UKU-BALA'I=16

793 30 0
                                    

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA GOMA SHA SHIDA.
Juyi kawai yake yi kan kafcecen gadon sa yana faman kai komo da zuciyarsa da ta hana idanuwansa barci ko na yan mintina ne yayi iya yin sa amma abun ya ci tura sosai yake ganin komai na dawo masa kamar yanzu fuskarsa yake hangowa tana yi masa shawagi a cikin idanuwansa in ya rintse guntun murmushin da ta sakar masa a waccan lokacin yake hangowa na yi masa barazana sosai yayi nisa cikin tarkon ta da yake tsammanin ta ɗana masa ba wai aiki kawai ta zo nema kamfanin sa na AFC ba har da da faraunatar zuciyarsa wacce cikin dakiku ta zabare masa ita ta tafi da ita bai sai hakan ya afku ba sai cikin wannan sulusun daren wanda ya dace ace yana kwance yana barci domin baiwa zuciya da gangar jiki hutu amma ina! hakan ya gagara.
A hankali ya kai hannunsa wajan makunnin wutar dakin ya kunna haske ya gauraye dakin agogonsa kirar Rolex da ke ajje saman yar karamar dirowa dake girki gefen gadonsa ya dauko ya duba karfe 3:15am. ya nuna masa sosai ya ware idanunsa yana jin yarda kirjinsa ya buga kadan maidawa yayi ya ajje sannan ya juya gefen hannunsa na hagu kafun ya dan tashi kadan ya jingina da fuskar gadon sosai hannu bibbiyu ya tallaɓe haɓarsa abun duniya yake ji duk ya addabar masa rayuwa ya surkutar dashi cikin yan awanni da ba su haura goma sha tara bs komai ganinsa yake yi kamar wanda akayi shekara goma sha tara kafun ya tabbata sosai yake jin wani iri a duk wani sassa na jikinsa da zuciyarsa sosai yake hangowa kansa tashin hankali in har abin da zuciyarsa ke sanar dashi bai tabbata ba sosai yake ganin komai zai iya faru in har Areefa Saif ba ta bashi dama ba.
Zuciyarsa yaji ta fara yo masa kuwwa da zancen amincewa daga bangaren Areefa tana mai sanar dashi in dai da kudi komai zai kasance kamar yarda ya fuskanci ita kanta Areefa din zata so jindadi da hutu kamar yarda hakan ya nuna ba tare da yaji daga gareta ba. Ba ya zaton zai samu matsala in dai ta bangaren kudi ne  tabbas za suyi masa abin da yake so kuma a lokacin da yake so ko tattama ba zai yi ba yana da kudi yana da kadara wacce zai iye sayr zuciyar Areefa da komai nata da ta mallaka ya zama dole ta yarda dashi ya zama dole ma ta amshi bukatarshi hannu bibbiyu ba tare da tsaya yawo da hankalin sa ba.
Gyaɗa kai ya shiga yi yana hada hannayensa waje daya yana lakwasasu suna ba da wani sauti mai amsawa sosai yake sakin murmushi mai karfi a fuskarsa sosai yake jin wani farinciki na samun gurbi a filin zuciyarsa sosai yake hango amincewar abin da yake bukata daga Areefa sosai yake ganin yarda ta amshi bukatarsa cikin lokaci kalilan ba tare da ya samu wata tangarɗa ba gareta.
A hankali ya koma ya kwanta yana kai hannunsa wajan makunnin wutar yana kashewa rufe idanunwansa yayi har lokacin fuskarsa bata rabu da murmushin da yake yi ba sosai yake hango Areefa a wannan lokacin tana yi masa shawagi a duniyar idanuwansa da suke rufe sosai yake hango wani tattausar murmushi na samun gurbin zama a fuskarta tana jefa masa wani kallo wanda yake kara rugurguza duk wani sashi na filin zuciyarsa yana jin yarda wani abu mai girman gaske yana wanzar da mazauni a filin zuciyarsa ta shi, sosai yake ganin rashin samun Areefa tamkar rasa rayuwarsa sane da duk wani buri da kudiri nasa da ya kafa akanta gani yake yi in har ya rasa abin da yake bukata a gareta tamkar yayi wa rayuwarsa babban gibi ne wanda ba ya tsammanin yana da abin da zai cike masa wannan gibin.
Cikin wannan yanayi barci barawo ya zo yayi awon gaba dashi ya jefashi wata duniya mai dauke da Areefa a cikinta...
****
A hankali ya shiga rage sautin wakar 'Don't Judge Me' ta Chris Brown dake tashi cikin sifukun motar wayarsa dake hannunsa ya shiga latsawa a yan sakanni ya kai ta zuwa kunnansa yana faman jan numfashi kamar wanda yayi gudun tsira sosai fuskarsa ke bayyanar da halin da yake ciki na damuwa sosai kunci ke wanzuwa a fuskarsa da kwayar idanuwansa.
Laɓɓansa yake turawa cikin bakinsa ya na cizawa kamar ba a jikinsa suke ba sosai yake jin wani irin yanayi da zuciyarsa take haifar masa a duk sakan daya na jan numfashinsa.
A hankali ya sauke wayar fuskar na kara ya mutsayewa cikin yanayi na damuwa da rashin abin yi sosai yake jin komai na kwance masa sosai yake jin lissafin kwanyarsa na wargajewa cikin yan dakiku bai san abin da ya dace yayi ba, bai san me nene ya kamata ace yayi ba a daidai wannan lokacin ba yana bukatar mataimaki yana bukatar wanda zai tayashi zaman jajen zuciyarsa daga halin kuncin da take ciki...
Kamar wanda aka zungura da sauri ya sake dauko wayar da ya ajje gefe cikin yan dakiku ya kai ta kunnansa bayan ya binciko lambar da zai kira.
A hankali yake jan numfashi yana motsa laɓɓansa zuciyarsa yake jin tana wani irin mataki da ya tabbata gaf take da kamuwa da cuta mai girma gareshi dama gabadaya gangar jikinsa.
"Khairiyya...".
Ya fadi cikin wani irin sauti mai rauni sosai a hankali ya sanya hannunsa daya yana dafe kansa da yake jin yana kokari wargajewa.
Yana jin yarda numfashinta ke sama da kasa daga bangarenta sosai yake so ya fahimci wani abu cikin yanayin da take ciki zuciyarsa ta cilla shi wata duniyar tunani ya shiga nazarin yanayin da yaji Khairiyya sosai zuciyarsa take sanar dashi wani abu na daban da bai yi tsammani ba.
Girgiza kai yayi cikin yanayi na kin yarda da zancen zucin nasa kafun ya nisa cikin yanayi na damuwar zucci.
"Ban san mai nayi miki ba kika gujeni tsayin kwanaki Khairiyya, tun da nake dake daidai da kwana daya ba mu taba kin sa junanmu a idanuwanmu ba, amma cikin wannan lokacin gabadaya na lura sauyawa kike yi me yasa?".
Ya ida muryarshi da sanyi a cikinta sosai yayi shiru yana jiran tsammani daga bangaren ta amma shiru kusan mintina biyu a hankali ya sauke wayar yana duba screen amma ba alamun yankewar wayar har yanzu akan kira take.
"Uhmm...".
Ya kokarta nisawa domin tunatar da ita yana kan layi in mantawa tayi take wata sabgar ta daban.
Jan numfashi yaji tayi mai karfi kafun ta fara magana da wata murya wanda da ka jita zaka gane akwai abin da ke damun mai muryar.
"Huzaif...".
Ta fadi da sauti kafun ta sake jan numfashi ta dora.
"Bakomai kawai dai...kawai gani nayi kana bukatar a baka fili a duniyar rayuwarka domin daidaita halin da kake ciki na damuwa...".
Da sauri ya tare ta.
"Haba mana Khairiyya wacce irin magana ce kike yi haka wanda sam bata dace ace ta fito daga gareki ba".
Ya karashe yana mai jan numfashi sosai ya hasaso wani abu mai kama da bacin rai a cikin kalamanta sosai ya fahimci akwai abin da ke dawainiya da ita a zuciyarta.
"Yi Hakuri...".
"Huzaif!".
Ta fadi da sautin murya mai nuna da bata so abin da yace ba.
"me kayi mani kake bani hakuri, wanda ni ban sani ba?".
"Ban ce nayi miki wani abu ba amma kuma muryarki ta fallasa asirin zuciyarki da halin da kike ciki".
Yana jin yarda ta saki numfashi mai karfi kafun yaji maganarta ta doki dodon kunnuwansa.
"bana gari nayi tafiya kuma gaskiya ban san ran dawowa nan kurkusa ba...".
Bai bari ta ida batun nata ba ya tare da sauri.
"What! me kike nufi Khairiyya kin yi tafiya ba tare da na sani ba mai haka ke nufi shin kin manta halin da nake ciki kuma kin san ina bukatar taimako daga gareki amma ki kayi min haka Well..shikenan..shikenan".
Ya karashe cikin wani irin yanayi mai sanya daci akan harshe da zuciya
Ita kan ta haushin nr cinkoshe a zuciyarta take faman kokawa dashi kar ya kufce ya yo waje domin ta tabbata komai zata iya gayawa Huzaif akan bacin rai da cin kashin da yayi mata. Sosai take jin bacin rai da takaici wanda ta hakikance haka a matsayin raini tsagwaron sa da rashin sanin darajar ta.
Alkawari tayi sai ta bashi mamaki sai ta nuna masa asalin wacece ita sai ta ganar dashi 'YA MACE irin ta ba kowa yake dauka ya wulakanta ba sai ta nuna masa suma 'YA'YA MATA akwai daraja garesu ba wai ledar pure water bace duk in da ka gilma zaka tsince ta kuma ka zabi wanda tayi maka.
"Sai Anjima!".
Ta fadi a zafafe gami da kashe wayar bakidaya.
Sakato yayi da baki bayan ya sauke wayar ya kafe Screen din da kallo wani abu yaji yanayi masa yawo akai ji yake yi duniyar na juyawa dashi a hankali komai na kwancewa akansa runtse idanu yayi mamaki ne da tu'aji yake kunno wa daga zuciyarsa sosai  yake ganin kamar a mafarki wai Khairiyya ce tayi masa haka ita ce take fada masa magana cikin bacin rai abin da tun da suke da ita bata taba yi masa ba sosai take nuna kulawa da tattali gare shi amma a yanzu lokaci guda komai ya wargaje.
Gyaɗa kai ya shiga yi yana hango rashin sa'a rayuwarsa wanda ƙaddara ta kinkimo ta kawo masa lokaci guda kuma take kokarin tarwatsa komai na ginin rayuwarsa da yayi a baya mai cike da kayan kwanciyar hankali da jindadi.
Sosai ya jima cikin shiru hannayensa rungume da kansa zuciyarsa sai faman harbawa take yi da wani irin yanayi wanda ke kara hargitsa masa tunanin kwanyarsa sosai ya fuskanci rayuwarsa gaf take da tarwartsewa koma yace ya tarwatse domin kuwa shi dai bai ga amfanin haduwa da wannan yarinyar ba wacce ta dagula masa lissafi da komai nashi kuma take kokarin zautar dashi bai san abin da ya dace yayi mata ba bai san mai ya kamata ace yayi akan ta ba domin daidaituwar komai nasa sosai yake kasa aiwatar da niyyarsa gami da kudirinsa akan ta bai san mai yasa hakan na tunaninsa ya zama abokin sa a kowani lokaci dare rana dama cikin barcinsa ba wanda hakan ba karamin tashin hankali yake shigar dashi ba sosai ya fuskanci yarinyar ta samu gurbi a filin zuciyarsa tayi kane-kane ta hana zuciyarsa sak! da ruhinsa sosai take haifarsa masa da wani ciwo mai girman gaske a duk wani sashi na zuciyar tashi har da kasan ruhinsa.
Numfashi yaja mai karfi kafin ya kai hannunsa saitin kirjinsa inda yake tsammanin nan ne zuciyarsa take girke wani irin bugu takeyi a hankali a hankali wanda hakan ya tabbatar masa ta kamu da ciwo mai tsanani har yake kokarin sumar da ita.
Girgiza kai ya shiga yi yana jin yarda idanuwansa suke kokarin tara wani abu cikinsu wanda ko shakka ba yayi hawaye ne wanda shi kan sa bai san ya akayi har hakan take kokarin faruwa da shi ba da sauri ya sauke hannunsa yayi wa motarsa Key gami da kure karar sautin sifukun cikin motar yayi hakan ne ko zai samu sa'ida da saukin tunanin zuciyarsa sosai ya fizgi motar kamar zai tashi sama.
*****
A hankali yake tafiya yana jin yarda kafafuwansa ke wata irin karkawa kamar za su fice daga jikinsa sosai ya ke jin tashin hankalin da zuciyarsa take hakilo akai kamar zai tarwatsa masa kirji sosai yake jin lissafin tunaninsa na kwanya na kara wargajewa.
Bai san mai zai yi ba bai san abin da zuciyarsa take kokarin tunkuɗa shi yayi ba sosai ya barwa zuciyarsa gangar jikinsa take sarrafawa.
"Yaa Allah!".
Abin da ya fadi kenan a wahale kafun ya buɗe idanuwansa da yake jin su tamkar wanda aka daura musu wani abu mai girma sosai sun  kaɗa suyi jajir.
Mutum ya gani tsaye yana kallonsa sosai fuskrsa na bayyanar da wani irin yanayi wanda shi ya kasa fahimta shima kallonsa yake yi da duk ganinsa sosai yake jin zuciyarsa tana sanar dashi ya san shi ya taba ganinsa ko ba ma a zahirance ba zai iya kasancewa a cikin mafarki sosai ya cigaba da ware idanuwansa akan sa yana karaton a inda ya san shi lokaci guda zuciyarsa ta canko masa.
Tabbas ya san shi sun taba haduwa kuma ko shakka ba yayi cikin asibitin nan ne suka hadu kwanakin baya can gyaɗa kai yayi kafun ya dan kauce gefe har lokacin idanuwan Dr.Aqeel na kansa sosai yake kallonsa yana karantar yanayin da yake yana kallonsa a ciki sosai ya fuskaci ba cikin hayyacinsa yake ba akwai abinda yake dawainiya dashi wanda ya kasance ba mai sauki ba ne.
Daga kafada yayi kafun ya gyaɗa kai alamun ko a jikinsa a hankali ya fara taku kan kafafuwansa yana jin wani abu na samun gurbi azuciyarsa akan Huzaif sosai yake jin abu sosai yake jin gabansa na bugawa a hankali ya tsaya da tafiyar da yake yi ya waigo ya sauke kallonsa kan Huzaif har yanzu yana yarda ya bar shi sai hannu da yaga ya saka cikin sumar kansa yana cakuɗawa.
Sosai Dr.Aqeel ke jin Huzaif bai kwanta masa azuciya ba sosai yake jin wani abu daban game dashi sosai yake jin abu mai girma na samun masauki game dashi tsaki ya dan ja kadan yana mai tsuke fuska, hada idanu sukayi tsakaninsu wani irin kallone ya sarke a idanuwansu kallo na rashin fahimta kallo ne na ba kayi  mani ba.
Da sauri Dr.Aqeel ya janye idanuwansa a dan haryarce yayi hanyar Get din domin fita yana TUFKA DA WARWARA game da Huzaif sosai yake jin hankalinsa bai kwanta dashi ba...
"Yah Dr.Aqeel".
Kamar daga sama yaji muryarta na fadin haka ko bai ma dauki muryar ba mace daya ce ya sani ta na ambatar sa da wannan sunan a hankali ya lumshe idanunwa yana buɗe su kanta yana ware idanuwansa sosai lokaci guda ya jefa tunanin da yake yi a kwandon shara ya sanyawa fuskarsa murmushi mai karfi hannayensa ya sarke a kirjinsa yana jiran karasowarta fuskarta ita ma da murmushi numfashi taja lokacin da ta iso gareshi.
"Daga ina kike Mariya?".
Ya fadi yana mai tsare ta da idanu da alamun tuhuma.
Gyaɗa kai tayi kafun ta numfasa tayi kasa da kai.
"Umma ce take bukatar wannan".
Ta fadi tana mai nuna masa bakar ledar dake hannunta dauke da kankana da ayaba.
Ware idanu yayi kafun ya gyada kai
"Naje dakin ai bakya nan ita kuma ta zaga bandaki ganin ki da banyi a dakin ba shi yasa ma na fito waje".
Ware idanu tayi tana murmushi.
"Sai kace wacce za a sace shine ka biyo sahu".
"Uhmm Mariya kin ga wuce muje ciki nan ai a hanya muke ko".
Ya fadi yana mai kafeta da ido ba ta ce da shi komai ba suka fara takawa yana gaba tana biye dashi a baya sosai take kallon yarda yake tafiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa lokaci guda ta dubi kanta sai taji wani iri a zuciyarta yanayin shi da ita sun bambanta sosai.
Sosai hankalin ta yayi nisa wajan kallon Dr.Aqeel tana tunanin yarda har ya amince ya shigo  rayuwarta a yarda take wanda take ganin rashin dacewar haka kamar akwai nakasu a tarayyar sosai...
Ba ta kai ga gama lissafin tunanin ta ba kamar ance ta daga kanta wa zata gani da sauri taja da baya tana Ambaton Allah idanuwanta a warwaje wani irin bugu taji kirjinta yayi har sai da ta kai hannunta ta dafe rintse ido take yi gani take kamar a mafarki ba gaske ba sosai tsoro da wani irin yanayi yake bayyana a jikinta sosai take jin wani abu mai girma na saukar mata a zuciyarsa sosai taji zuciyarta ta ta shiga tsalle cikin wani irin yanayi wanda ta rasa a mizanin da za ta ajje shi ba abin da ke mata yawo aka sai sautin marin da tayi masa a can baya gani take kamar yanzu komai ya afku sosai taji ranta na baci da wani irin abu mai girma a hankali ta buɗe idanuwanta tana sauke su akansa sosai ta hango yarda idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir sosai take hango wani abu mai kama da tashin hankali cikin idanuwansa gabadaya take ganin yanayinsa a firgice yake sosai take hango yarda ya sauya ba kamar da ba yarda ta ganni sosai ta hango rauni mai girma a tattare dashi ba tare da jarumatar da ta san shi da ita ba
"Yaa Allah!".
Ta furta cikin karfin hali domin ji take komai yana wargaje mata na tunaninta sosai take jin wani abu na yawata mata cikin gangar jikinta gami da zuciya da ruhi wanda ta kasa gane menene haka din.
A hankali ta fara kokarin taks kafafuwanta da take jin sun sunyi mata nauyi sosai ji take kamar dutsen dala aka daura mata numfashi take ja yana kufce mata sosai tayi kokarin jan kafarta har ta iso in yake jingine jikin motarsa tana kokarin gifta shi kamar sautin muryarshi taji ya ambaci sunanta da sauri ta waiga ta sauke masa idanuwanta shima ita yake kallo da wani yanayi wanda ta kasa fassara ko na mene ne abu mai nauyi da girma ta ke hangowa cikin idanuwansa wanda hakan ba karamin narkar mata da jiki yake yi ba gabadaya taji tunanin kwanyarta na wargajewa.
Muryar Dr.Aqeel ta jiyo kamar daga sama hakan ya farfado da ita daga sumar da take tsammanin tayi sosai ta dago kanta ta dube in da yake dan nesa da ita tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa wani kallo taga yana yawatawa dashi a kanta wanda hakan ya kara firgitata sosai da sauri tayi kasa da kai kafun  ta dago ta dubi Huzaif wanda ya gama zama kalar tausayi wani kallo ta watsa masa wanda ita kanta ba ta san ya akayi tayi masa shi ba.
A hankali ta fara takawa kafafuwanta na rawa sosai abu mai girma take jin ya danne mata zuciya yana kara luguiguita mata da gangar jiki da ruhi kanta a kasa ta isa wajan Dr.Aqeel wanda take jin kallon da yake watsa mata kamar ana watsa mata garwashi wuta.
"Waye waccan?".
Taji muryarsa ta ambata da wani irin yanayi wanda ta tabbata bacin rai ne a cikinta sosai da sosai ba ta san mai zata ce masa ba bata san wata irin amsa ya dace ta ba shi ba sosai ta fuskanci yana cikin yanayin bacin rai wanda ta rasa mai yasa hakan ya bayyana shin ko dai ya san Huzaif ne ko dai ya san wanene shi.
Tambayoyin da su dinga mata shawagi kenan cikin kwanya suna kara haifar mata da tashin hankali mai girman gaske.
"Dake fa nake Mariya kika yi shiru wanene waccan kin san shi ne?".
Sosai taji muryarsa ta kara buɗewa da sautin fushi a cikinta wani kaɗawa taji cikinta yayi ba ta taba zaton akwai ranar da za taji muryarsa haka ba bata taba zaton akwai ranar da zata ji magana irin haka mai dauke da daci a cikin ta ba girgiza kai ta shiga yi a hankali kafun ta kokarta jan numfashi.
"Ban san shi ba kawai dai...".
"Kawai dai me?".
Ya tare ta da sauri har lokacin muryarsa ba ta canza ta koma yarda ta santa ba.
Wani karfi taji ya zo mata cikin zuciya da sauri ta dago idanuwanta a rintse ta sauke su saitin Dr.Aqeel kafun ta juya ta kalli inda Huzaif yake tsaye har yanzu tana hango irin tashin hankalin da yake ciki.
"Gani nayi kamar yans cikin Matsala  sosai naga haka a idanunsa shiyasa na ji ba dadi...".
Ba wai don ya yarda da maganar ta bane dari bisa dari domin zuciyarsa taki yarda da abin da yake gani jan numfashi yayi mai tauri yana kokari ajje maganar tata a zuciyarsa yana yarda da cewa ita  ta hango tashin hankali game dashi ne shiyasa ta nuna jajantawa gareshi duban Huzaifa yayi daga inda yake tsaye yana hango tashin hankalin da yake ciki idanunsa sosai ya fuskanci wani abu cikin Maganar Mariya kuma zuciyarsa na karyata abin da yake zargi ba tare da yace da ita kala ba ya juya ya cigaba da tafiya jan numfashi tayi ita ma tana sake kallon Huzaif kafun ta kau da kai hadi da hadiye wani abu mai girma da ya tsaya mata a wuya ta daga kafafunta ta bi bayan Dr.Aqeel zuciyar cunkushe da abubuwa ma bambanta wanda ta kasa gane in da suka sanya gaba..

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now