🌸🌺 *FABEELAH* 🌺🌸
🌺🌸 🌸🌺*Dedicated to my group members DANDALIN LATEST NOVEL👩❤️👩🌸 I love you die*❤️❤️
*Wattpad👉🏻 SUMIE_London*
6️⃣7️⃣🌺6️⃣8️⃣
Bacci yake sosai dukda irin saurayen Da suka ciccizesa amma sabida tsabar wahalar dayasha har asuba tayi akayi Sallah bai sani bah,da yake shima Sama'ila sallah ba damunsa tayi ba dan haka bai damu ya tashesa ba ,fabeelah ceh a zaune a Parlour Da plate a hannunta Da alamu abin zaqi neh a ciki takesha, Da gudu ta tashi lokacin data hangosa shida securities Lokacin Da suka doso dakan motansu cikin gidan,tun kafin su gama packing taketa tsalle alamar ta qagu ta ganshi,shima ya qagu ayi packing ya fito ya sameta ganin sun kasa gyara packing dinda wurine yasa shi dakatar dasu yace "Kai wai meke damunku,kuyi maza ku tsaya na sauka" ya fada tareda zare musu ido. "I'm sorry sir" driver din ya fada tareda tsayawa,fita yayi Da sauri kamar wanda aka tsikareshi Da gudu tazo tayi hugging dinsa tareda rintse idanunta tana daria,shima darian yake sannan ya dauke cak sukayi cikin gidan,saida sukaje Parlour sannan yayi dropping dinta,plate din fruit din dake a ajiye akan center table ya kalla sannan ya maido idanunsa kanta tareda lakace mata hanci yace "Princess anya kuwa ba baby na bane a wannan plat tomy dinnan naki bah" zaro ido tayi tana kallonsa sannan tace "Kai babe nah yanzu kuma wani baby ana zaune qalau koka manta bamu taba..🙊" tana zuwa nan ta kasa qarasawa,daria ta tashi sannan yace "Tohm princess Ai InshaAllah yau zamu samu babyn mu muma,ki zama mommy na zama daddy" da sauri ta kife kanta a jikin kujerar tana daria,shima daria ta bashi,Da sauri ta dago tace babe nah ba kace yau zamuje gidan mommy bah,murya a shagwabe,murmushi yayi tareda mika hannu ya dauko plate din fruit din ya dauki daya zai saka a baki ta rike hannunsa sannan ta juya ta dauko Fock din data cillar dazu bata sani ba sabida tsabar zumudin ganinsa,guda daya ta dauko ta saka masa a baki shima kuma yana bata,saida suka kusan cinyewa sannan tace "babe magana fah nake maka" ajiyar zuciya yayi sannan yace "Ki bari gobe sai muje Da wuri saiki wuni acan" take ta hade rai,idanunta harsun cicciko Da qwalla,zaro ido yayi yace "OMG princess me aka miki" sosai ta fara kuka,hankalinsa ba qaramin tashi yake ba idan yaga tana wannan kukan dan haka Da sauri ya janyo ta jikinsa ya fara rarrashi sannan yace mata "princess akan nace bazamuje gidan mommy yauba shine kike kuka?" Dago jajayen idanunta tayi sannan tace "Ba kai bane bah,tun rannan kake cemin zaka kaini Amma kaqi kaini,kuma tun rannan mukayi waya da mommy tace dan Allah muzo,kaga fah mommy har rokonmu tayi Da Allah" daria ta bashi yadda take maganar tana cuno baki sannan yace "Tohm I'm sorry zamuje kiga mommy yau ,kar naje ki hanani bacci " dukansu daria suka saka sannan yace "tohm babe muje mana ki shirya ni inci abinci dana gama sai muje gidan mommy" da sauri ta mike tareda ansar bag din hannunsa,kai tsaye daki sukaje ganin zai cire kaya a gabanta neh yasa tayi saurin ficewa daga dakin,sosai ta bashi daria daman kuma yasan kawai biyosa tayi Amma bazata iya tsayawa har yayi wanka ba , a fili ya furta "matsoraciya,ai yau zanyi maganinki" saida ya gama komai sannan ya saka jallabiya ya fito ,lokacin harta gama hada abinci akan dining table,sosai yayi mata kyau harta manta Da abinda take tana ta kallonsa har saida yazo yayi waving face dinta sannan ta dawo hayyacinta,sosai taji kunya Da ganinta Da yayi tana kallonsa,shima ya gane hakan don haka ya basar,hannunta ya rike sannan ya zauna ya daurata itama akan cinyar sa,serving dinsa tayi sannan ta fara bashi a baki,shima spoon ya dauko zai kai bakinta tace mishi "Ta koshi" ganin ya dagene yasata ta faraci,tare suka gama komai har maida komai kitchen tare sukayi ,ce mata yayi ta rakashi daki zai chanja kaya,binsa tayi don itama tanason chanja war sabida fitarda zasuyi Amma kuma tana tunanin taya zata chanja kaya a gabansa,har suka karasa daki tunanin Da take kenan,suna shiga ya juya ya saka key,sannan yaje door din toilet ma ya saka key dan yasan idan taga ba yadda zatayi toilet take fadawa,ganin yana karasowa kusa da itane yasa tayi rau rau Da ido,pushing dinta ya rinkayi har sukaje bakin gado,zatayi magana yayi saurin hade bakinsu,wani rikitaccen kiss ya fara mata,tun tana kaucewa har ta kasa sosai yake kissing dinnata,gown dinda yake jikinta yasa hannu ta baya ya zuge zip din sannan ya cire mata,duk jiki ba kwari tanaso ta mishi magana Amma ina ta kasa,romancing dinta yake sosai har dukansu suka fara fita daga hayyacinsu yana nishi itama tana Wani irin nishi,
Wani ruwa me mahaukacin sanyi yaji an kwara masa a jikinsa ,Da alama bokiti dayane,Da sauri ya farka yana neman wanda ya musu wannan aika aikan,Sama'ila ya gani a tsakiyar kansa sai huci yake kamar tsohon zaki yace "kai ubanwa neh zai maka aikin yau daka kwanta tun dazu kanata shara uban bacci,koka manta a inda kakene,Dallah malam tashi ka tsaya ka tsareni Da wannan mayun idanunnan naka kamar na macizai" jiki ba kwari ya mike yana tunanin irin mafarkin Da yayi shi ba'abinda yafi bashi haushi irinna wannan baccin Da aka tashesa,saida yayi alwala yayi sallah sannnan ya fara aiki,shara yayi tatas sannan yabawa dabbobi abincin su ya kwashe kashi,Sama'ila neh yazo ya sameshi yace mishi ya shirya yau zai fara noma,sosai ya nuna masa yadda zai rinka yi,a ranar wuya iya wuya kwa yasha ta, harya fita daga hayyacinsa gabaki daya,abin tausayiLokacin da labari ya riski mommyn Imam ba karamin firgita tayi ba Da kuma rikecewa,takardar taketa kallo gashi kuma hand writing dinsa neh bana kowa bah,rasa ma abinda zatace tayi,friend dinta ta kira sannan ta fada mata abinda ya faru,ce mata tayi karta je itada kanta,ta baiwa driver dinda yasan garin sannan yasan gidansu yaje ya kai musu Amma kuma ba yanzu ba ta bari sai next week,amsa mata tayi Da toh kawai sannan ta kashe wayar,phone din Imam ta sake kira Amma shiru yaki shiga kasa ta sauka wajensu Abban Haiam don ta maida musu Da takardar,saida tazo kasa wani jiri ya ebe ta tafadi a kasa sumammiya,Da gudu sukayi kanta Amma inaa,ko numfashi batayi,hospital aka kaita duk wani taimako daya kamata an mata,Amma bata farka ba still,saida aka kira kwarrarun likito ci tukun aka samu aka ceci rayuwarta,alluran bacci aka mata sannan suka fito daga dakin,Abban Haiam Da yaketa zariya neh a wajen yana hango likitan yayi kansa,ce mishi yayi ya biyoshi office, "Gaskia Alhaji saide kuyi mata Addu'a Amma jininta yahau sosai muma dakyar muka ceto ranta sanann kuma dan kwananta Yana nan gaba neh Amma wallahi Da tuni saide kuji ance ta mutu yanzu de qanwar ka tana dauke da heart attack me qarfin gaske ma,akwai wani abinda yake damunta matuka sannan kuma ga Abubuwan Da suka mata yawa a zuciya,Amma ku kiyaye yanzu de saitayi kusan 2weeks sannan zamu sallame ta saide ayi hakuri,Tuni idon Abban haiam yayi jawur,yar kwanwarsa Da yake ji da ita duk dunia babu wanda yakeso irinta shine yau itace wai ta kamuda wannan mummunar cutar,magunguna aka hada musu sannan ya biya kudin komai ya tashi ya fito daga office din wajen Mammyn haiam yaje ya zauna sannan yake fada mata abinda sukayi da likitan sosai itama abin ya shiga ranta ba abinda take cewa sai Allah ya bata Lapiya,sannan kuma tace "Alhaji ba zama zakayi kana tunani ba Addu'a zamuyi ta mata har Allah ya kawo sauki,abinne ya zamar mata goma Da ashirin,ga saki,ga bacewar da,saide muce Allah ya kawo mana mafita
Sosai ta tsorata Da ganin mutanen sabida su kansu abin tsoro neh,daddy neh ya musu bayanin abinda zasuyi Da wanda zasu aiwatar,ana gama fada musu suka tintsire Da wani mugun daria kamarna shaytan,sannan yace "Tohm nawa zaka bamu" daria daddy yayi sannan yace "ai wannan ba komai bane a wajena idan har aiki zaiyu" suma darian sukayi sannan sukace "Zaka iya bamu 50million" Da sauri daddy ya zare ido yana kallonsu yace "Haba de yanzu kawai dan zakumin wannan abun shine saina bada 50mill" daya daga cikinsu neh ya tuntsure Da daria sannan yace "ku dallah ku sheme shi wannan wasa yazoyi ba gaske ba" jin hakane yasa daddy cewa "Ahh haba ai baza ayi haka bah,zan baku InshaAllah" haka deh suka gama tsara yadda abin zai kasance Zahra de dadi kamar ya kashe ta,suna tapiya a mota daddy yake cewa "zahra yanzu inazan samu wa'annan kudin,kinsan kuwa bazan iya bada wa'anann kudin ba sabida idanna basu kudadena sun zabtare " wani murmushi tayi sannan tace "haba daddy ,koka manta wanda nake aure,idan na auresa ba sai mu fanshi kudinmu ba" sai a lokacin ya tuna wani daria yayi sannan yace "Amma kuma wani hanzari ba gudu ba, ai kuma kudin ba nasa bane na babansa neh kokin manta?" Wani kallo tayi masa sannan tace "shima ba saimu saka akau dashi ba,kaga kuwa dole gado hannunsa zai dawo" shiru yayi yana girgiza kai alamar gamsuwa sannan yace "haka neh Amma kuma ai kudin hannun Imam zai koma" daria ta sakeyi sannan tace "shima sai a kauda shi" daria yayi sannan yace "Allah ya barmin ke Zahra,haka kuwa za'ayi Amma kuma kinsan kashe Alhaji Ibraheem ba abu bane me sauki koh,karki manta fah shugaban kasa yake nema kuma na tabbata saiya ci " itama ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juyo ta kallesa .
SUMIE London 💄👛