31=UKU-BALA'I

495 50 1
                                    

Tsaye tayi ki kam!. tana faman yatsine fuskarta da cizon laɓɓanta sai faman ajiyar numfashi take kamar wacce tayi Gudun ceto rai.

"Ni wallahi gabadaya na gaji".

Ta fadi tana mai jingina da bishiyar dogon yaron dake bakin hanyar da zata fiddo su daga cikin surkuk'in dajin da suke. kallo daya za kayi wa wajan ka tsoro ta sosai musamman in ka kasance mai karyayyiyar zuciya in aka ce ka shigo wajan ko da kudi ne ba zaka shigo ba daji ne sosai mai dauke da surkuk'in ciyayi da dogayen bishiyu kamar su sukayi kansu ga wasu gingima-gingiman duwatsu suma abin dai na tsoro gashi nan ba kajin kukan komai sai na gyare da tsintsaye.

Tsaya tayi da tafiyar da take yi jin abin da Hafsi ta fadi ta juyo kallo daya zakayi mata ka gane itama ba karamin gajiya tayi ba sai faman numfarfashi take yi jin jikinta take kamar wacce akayi wa dukan kawo wuka.

"Ke kam kin fiye tsirfa wallahi ni ban ce na gaji ba sai ke mai jikin kuruciya kai jama'a ke dai kam anyi ranguwa wallahi Hafsi".

Sake turo baki tayi gaba tana kokarin zama gindin bishiyar.

"Haba mana Goggo Marka ki dubi uwar tafiyar da muka dauko fa aiko akan abun hawa muke wallahi sai mun gaji ga kuma fargaba da tsoro ki dubi dajin nan fa ki gani ba kowa bane zai iya shigarsa ko ni dai na shiga a tsakanin rayuwa ko mutuwa wallahi ban ma yi tunanin zan fito ba don tuni na fara dankaro salati a bakina...".

Cak! ta tsaya da maganar da take hango maciji tayi saman jikin bishiyar da take jingine wata irin

razananniyar kara ta saki idanuwa warware Goggo Marka dake rike da kugu jin ihun Hafsi ya sanya Goggo Marka shekawa da gudu tana tsalle tsalle kamar wacce abu ke biwa kafa dama tuni a tsorace take tun da suka shigo cikin dajin gabanta ke faman dukan luguɗe.

Ihun Da Hafsi ta cigaba da yi ne ya sanyata tsayawa can gefe tana faman numfarfashi tana bin ko ina da kallo
.
"Ke Hafsi Lafiya kike kuwa".

"Maci...ji neee".

Ta fadi cikin rawar baki da na jiki da sauri Goggo Marka ta sake fallewa can gefe tana mai cewa.

"Rugo ki baro wajan mana tun kafin ya illata ki in ma zaki iya kashe shi kawai...".

Ai ba ta karasa abin da take cewa ba itama kurma ihu jin abu ya taba mata kafa.

"Laha'ilaha 'ilallahu muhammadan rasulullahi Sallallahu alaihin wassalam".

Kam! ta kame a tsaye lokaci guda fitsari ya fara bin kafafuwanta.

Hafsi dake can gefe tana faman kurma ihu da tsalle-tsalle kamar wata biri lokaci guda ta fallo a guje tana mai wurgi da kallabin dake kanta zaninta kuwa gabadaya ta tattareshi ta cukuikuye zuwa kugunta a haka har ta iso wajan da Goggo Marka take a kame kanta tayi tana rungume gabadaya ta ma k'yalk'aleta ji kake rigija sun zube a kasa hakan ya dawo da Goggo Marka hayyacinta ta shiga ihu tana mai cewa.

"Ya sare mani kafa shi kenan na bani na lalace shikenan Alkiyamata ta zo wayyo ni kai na...".

Hafsi ta gani zube gefe guda tana faman sakin numfashi gami da dariya ya sanyata yin fakare da idanuwa jikinta sai k'yarma yake yi a hankali ta shiga jan numfashi tana mikewa kafun ta gyara daurin zaninta.

"Ba dai ya sare ki ba ko Hafsi".

Ta fadi tana bin sassan jikinta da kallo Hafsi ce ta sake kecewa da dariya tana mikewa har lokacin jikin nata bai daina bari ba.

UKU BALA'I (Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora