64=UKU-BALA'I

422 32 4
                                    

Duban idanuwanta yake yi dauke da wani irin yanayi mai taba zuciyar masoya wanda suka tsumu cikin kugin soyayya da kaunar juna fuskarsa sai kara yalwatuwa take yi da murmushi mai girman gaske janye idanuwansa yayi lokaci guda yana mai da numfashi kafun ya motsa laɓɓansa.

"Mariya kin yi shiru baki ce komai".

Murmushi ita ma tayi gami da tura dan yatsanta guda cikin baki kafun ta shiga kokarin magana.

"Duniyarnan a yanzu jin ta nake kamar ba wanda ya kai ni farinciki a cikinta".

Cikin mamaki da tuhuma yake dubanta jin abin da tace dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani iri yanayi musamman yarda ya ga ta saki jiki dashi yau rana daya tana dariya gami da murmushin da yake kokarin hallaka masa zuciya.

"me ke faruwa ne Preety? da alamun zuciyoyi sun kusan barin kunci zuwa farinciki".

Runtse idanu tayi gami da buɗe su sosai akan sa kafun ta juya ta kalli kofar gidansu.

"Mahaifina ya dawo".

Zare idanu yayi cikin mamaki da kuma al'ajabi bakin sa yake motsawa yana son yin magana amma ya kasa wani farinciki ya ke jin kansa a ciki a daidai wannan lokaci da bai taba

tsammani ba lokaci guda yaji kamar an watsa shi cikin aljanna don farin cikin da sauri ya kara takowa zuwa gareta kamar zai hade jikinsa da nata da sauri ta ja baya da murmushi afuskarta.

"Are you Seriuos?".

   Ya fadi yana mai tallaɓe haɓarsa sai faman zabga murmushi yake yi gyaɗa masa kai tayi da sauri ya juya yana kokarin tunkarar kofar gidan da sauri ta daga masa hannu tana mai sanya idanuwanta cikin nasa.

"Me kenan kake kokarin yi?".

"Oh God! don Allah ki bar ni naje na gan shi kin ji kuwa yarda zuciyata take farin ciki kin ji irin dadin da nake ji a wannan ranar sosai nake jina a wani mataki mai girma wanda na jima ban shige shi ba ZUCIYARMU DAYA ne ni dake abu daya muka zama dole na tayaki farinciki dole na nuna kauna ga yanayin da kike ciki ayanzu".

   Yana gama fadin haka ya riko hannayenta ya fara kokarin janta da sauri ta fizge tana dubansa lokaci guda ta daure fuska tamau kamar ba ita bace mai dariya da farinciki yanzu idanuwanta take amfani da su tana tura masa hukuncin kuskuren da yayi a yanzu abin da ta tsana abin da bata so shine yau yayi mata tana soron irin wannan yanayin sam bata so ko

numfashi suna hadawa da ɗa namiji domin kuwa sosai ta tsorata dashi musamman ganin halin da Hafsat ta shiga A DALILIN ƊA NAMIJI duk da dai ita har da yardarta da amincewarta domin ba yarda za ayi namiji ya saka mace yin abu dole ba tare da amincewarta.

  Sosai ya gane yayi kuskure sosai yake jin kallon da take masa yana bula masa jiki yana yanke masa hukunci mai girma runtse idanu yayi ganin yarda fuskar tata ta sauya a lokaci guda.

"Kiyi hakuri Mariya hakan ba halina bane ban yi da wata manufa ba dokin farincikin ki ne shi ya je fani a wannan matakin da na so aikata kuskure mafi girma a gareki".

   Kau da kanta tayi batare da ta ce dashi kala ba ta fara tafiya domin komawa cikin gida shi kansa ya tsorota sosai ganin yanayin da take ciki a hankali ya fara bin ta a baya tana jin ta kunsa amma tayi banza dashi domin kuwa sai ta nuna masa kuskurensa ko da kuwa ba da gangan yayi ba.

UKU BALA'I (Completed)Onde histórias criam vida. Descubra agora