiga ta samu waje ta zauna tace "mommy kece ke kirana "yes nice nake kiranki, mene yasa jiya kika aika wannan yarinyar wajen Imam,kallonta tsaya yi sabida mamaki,ita datasan abinda yasa ta kirata kenan da cewa zatai ace mata wani abu takeyi,maganar mommyn neh ya dawo da ita daga tunanin da take "haiam I'm i not talking to you,toh bari kiji na fada miki,daga yau sai yau karna sake ganin kin bari ko magana ta shiga tsakaninsu bare har kikai ga aikata inda yake,banaso,tashi ki tafi ki bani waje,jiki a sanyaye ta tashi ta fita daga part din zuciyarta na mata kuna,wai me fabeela ta danne musu neh da suka tsaneta haka,da tasan abinda zai faru kenan bazata gayyace ta ba bare harta zo a wulakanta ta,sakin fuska tayi don kar fabeelan ta gane akwai wani abu sannan ta karasa inda take ta zauna,bata jima da zama ba mommy ta sake aikowa a kirata,tana zuwa tace mata tana so tasa masu aiki su kaiwa Imam abinci baijin dadi,dazu taje dubashi yana bacci kuma yanzu tayi baquwa,okay tace mata sannan ta sake mikewa ta fice, "Sai naga kamar dazu bamu cinye cheeps dinnan ba ko,haiam ta ke tambayan fabeela lokacin da take qarasowa "yes akwai,zaki qarane fabeela ta bata amsa "no mommy ceh tace na kaiwa Imam breakfast , "Alright ki kai mishi mana,yana daki nah, "tohm muje ki rakani, ba musu ta tashi ta bita,kai tsaye room din fabee suka wuce suka dauko kayan breakfast din sannan suka nufi room din Imam,lokacin da sukaje harya shiga wanka,ganin yadda room din ya rikice neh yasa suka kintsa mishi sannan fabeela ta fice daga room din,ba yadda haiam batai da ita akan ta zauna ba amma taqi don haka kawai saita kyale ta.....,a bangaren mommyn Imam kuwa,dukta kwashe labarin abinda ke faruwa ta bawa qawar tata, da mamaki qawar take kallonta "lallai fateema shine baku koreta ba ,ina Imam ina yar talakawa, "hmm kede bari ai shine nakeso nayiwa tufkar hanci, gyara zama qawar tata tayi sannan tace "wai cewa yayi yana sonta neh ko kuma me , "no baice yana sonta ba ,kawai de naga take takensa neh,,.."toh wallahi fateema ki gaggawar mikewa tun wuri ku mata korar kare inba haka ba saide kiji a salansa,kinsan mu bama harkar qaranta,bazaiyu ace danmu nason yar kauye ba ,ina ruwanmu da kyawunta mtseeww,nan taita bama mommy shawarwari marasa kyau,itama kuwa tahau kai ta zauna daram sannan ta rakata har mota driver ya tapi da ita
Kai tsaye mommy wajen Abban zahra taje,tana zama ta mishi bayani Akan zancen Imam da Zahra,nan suka yanke shawara akan idan za'a cigaba da bikin haiam ranar daurin aure sai a hada Da nasu,Abban Zahra ba qaramin murna yayi ba,yana saka abubuwa kala kala a ransa na mugunta,mommy ceh ta dawo dashi daga tunanin da yake tace "yanzu ya zamuyi da yarinyar nan,friend dinI haiam Cox naga kamar sonta fah yake,wani shu'umin daria yayi sannan yace mata ,fateema kenan ai wannan ba komai bane a wajena,nide kawai na gode da kika amince danki zai auri yata,Allah yabar zumunci na gode sosai,Amma me kike ganin ya kamata ayi Akan wannan lamarin,magana ya farayi kasa kasa wanda ni kaina banji me sukace ba ,kawai sai naga Abban Zahra ya tuntsure da daria sannan yace gaskia fateema shawarar ki yayi sosai,karki samu damuwa nizan shirya komai,hirar yadda bikin zai kasance suka shiga yi har lokacin da Zahra ta shigo Parlour din,da murna taje tayi hugging mommy suka gaisa,sannan mommy ta fada mata yadda sukayi da Abban nata,tace mata tayima me yiwa haiam gyaran jiki itama za'a fara mata nanda anjima,murna kuwa bai misaltuwa wajen zahra,harda sunkuyar dakan munafurci anayiwa mommy godiya "ba komai zahra ai kema yata ceh kamar yadda Imam yake Dana ,yanzu ki tashi kije ki dubashi,baida lapiya tun jiya, Tohm tace mata sannan ta mike ya fice ,saidata biya room dinta ta feshe jikinta da turare kasancewar tayi wanka,sannan ta shafa powder ta tapi wajensa,shiga tayi kai tsaye ,zaune ta gansu,da alamu yanzu ya gama breakfast haiam na bashi magani,da sauri ta qarasa tayi hugging dinsa,tana wani shagwaba "eyya babe nah ashe bakaji dadi ba ,ban sani bah sai yanzu mommy ke fadamin tace naje na duba ka...,wani harara ya watsa mata sannan ya daka mata tsawa "I'm i your mate,i'll slap you right away,will you get up,stupid kawai ya fada tareda tureta da qarfi, cikin kuka ya fara cewa "mommy ceh fah tace nazo na dubaka,wallahi saina fada mata tana gama fadin haka ta fice tana kuka, tsaki yayi sannan ya juya yana kallon haiam wanda tun dazu haushi ya sakata ta kasa magana...dan numfasawa tayi sannan tace "Allah daiya kyauta,bari naje Imam inada abinyi,zan dawo soon,Alright yace mata sannan ya koma kan gado ya kwanta
Mommy ceh ta shigo rikeda hannun zahra rai a bace tace "Imam me kake nufi neh,me yarinyar mutane ta maka,daga zuwa dubiya shine zaka mata wulakanci,karka sake banaso,kuma wallahi saika aureta saide ka mutu,yi hakuri kinji zahra jeki hada mishi ruwan wanka,duk abinda ya sake miki ki gayamin,bata jira taji mezaice ba ta juya ta fice,toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka sannan ta dawo ta tsaya a kansa tana masa magana,ganin yaqi kulata neh yasa ta fada kansa,tana shafa mishi jiki a hankali,bakinta takai daide nasa zatayi kissing dinsa da sauri ya tureta yana cewa "ke wallahi ki shiga hankalin ki,niba dan iska bane irinki kinji,karkiga kamar mommy tamin magana Shiyasa kike abinda kikaga dama toh wallahi tattaka ki zanyi,tashi ki ficemin daga daki banson ganinki, "naji ba komai ko me zakace kace,wataran zaka soni idan mukayi aure,tana gama fadin haka ta shafa mishi gefen fuska tareda kashe mishi ido daya ta fice daga room din,
SUMIE London 💄👛