60=UKU-BALA'I

489 22 4
                                    

Tunani kawai take yi akan yarda zata anshi Dr.Karami lokaci guda bayan kuma ta san akwai wani akasa ko da yake ya kamata izuwa wannan lokaci ta saukaka wa kanta domin samun natsuwar zuciyarta.

Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zata faru bata sani ba bata san yarda zata dauki lamarin ba sosai take jin kamar bata kyautawa Dr.Aqeel ba in tayi duba da yanayin dake tsakaninta dashi.

"So daban kyautatawa daban".

Ta jiyo wani sashi na zuciyarta na dauko mata wani sashi na zancen Dr.Karami da ya faɗa mata.

"Amma ai kyautatawa na haifar da so da kauna ga mutane biyu? Kuma ai kyautatawa na cikin abin da ke haifar da so ga zukatan dangin rai".

Ta fadi tana tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa a hankali juyi tayi daga kwance da take ta mai da idanuwanta suna kallon sama sosai take jin

zuciyarta da kwanyarta na mikata wani mataki na musamman wanda zata so ace ta rayuwa a cikin sa har gaban abada amma kuma bata zaton haka ganin lamarin take kawai a labarin kanzon kurege ba zai taba tabbata ba.

Numfashi ta ja tana mai da numfashe idanuwanta a hankali ta buɗe su ta dago dan yatsen hannunta wanda yake dauke da zoben da Dr.Karami ya sanya mata kallonsa take yi zuciyarta na kara buɗewa da kaunarsa ji take yi duk wani GURBIN SO na zuciyarta Dr.Karami yana kokarin mamayewa cikin yan kwanakin nan sosai take jin ta a wani mataki na farin cikin zuciya wacce ta cika da kauna zallarta.

Zata so ace rayuwar ta mika a haka za ta so ace rayuwar ta cigaba da tafiya a haka amma ina! akwai wani wajan da za a kin tafiyar ta sani ALKALAMIN ƘADDARA zai iya zano mata wani abu mai girman gaske ya dora mata a matsayin JARRABI izuwa wannan lokaci ta rigaya ta saba sosai da sosai bata tunanin akwai kaddarar da zata fado rayuwarta bata yi kokarin ganin ta cinye ta ba.

Gabanta ne ya doka da sauri ta mike tana ambatar 'Hasbunallahu wa ni'imal wakil Yaa Hayyu Yaa Kayyum'.
Idanuwanta ta zaro sosai hannayenta saman kirjin ta tana jin yarda BUGUN ZUCIYARTA ke kara tsananta.

"ME KE FARUWA?".

Ta fadi tana jan numfashi da sauri ta shiga kokarin mikewa ji tayi duk ilahirin jikinta ya dauki sanyi kamar an doke mata duk wata gaɓa dake jikin ta a hankali ta shiga taka

kafafuwanta kanta ko dan kwali babu yalwataccen gashin kanta ya baje sosai har zuwa fuskarta da sauri ta janyeshi zuwa baya ba tare da ta sanya dankwali ba tayi hanyar waje a bakin kofa ta tsaya tana ajiyar zuciya Umma ta gani zaune ta zabga tagumi da sauri ta isa gareta ta taɓa ta amma ba alamaun ta san ta zo wajan.

"Umma!".

Mariya ta fadi da sauti a muryarta tana mai jinjigata a hankali taja wani dogon numfashi ta dago idanuwanta da suka dan kaɗa ta dubi Mariya kafun ta kau da su cikin wani irin yanayi na damuwa.

"Umma lafiya na ganki haka?".

Murmushi kadan tayi wanda da ka kalle ta zaka gane na dole ne girgiza kai tayi tana cizon laɓɓa.

"Mariya mahaifin ki shi na tuna wani mafarki mara dadi nayi a yanzu a nan zaune ina gangaɗi sosai naji na tsorata".

Ware idanu Mariya tayi jin abin da Umma ta fadi ko dai wani abu na shirin faruwa ne domin itama taji irin yanayin a yanzu zuciyarta ta sake bugawa hannun Umma ta kamo ta danke sosai cikin nata.

UKU BALA'I (Completed)Where stories live. Discover now