50=UKU-BALA'I

382 18 0
                                    

A hankali take duban Hajiya Layla gabanta na sake tsananta faduwa duban mutumin dake zaune gefe guda tayi sannan ta kalli dubun nan kudin da suke ajje cikin leda wani irin kartawa taji zuciyarta tayi da wani irin yanayi mai zafi da raɗaɗi ji take yi kamar ta hadiyi zuciya ta mace.

Sosai ta ke jin komai na canza mata sosai take jin zuciyarta na sake yayyagewa da tashin hankali wanda bata yi tsammani zata kasa daukarshi ba tayi tunanin zuciyarta zata bata dama har ta ga kullewar wannan lamarin amma ina! ba zata iya ba da sauri ta fara ja da baya idanuwanta na rinewa da tashin hankali kafun ta juya da gudu tayi cikin dakinta.

Hajiya Layla da tun dazu take kallon Areefa zuciyarta na tausayinta ta sani tabbas dole Areefa taji ba dadi amma ba yarda zatayi dole wannan hanyar ta kasance mafita a gareshi su ita ce kawai take hango komai zai zama daidai bata tare da an samu matsala ba nisawa tayi sannan ta dube shi da fuska cikin damuwa.

"Yanzu ya kukayi da su mutanan da suka zo neman Aure?".

Murmushi ya saki tare da gyara zama sosai yana fuskartarta kafun ya ja numfashi.

"Ai Hajiya ba wata matsala duk yarda kika ce ayi haka akayi sati biyun nan dai masu zuwa za a daura auren kamar yarda kika bukata su ma ba su ja ba".

Murmushi tayi wanda iyakarsa laɓɓan bakin ta kafun ta janyo jakarta dake gefe ta zuge zip din kudi ta zaro ta mika masa kafun tace.

"Ga wannan sai ku fara saye-saye wanda ka san gidan biki na bukata sannan duk wani abu zan turo muku dashi wanda zai tabbatar da cewa eh bikin na gaske ne".

Gyaɗa kai yayi yana ansar kudin goɗiya yashiga zabga mata kafun ya mike ya fice daga cikin gidan.

Sai lokacin Hajiya Layla ta samu tayi ajiyar zuciya mai karfi a hankali ta mike ta dauki ledar da kudin suke ciki zuciyarta na mikata wani mataki na tausayin Areefa a haka har ta isa cikin dakin ruf! da ciki ta hangeta ta hade fuskarta da filo a hankali ta taka ta isa gareta bakin gadon ta zauna bayan ta ajje kudin gefe guda.

Duban Areefa ta shiga yi wacce ta tabbatar taji shigowarta a hankali ta kai hannunta saitin bayan ta tana bubbugawa kadan-kadan kafun ta shiga cewa.

"Areefa mai yasa zaki yi mani haka bayan kin min alkawarin ba zaki sake nuna wani damuwa kan lamarin nan ba karki manta ba wai nayi niyyar yin wannan abun bane don cutar dake a,a nayi ne don ƙwatar miki yancin ki wanda na tabbata in komai ya kammala ke akaran kanki zaki yi farin cikin haka".

A hankali Areefa ta dago tana zama idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir sai faman cizon laɓɓa take tana dakune fuska.

"Farin ciki fa kika ce Maama kina tunanin a duniyar nan zan sake samun farinciki ne kina tunanin farincikin da ya guje mani zai sake dawowa gareni ne a filin rayuwar ta bana tsammanin haka zai kasance na sani rayuwata ba komai bane a duniyar nan bana tunanin a rayuwata farinciki zai wanzu...".

Numfashi taja da taji yana sarke mata wasu kwalla masu zafin gaske suka zubo mata saman kuncinta hannu ta saka ta dauke su kafun ta shiga girgiza kai.

"Ban san ya zan fuskanci wannan rayuwar ba kawai ina yin ta ne ba wai don farinciki ko kwanciyar hankali ba dama can Allah ya halicce ni a haka zan kare rayuwa ta cikin kunci da takaici da rashin 'yanci na lura a duniyar nan in har baka da

makusanci to kai ba ka da wata daraja ko kima da za a ganka da ita kai da banza duk daya ne....Maraya shima mutum ne kamar kowa yana da 'yanci a wajan ubangijinsa ko bai dashi a idon jama'ar duniya bani nayi wa kaina haka ba ba a son raina na zo a wannan yanayin ba amma saboda rashin 'yanci da sanin daraja ta aka lalata min rayuwata aka kashe mani duk wani hanyar da zan samu

UKU BALA'I (Completed)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin