🌸🌺 FABEELAH 🌺🌸
🌺🌸 🌸🌺Dedicated to my people☺️❤️
Juma'at Mubarack to you all beautiful people 😻✨5️⃣3️⃣-5️⃣4️⃣
Zaune take a gindin murhu idanunta sai ruwa sukeyi,tanata faman fifita, "Fabee dan Allah ki hakura haka,nace ki bari Kande tazo tayi tunda kinga tunda kika dawo ba wani cikakken lapiya gareki ba,ya fada lokacin dake zuba ruwa cikin bokiti da alamu na dabbobine, murmushi tayi sannan tace "kai yayana,yanzu kullum ace Kande ceh zata rinka aiki kuma ni ina nan,ai kaga kuwa zataji kamar ba dadi,nama kusa gamawa fah,yanzu miya neh kawai yayi saura" ta qareshe maganar tana jan majina,ruwan ya dauka yayi hanyar wajen dabbobi dasu yana mai tausayama qanwar tasa,itama aikinta ta cigaba dayi,saida ta sauke tuwan ta malmala,sannan ta daura tukunyar miya,ba'a jima ba ta gama,dede lokacin data sauke kande ta shigo,Kayan hannunta ta sauke sannan ta karasa inda fabeela take "sannu da kokari fabeela,aida kin bari na dawo nayi,keda ba wani isasshen lahiya gareki ba,toh barshi nakai Kayan ciki" ta fada tareda durkusawa ta dauki robar da tuwan ke ciki,itade batace komai ba ,tukunyar miyar itama ta dauka ta shige ciki,kande ce ta fara ci don tasan ita fabeela ba yanzu ba saita jira Nura,ba'a dade ba ya shigo,tunda suka faracin abincin zuciyan ta ke tashi,yunkurin tashi tayi Amma Ina, tuni ta fara kwaranyo amai a wajen,sosai ta runka amai kamar Kayan cikinta zasu zubo,hankalin Nura idan yayi dubu ya tashi,cewa kande yayi ta debo ruwa,ruwan ya zuba mata yace ya kuskure baki,sannan ya gyara mata jikinta,ya dauketa cak ya kaita daki sannan yacewa kande ta gyara wajen,take zazzabi me zafi ya rufeta,maganin dayake batan ya dauko ya Kara bata,ba'a dade ba bacci ya kwashe ta,komawa yayi inda kande take shima ya zauna idanunsa sunyi jaa,hannunsa yasa ya dafe kansa, "Nura meke faruwa neh,ya jikin nata" kai kawai ya gyada mata alamar da sauki, "Allah ya qara sauki" tace sannan ta mike ta kwashe kwanukan takai kitchen sannan ta dawo ta zauna, "wai nura meke faruwa neh naga tunda fabeelah ta dawo ta dena wani walwala kamar yadda ta saba ada,kaima din naga ka canja?" Dagowa yayi ya kalle ta sannan yace "Kande mun taso cikin rashin uba,ba'a dade ba mahaifiyar mu ta bishi,mun taso cikin rayuwar kaskanta,bamuda kowa bamuda komai,bamusan inda yan uwanmu sukeba,munsha wahala a rayuwarmu,bamusan dadin rayuwa ba,haka rayuwa ta cigaba da tapiyar mana har takai ga na samu abunyi na saka fabee a makarantar masu kudi dukda bawai kudin gareni ba Amma zan farantawa fabeela inhar zataji dadi,ita kadai gareni nima kuma ni kadai gareta,matsowa tayi kusa dashi tace "Nura ka dena fadin haka ,wannan qaddara ceh daga Allah ,idan kana fadin haka sai Allah yaga kamar ka Gaza neh,haka Allah yaso ya ganku,bakasan wataran mezai faru ba ,bakasan wataran me wani a cikinku zai zama ba,abinda ya kamata kayi shine kullum ka kasance cikin yiwa iyayenku Addu'a,insha Allah zakana ganin ci gaba fiyeda yadda kake tunani a rayuwar ka,sannan kuma ka dena shiga irin wannan halin ka dauka Allah neh yaso ya ganku a haka,ka dauki komai ba komai bane,inba haka ba idan fabeelah tana ganinka a haka itama kullum zakana sakata cikin damuwa ,sabida kasan raunin mace dana miji ba daya ba,kayi hakuri nura wataran sai labarai,ka kasance mutum mai tawakkali,Allah yana kallonku kuma tabbas bazai manta daku ba yana sane daku kaji?" Maganganun da kande tai mishi neh yasa zuciyar sa tayi sanyi,hawayensa ya share sannan ya juyo suka cin gaba da hirarsu ta duniya har yake bata labarin abinda yasa fabeela ta dawo,bataji dadin abinda ya faru ba Amma sai tace mishi suyi hakuri duniya ceh,wataran sai labari
Yau ranar Friday wato ranar daurin auren Imam da Zahra,da kuma Haiam da Fadeel, saida aka fara daura na haiam sannan aka daura na zahra da Imam,lokacin da Zahra taji an daura harda kukan dadi saida tayi,mommy ceh tasa aka kira mata ita,fada ta mata sosai kamar yadda uwa takema danta,haiam kuwa ansha kuka duk shagalin bikin da ake ba'a son ranta akeba idan ta tuna da fabeela,Imam kuwa dashi akayi dinners dukda yanzu ya dena sakarwa zahra fuska,Amma ita bata damu ba a ganinta idan aka riga aka daura aure komai zai dedeta, yaune ranar da kowa zai watse, A falon daddyn haiam kuwa haiam ceh zaune a kasa mommyn ta da daddyn ta suna kan kujera sai kuma kannen mommyn ta da kuma kakarta wato mahaifiyar mamanta,fada suka mata sosai,kuka kam tashashi ana gama mata fadan mommyn ta taja hannunta zuwa dakinta,tsimi ta bata kala kala sannan ta shirya ta itada kanta sannan ta fito da ita zuwa falo,ba'a dade ba motocin daukan Amarya sukazo,mommyn Imam ceh da kanwar mom dinta suka kama hannunta aka wuce da ita.....Zahra kam tana zaune anata faman gyara jiki don gobene zasu wuce,a gidansu za'asha budiri,anan aka mata kunshi da komai har gyaran gashi da tsumin mata sabida tasan idan ta koma gida bai zama lallai Ammin ta tai mata bah,tana zaune a wajen harsu mommy suka dawo daga kai haiam Amarya,abinci ta bata tace takaima Imam,ansa tayi saida taje dakinta ta shirya cikin wani dogon riga sky blue me flower pink sannan ta wuce wajensa,lokacin data shiga yana toilet don haka ta samu waje ta zauna,fitowa yayi daure da karamin towel a kugunsa,bai lura akwai mutum a room dinba,har yaje gaban mirror ya hango ta ta mirror,ba qaramin tsorata yayi ba Amma saiya dake ya juya,yana juyawa suka hada ido,shi yama manta towel neh a jikinsa sai a lokacin ya lura,da sauri yayi hanyar toilet zai koma tayi sauri ta tashi tayi hugging dinsa ta baya,take tsigar jikinsa ya tashi, "ke bakida hankali neh,sakeni mana bakya ganin abinda ke jikina" hannunta ta sakalo ta qirjinsa tareda sauke wani numfashi har saida yaji iskarsa na ratsa fatarsa,sannan tace "habba my prince koka manta yau aka daura mana aure" idanuwansa ya lumshe a hankali sannan yace "wai mesa ke bakida kunya neh,ba mace kebin na miji bah ,na miji ne kebin na mace,irin kunyar nanda mata sukeyi ke mesa bakyayi" wani shu'umin murmushi ta saki sannan ta dawo gabansa ta tsaya tana kallonsa,suffarsa ba qaramin birgeta yayi ba,daman irin mazan da takeso kenan,yau Allah ya amsa mata Addu'ar ta,hannunta takai kan qirjinsa tafara zane kamar me zana wani abu,damke hannunta yayi sannan ya hankade ta ya shige toilet,jallabiyan daya bari dazu ya dauka yasa sannan ya fito,a wajen ya sameta ta hada kaida gwuiwa tana kuka,wuce ta yayi waje gaban mirror yayi abinda zaiyi sannan ya dawo kan wani kujera a dakin ya zauna,phone dinsa ya dauko,miss calls din mommy ya gani kusan 3 ,saida ya daga kai ya kalli zahra dake gefen gado a kasa tana kuka tukun,ce mata yayi tayi shiru please zaiyi picking call,Amma kamar tunzurata yake,mikewa yayi yaje inda take sannan yasa hannu ya mikar da ita, "please kiyi shiru kinji mommy ceh ke kirana zanyi picking call dinta" kukanta ya cigaba dayi har mommyn ta sake kira,ganin zai katse a karo na 5 neh yasa yayi sauri yayi picking sannan ya kara a kunne "mommy" ya fada taredasa dan yatsa akan bakinsa yana mata alama datai shiru "kana inane inata kira bakayi picking bah "eyya mommy Ina toilet bansan kinata kira ba ,phone dinne yana silent",..."okay daman i just want to ask na aiko zahra tun dazu da abinci kota kawo maka?" Murmushi yayi tareda kallon zahra wanda tun dazu taqi tayi shiru,yasan so take kawai ta hadashi da mommyn sa yace "yes mommy ta kawo min"... "okay tohm take care of yourself ka tabbatar kaci sosai kaji?" Okay yace mata yana sauri saurin ta kashe don baison taji kukan,harya kai hannu zai kashe "Imam" yaji ta kira sunanshi, zaro ido yayi ya sake kallon zahran yana mata alama datai shiru yace "na'am mommy" ....."kukan me naketaji tun dazu" sosa kai ya farayi kamar tana kallonsa yace "Ahhm mommy kuka kuma?",,,,"karka maidani karamar yarinya mana koba zahra ceh ke kuka ba" ,,,,"Eh eh mommy itace" ,,,,"mekayi mata Imam?,wai mesa kakeson neman bakina,yanzu adaura muku aure da yarinya yau yau dinnan shine harka fara sakata kuka" ,,,"Ayya mommy ban mata komai ba fah,faduwa tayi a toilet shine take kuka kuma tun dazu naketa bata hakuri taqi tayi shiru",,,,,"bani ita inji daga bakinta" rokonta ya farayi da hannu alamar ta rufa mishi asiri,maqe kafada tayi alamar A'a,da sauri ya kamota ya rungumeta yana shafa mata wuya,jin ya mata hakane ta ansa ta kara a kunne "mommy" ,,,"na'am Zahra,me yayi miki?" Dagowa tayi tana kallonsa,kara hugging dinta yayi sosai harda mata kiss a hannu "ba abinda yamin mommy",,,,"kar kiji tsoronsa zahra ki fadamin gaskia" ,,,,"Allah mommy faduwa nayi ",,,,"tohm shikenan Allah yayi muku Albarka kinji " "Amin" tace sannan ta katse wayar, sakin ta yayi zai tashi da sauri ta riko sa tareda turo baki tace "Allah zan kira mommy" jin tace zata kira mommy neh ya koma ya zauna,dagowa tayi tana kallonsa sannan tace "Please can you do me a favor" tabe baki yayi sannan yace "why not" Murmushi tayi sannan tace "please I like your lips,inaso kamin French kiss ta fada tareda kai hannunta kan lips dinsa, "ban iyaba, wai inama abincin da akace ki kawom... hade bakinsu tayi waje daya,kiss sosai take mishi,shi yama kasa kwace bakinsa sabida tsabar mamaki,wai dama Ana samun irin mata haka a duniya,tuni shima ya rikice jin irin sabon salon da take masa ,romance sukayi sosai,kamar an tsikaresa yayi sauri ya mike ya shige toilet ya barta kwance a wajen ,harya fito tana kwance,haushin kansa ya rinkaji na biye mata dayayi,abincinsa yaci sannan yayi sauri ya fice daga dakin,tana kallonsa yayi komai ya fice ta kasa tashi,jikinta gabaki daya ya mutu,zahra irin matan nanne masu matsanancin sha'awa ,dakyar ta iya mikewa ta shiga toilet
Washe gari tunda safe Imam yasa sale ya rakashi airport,ticket yaje ya sauya da wanda mommy ta musu tun farko sannan ya koma gida,kai tsaye dakin fabeelah ya wuce yana shiga ya bude wardrobe dinta kayanta ya gani wanda tazo dasu da wanda aka dinka mata anan,take yaji wani sabon sonta na sake shigarsa,juyawar dazaiyi ya hango phone dinta a ajiye da sauri yaje ya dauko saida yayi kissing phone din sannan yasa aljihu,phone dinda Moha ya siya mata ya gani,take annurin face dinsa ya dauke,hotonta dake rataye a bangon dakin itada haiam wanda aka musu na biki ya ciro,kallon picture din ya tsaya yanayi ,sai a lokacin yaji labarin da haiam ta bashi ya dawo mishi sabo, kallonta ya cigaba dayi,daria yana mata kyau ya fada a fili, "I LOVE YOU Fabeelah" ya fada lokacin da yake hugging hoton,kamar ance ya kalli wani waje,pictures din bikin yagani wanda aka dauka ranar dinner,hotonsu neh a farko shida ita wanda Photographer dinnan ya dage saiya daukesu,ba qaramin kyau sukayi ba,shi kanshi sai yanzu yake gasgata zancen Photographer din ta yake cewa sun dace,dukda ko wanne a cikinsu ba wani maida hankali yayi Akan hotonba,wani picture din ya sake gani nasu lokacin da fabee take rawa a stage shi kuma ya tsaya yana kallonta,hoton ba karamin kyau yayi ba ,duk hotunansu ya tattara wanda suka san an musu da wanda basu sani ba,sannan ya fice daga dakin,saida kowa ya watse kafin suma suka fito,airport sukace gaba daya ,dakyar aka banbare zahra daga wajensa ,harda kukan munafurci,shikam haushi ya cikashi ji yake kamar ya mangareta Amma idan ya tuna wani abu sai yaji zuciyarsa washar,su mommy kam se hakuri ake bata acewarsu kwana nawa neh zasu zauna tareda shi har abada,tayi hakuri,jirginsu suka shima harya tashi,sai daga baya su Imam ma nasu ya kusa tashi harsun shiga jirgi,tun kafin su shiga mommy take jin ishir ruwa din haka ba musu yaje ya samo mata,suna shiga jirginsu ba'a dade ba kuwa ya tashi.
SAI ABUJA😀SUMIE London 💄👛