Part 13

83 2 0
                                    

🌸🌺 FABEELAH 🌺🌸
🌺🌸                     🌸🌺



            2️⃣3️⃣-2️⃣4️⃣


      Dedicated to Bilylosh❤️ the LOML😩❤️ Allah ya albarkaci rayuwarki bestfriend❤️👭


      Dukansu tsayawa sukai suna zuba ido suga waye me turo qofar, lokaci daya kuma ya tamke fuska sosai ya hade rai ganin zahra ceh a tsaye tayi fiki fiki da ido tana kallonsu,itama mommy tsayawa tayi tana kallon yarinyar da mamaki shimfide akan fuskar ta ganin yadda taci kwalliya ta matse kamar zataje club,sai kuma ta saki murmushi tana cewa "A'a zahra ceh kenan ,qaraso mana 'yata ,taji kunya don bata zaci zataga mommy ba amma kawai saita daure ganin mommy tana mata murmushi,itama murmushin ta mayar mata sannan ta qarasa ta durqusa har qasa ta gaishe ta ,dagata mommy tayi tace "tashi mana zahra, giftasu yayi zai wuce mommy tace "kai Imam bakaga yar uwarka ba zaka wuce bazaka tsaya ku gaisa ba, daga inda yake yace mata sannu yana kallon wani gefen,kafin ta bashi answer yasa kai ya fuce rai a bace,shi meyasa mommyn shi take mishi haka ,ita batasan baya son ko ganin yarinyar bane dahar zatasa ma ya mata magana salan ta raina shi,yarinya sai kace mayya kullum saitaje inda yake, inda tasan tsanar da yake mata da ko cemata akayi ta kalleshi bazatai ba, ita kuma tana tsaye tareda mommy ta rasa me zata ce mata,phone din mommy neh ya fara ringing,da sauri tayi picking jin muryar matar yayannata tana cewa "Fatima kina ina,me muku kunshin fa tazo tun dazu ke kawai ake jira tunda kince ke za'a fara yiwa , "toh ganinan zuwa yanzu ta fada tareda katse phone din tana kallon zahra dinda ta sukayyar dakai tana faman danna waya tace mata "zahra bari naje anzo mana kunshi kinji "toh tace mata don ita kunyar tama take ji sabida yadda Imam ya yarfa ta dazu a gaban mommyn,itama mommyn ta gane abinda yasa ta kunyar da haka ta tashi ta fice a dakin ta nufi part dinda mai kunshin suke,tana fita zahra ta saki wani nannauyan ajiyar zuciya sannan ta kwanta akan kujera a hankali tayi rufda ciki tana tunanin hali irinna Imam,waishi wannan wani irin mutum neh,mesa yakemin haka neh, ko dan yaga Ina nuna damuwa na akansa neh, saita saki wani kuka maicin rai tana cewa "wallahi saina aureka Imam wallahi dole ka aureni,kuma insha Allah saika soni,mena banda shi wanda baka sona,gani kyakkyawa,in farinne nima inada shi,idan dressing neh Nina baza'a barni a baya ba,idan kudinne iyayena sunada shi,cikin shassekar kuka taketa fadin maganganu kala kala har bacci yayi awan gaba da ita

  

       Shikam yana fita yayi hanyar cikin gidan ,sama yahau da nufin yaje room dinsa, anan ya hadu da haiam din itama da saka abaya baki zata nufi room din fabeelah, "tana ganinsa ta saki murmushi shima murmushin ya maida mata sannan ya qaraso inda take yace "Amarsu ta ango,waike ina kika shigane ba'a ganinki sai za'a tafi event,daria tayi sannan tace Ina nan mana kawai dai fitane banson yi sabida mutane sunyi yawa a gidan kuma ko Ina ka wuce kallonka ake ni kuma banson kallon ka sani, "toh yanzu ina zakije da kika fito "zance wajen fabeelah neh sabida zata rakani na karbo dinki a wajen Wani tailor dina,shiru yayi yanason ya tuna mai sunan amma ya kasa sai yace mata "who's she yana kallonta "my bestfriend mana ta fada tana fara tapiya "ohh okay ,toh mesa bazaki ayka a karbo miki ba "no zan gwada Kayan neh acan kar naje tayi ba daide ba "okay ya sake ce mata ya juya zai tafi ta riko hannunsa tace "what are you doing now "nothing yace mata ya tsaya yana kallonta,akwai wani abune ya tambaye ta "yes inaso ka rakamu wajen mana ,shiru yadanyi for a while sannan yace mata okay no problem ku shirya sai kuzo ku sameni a room dina Ina jiranku "okay tace mishi sannan tayi gaba ..tana zuwa tasa fabeelah a gaba dole saida ta shirya,wani doguwar riga ta saka red mai design baki baki a jiki sannan tayi rolling da vail baki,sai ta saka palms black shima ,dukda ba kwalliya tayiba amma tayi kyau sosai kamar balarabiya,suna fitowa ta rufe room dinnata sannan sukayi room din Imam,itade tasan qasa zasu sauka amma taga sunyi wani part din batace komai ba kawai bin haiam din take don a zatonta ta zaci wani abu zataje ansa, a kofar wani room taga sun tsaya haiam tana ta norking anki budewa, haiam ceh ta fara magana "wannan wani irin abune wai,nima aji zaka jamin,anata norking tun dazu ya wani share mutane,dallah fabeelah zomu tapi sale ya kaimu,taja hannun fabeelah suka juya sun fara tapiya kenan yazo ya bude qofar yana cewa ,"toh al masifatu Ina toilet mana ,kinsan ko zanyiwa kowa ke bazan miki ba ya fada yana kallon su ,ita kuwa jiyo wa tayi tana hararar shi sannan tace muje fabeelah,yaga dama yazo ya bude, ita kuwa fabeelah tunda haiam din take fada take kallonta baki sake dan ita batasan dawa take ta faman fadannan ba ,saida suka juya ta jiyo muryarsa sannan gabanta ya fara bugu da karfi, dakyar ta iya juyowa,tana juyowa sukayi idon biyu kuwa dashi,wani abu dukansu sukaji a jikinsu ,a take ta sunkuyar da kanta kasa haiam najan hannunta har suka qarasa  inda yake sannan ya basu hanya suka shige, anashi bangaren kuwa shima tunda ta juyo yake kallonta, bai taba kallonta sosai ba sai yau "she's beautiful ya fada sannan shima ya juyo tare ta tura kofar ya rufe ya nufi cikin room din,suma suna shiga suka zauna akan chairs dinda suka room din guda biyu ,tunda suka zauna haiam take ta surutu shima biye mata yayi sunata yi yana shiryawa,ita kuwa fabeelah shiru tayi ,burinta kawai su fita daga room din ,dukda sanyin ACn dake room din amma zufane ke keto mata a haka ,shima kuma suna hira yana dan kallonta da gefen ido,yana gama shiryawa cikin jallabiyarsa brown color sannan ya fesa turare ya dauki phones dinsa sannan yace musu ya gama su tashi su wuce, suna fita harabar gidan daide lokacin da suka fito haiam da fabeelah suna baya shi kuma yana gabansu yana cewa shifa ba sanin gari yayi ba don haka sai sun nuna mishi, a lokacin zahra ta tashi daga bacci ta fito daga part din zata shiga cikin gidan ta hango su, tana ganin fabeelah a take ranta ya baci ganin yadda tayi kyau ras da ita,da sauri ta nufi inda suke tana cewa "haiam Ina zakuje ta fada tana qarasowa a daide lokacin da haiam suke rigima da fabeelah akan saita shiga gaba ,ita kuma fabeelahn tace haiam dince zata shiga gaba tunda itace cousin dinshi kuma itace zata nuna musu hanya tunda itace tasan gari, ganin zahra tana tambayan haiam dinne ta bata answer da cewa "wajen dinki zamuje ,,Imam neh ya katsesu da cewa "ke haiam wallahi zan fasa kaiku idan baki shigo mun tapi ba ,,, zahra ceh tace "zan rakaku please ,,,,daman fabeelah tana ganin zahra tayi sauri ta shige baya sbd kawai batason ta fara mata wannan kallon banzan nata,,shiga haiam din tayi sannan zahra din ita kuma ta bude murfin gaban ta shiga ta zauna kenan taji yana cewa "ke Ina zakije ,who invite you,,,please fita,fita ,ya fada yana raising voice dinsa tareda zare ido yana nuna mata hanya alamun ta fita ,dukkansu tsayawa sukai suna kallonsa,haiam ceh tace "haba Imam mene haka wannan wani irin cin fuska neh ka barta mana muje tare tana fadin haka taga ya bude murfin mota ya fita yace "ai kema kin iya driving saiki jaku ku tapi ya fada rai a bace,,da sauri haiam din ta fito ta riqe mishi hannu tana cewa "yi hakuri please bari na mata magana ,, ita kuwa zahra tuni hawaye suka fara rige rigen fita daga idanunta,tama kasa magana sabida tsabar mamaki da kuma kunya,,da gudu ta fita ta nufi cikin gida tana kuka sosai,haiam tana ganin ta fita sai ta jiyo tana kallon Imam tace "haba dan Allah kalli yadda kasa yarinyar mutane kuka ba gaira ba dalili,me ta maka neh wai,haba Imam dan Allah bakasan wukanta dan Adam bashida dadi ba kuma kaima kasan yanzu idan ta shiga gida In iyayenta suka gani bazasuji dadi ba ,karka manta fa cousin dinka ceh, shiko ko kulata baiyi ba ya juya ya shige cikin motar ,gani yake shi bazaima iya magana ba sabida yadda ranshi ya baci, shi baisan mesa ba baison yarinyar kwata kwata,yana cikin tunanin neh yaga itama haiam din tana qoqarin bude kofar bayan zata shiga a fusace ya juyo yace "waye driver dinku da zaku shiga baya dukanku, wallahi zan fasa kaiku aiba dole bane ,ko kulashi haiam batai ba sabida yadda ya bata haushi,wayarta ma ta dauko tasaka earphone ta saka waka ta fara ji, ita kuwa fabeelah tunda taga yayiwa zahra haka a take taji tsanarsa ya mamayeta ga tsoronshi da ta fara ji,don ita batason mutum mai wulakanta dan Adam,ganin haiam batada niyar fita kawai ita kuma saita fita ta koma gaba cikeda far gaba ,haka yaja motar suka fara tapiya ba Wanda ya kula kowa ,can haiam din ta dago tana mishi kwatance har suka qarasa, yana packing suka sauka ,shi kuma phone dinsa ya dauka ya shiga kiran Moha yaji yana ina ,nan sukayi waya da Moha yace mishi yaje su haiam karbar dinki,shima Moha ceh     Mishi yayi yaje yakai mamansa hospital batajin dadi amma anjima zaizo ,nan yace yai mata ya jiki shima zaizo ya duba ,da haka sukayi sallama ,ganin har yanzu su haiam basu fito ba shiga kiranta a waya,ba'a dade ba sai gashi sun fito ya gansu sunata daria, yadda fabeelah take daria ya burgeshi sosai don haka kallonta kawai ta tsaya yi,shi baisan meyasa idan tayi wani abu tare birgeshi ba,yarinyar nada nistuwa Sosai kuma tanada hankali,yana cikin tunanin yaji sun bude murfin motar zasu shigo ,suna shiga ya tashi motar suka nufi hanyar gida

    Ita kuwa fabeelah tana shiga gida kowa sai binta yake da ido ganin tana kuka sosai , wasu kuwa tambayar ta suke kodai wani abinne ya faru amma kota gansu batabi ba ta nufi inda su mommy suke Ana musu kunshi ta shiga part din da gudu ta qara qarfin kukannata ,a lokacin mommy aka gamawa sannan aka kama yiwa matar yayannata wato Hajiya Amina, suna cikin hirarsu sukaji shashhekar kuka,daga kanda zasuyi sukaga zahra ta shigo tana kuka ta fada kan cinyar Ammin ta daman ita ba'a fara mata ba ,a firgice suke kallonta tare da hada baki wajen fadi meya faru,meya same ki,dansu azantonsu wani gagarimin abune ya faru,cikin shashekar kuka ta fara cewa Ammi nah IMAM,IMAM Ammin,, a firgice suke tambayanta meya sameshi barema mommy da duk hankalinta ya tashi taji ana kiran tilon danna ta ,tuni ta mike tana yunkurin tashi tsaye zata bata kunshin ta ,abinda taji zahran tana fadane yasa ta fasa tashi hankalinta ya fara kwanciya don ita a zatonta ta zaci wani abune ya sameshi,,,cikin kuka take basu labarin abinda ya mata ,kanta a kife kan cinyar Ammin ta ,a zafafe ammin ta tureta, tana dagowa ta tsinketa da wani gigitaccen mari ta qara wanka mata wani marin cikin fushi ta fara magana "ki fita a idona zahra'u nace ki fita a idona,sau nawa na gaya miki,wallahi idan bakiyi hankali ba saina sassaba miki, shegiya mara kunya mara mutunci yanzu dama akan wannan abin shine zakizo ki tada mana da hankali kina shirinsa uwarsa a wani yanayi,zahra wallahi tallahi idan baki fita harkar Imam ba ranki zaiyi mummunan baci,tambadaddiya kawai ,mara kunya yanzu harke kin isa kizo kina bamu labari abinda Imam ya miki,aini wallahi yamin dede,kuma insha Allah bazai taba sonki ba har abada ,bacemin da gani kafin na tashi na saba miki kamanni,Ammin ta fada tana shirin mikewa zatayi kan Zahran ,mommy ceh tayi saurin rikota tana "haba maryam wannan wani irin hukuncine ai ba haka ya kamata ki mata ba ,a hankali zaki bita ,Ita kuwa zahra tunda tasha mari bata iya gane komai sosai tanajin Amminnata tayi yinkurin tashi zatayo kanta ta mike ta fita da gudu,kukanma ya kasa zuwa mata yanzu sai ajiyar zuciya take saukewa da qarfi, cikin fushi Ammin ta fara yiwa mommyn Imam magana "wallahi fatima bakisan halin wannan yarinyar ba ,makira ceh,na bita ta lallami ,nayi nayi da ita akan Imam data hakura dashi amma tayi taurin kai ta nunamin ban isa da itaba shiyasa dole yanzu na fara koya mata hankali, "toh wai meyasa bakyasonta da Imam inji mommyn Imam din tana tambayar Ammin zahra "nan Ammin ta kwashe labarin Muaz ta basu sannan kuma da gwagwar mayar da 'akasha kan ya yarda zai aure ta sannan ta qarashe da cewa "yanzu ma barina fada muku wani abinda baku sani ba auren saura one month, mommy ceh ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Gaskia dai zahra batada hankali, nan mutanen wajen sukaita Magana akan cewa Gaskia bai kamata abinda zahran takeyi ba ..haka sukaita bawa Ammin zahran baki har ta sauko daga fushin da take....

SUMIE London 💄👛

FABEELAHWhere stories live. Discover now